BA CIKI BANEHAUSA NOVEL

BA CIKI BANE

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳ

ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

 

*Page 21~25*

Rahma kuwa barci ta take sosai dan ita yanzu ba sallah take ba ba abinda ya ke tashe ta sai yunwa.

Tana fitowa a d’akin ta d’akin Nawaf taje ko da taje kwance ta same sa yana barci.

K’arasawa bakin bed nashi tayi sannan tace
“Kai malam Ka tashi nifa yunwa nake ji.”

K’in kulata yayi Rahma ganin haka ne yasata hawa kan bed d’in tana cewa
“Da kai fa nake magana kak’i kulani Ka tashi kaje kitchen Ka girka mun abinda zanci.”ta k’arasa maganar tana kai mishi duka.

Wani irin mik’ewa Nawaf yayi ya kai mata mari sannan yace
“Ke Wallahi ki kiyaye ni dan Uban ki nine zan dafa miki abinda zaki ci?
To wallahi sai dai ki mutu amman ni bazan dafa miki wani abu ba.” Ya k’arasa maganar yana huci.

Ita kuwa Rahma gaba d’aya ta tsorata tambayan kanta take akan “wai shin maganin Bokan baiyi komai bane?” Katse mata tunani yayi da cewa
“Ke tashi kibar mun d’aki tunkan naji miki ciwo a gidan nan.”

Ai kuwa da gudu Rahma tabar mishi d’akin Sa dan kuwa zai iya aikata abinda yayi niyya.

Kitchen ta wuce dan yunwa take ji indomie ta dafa sai da taci sannan ta koma d’akin ta dan yin wanka.

Tana shigo d’akin ta tarar da wayan ta yana ringing da sauri ta k’arasa wajen wayar.

D’auka tayi ta kara a kunne dan ganin mai kiran ta.

Wanda ya kira ne ya fara magana
“Hello Maman Baby kin tashi lafiya.”
“Lafiya k’alau.”
“To ya Babyna da fatan kina kulamun da shi sosai.”

Tsaki taja sannan tace
“Wai kai Suraj dan meyesa kake son takura mun ne?
Nace kafita a harkana ko?” Ta k’arasa maganar da karfi har sai da Nawaf da zai fita yaji.

“Haba Maman Baby kinsan bazai yu na barki haka ba ko?
Dole sai ina kula da ke ko kuwa Momy tana kulamun da ke?.”

Da karfi tace
“Suraj!
Dan Allah Ka barni nasamu hutu dan meyesa kake bibiyar rayuwa ta ne?
Bayan Ka yaudare ni kamun ciki duk da haka bazaka barni ba why?”

Murmushi Suraj yayi sannan yace
“Rahma bazaki gane bane but yanzu ki fad’a mun me kike buk’ata sai na aiko miki duk da Momy tace bak’ya buk’atar wani abu.”

“Ba wani abu nake buk’ata ba kud’i ne kawai banda shi.”
“Ok kamar nawa kike so?” Ya tambaye ta.
Murmushi tayi sannan tace
“Kasan ba ni kad’ai bace har da d’an ka kuma tun yanzu zaka d’auki nauyin abincin sa.”
“Eh naji yanzu nawa kika ganin zai miki nan da karshen wata?”
“No bazan yanke maka kud’in da zaka bamu ba kawai Ka kawo iya abinda yake wajen Ka.”

Cewa yayi
“Ok to anjima zan turo miki 50k yayi ko.”
Murmushin jin dad’i tayi sannan tace
“Yes yayi sai naji alert” tana gama fad’an haka ta kashe wayar, shi kuwa Suraj yana jin son ta a cikin ran shi.

Duk wannan maganar da sukayi a kunnen Nawaf amman kuma ya kasa magana hakan ne yasa shi juyawa ya fita ya hau motar sa bai tsaya a ko ina ba sai gidan su.

Zaune ya samu Hajiya da Hindu a parlour suna hiran su sallaman su ne ya katse musu.

Amsa mishi sukayi sannan ya shigo,
Har k’asa ya durkusa ya gaida mahaifiyar sa sannan Hindu ta gaida shi.

Hindu ce tace
“Bro daga ganin ka bakayi bearkfast ba bari na had’a maka” tana k’arasa fadar haka ta tashi ta nufi kitchen.

Hajiya ce ta kalle sa sannan tace
“Lafiya dai na ganka a haka ?”ta tambaye sa.

Samun kansa yayi da kasa fad’awa mahaifiyar sa abinda yaji sannan ya juya yace mata
“Umma daman inason amun alfarman a aura mun Safnah nasan nayi kuskure amman dan Allah Umma a taimaka mun wallahi banida wacce nake so sama da ita.” Sai kuma yayi shiru ganin Umma ta canza fuska.

Ce mishi Tayi
“Kai Nawaf bazaka maidamu k’ananun yara ba!
Auren Safnah kace ko?
To baza’a baka ba tun farko da akace Ka aure ta ba k’i kayi ba sai da kaga abu ya kwa6e maka zakace a aura maka ita to za’a aura maka ita d’in ba.”

Shi kuwa Nawaf shiru yayi yana jin Hajiyar tasa muryar Hindu suka ji tana cewa
“Haba Umma kuyi hak’uri dan Allah Ku aura masa ita kinsan ita da kanta Safnah tana son Bro kuma shima yana son ta kawai dai tsautsayi ne da kuma abinda Allah ya k’addara ba yanda za’ayi.” Ta k’arasa maganar tana mik’awa Nawaf plate d’in abinci.

Hajiya ce tace
“Haka ne Hindu amma ai duk shine sila da baik’i auren ta ba ai duk wannan abin bazai faru ba.”
“A’a Umma wannan abin Allah ya rubuta shi tun ran gini tun ran zane Kinga kuwa dole sai ya faru yana d’aya daga cikin k’addaran su Allah yasa shine mafi alkhairi.”

Gaba d’aya su ne suka amsa da “Ameen Ya Allah.”

Sun kuyar da kai Nawaf yayi yace
“Umma dan Allah a duba a taimaka insha Allah hakan bazai sake faruwa ba.”

Shiru tayi na d’an wani lokaci sannan tace
“To Allah ya tabbatar da alkhairi anjima zanje gidan nasu insha Allah komai zaiyi dai-dai.”

Hindu ce tayi tsalle ta fad’a akan Umma tana cewa
“Wayyo Allah Umman mu mun gode sosai anjiman nima zan biki.”

Ture ta tayi tana cewa
“Ke tashi mun a jiki kar ki karyani .”

Dariya Nawaf yayi sannan yace
“To Umma nagode sosai Allah ya kaimu anjiman.”
“Ameen.”

Bayan nan kuma suka d’an yi hiran su sannan Nawaf ya koma gida akan anjima zai dawo yaji ya su Umma suka yi.

Haka kuwa akayi da yamma misalin k’arfe 4:30pm Hajiya da Hindu suka sauka a gidan su Safnah.

Gidan Alhaji Isah suka tafi Yayan Hajiya Fatima.

Su biyu ne a wajen mahaifin su amman ba maman su d’aya ba.

Alhaji Isah Allah bai bashi haihuwa ba hakan ne yasa su d’aukan Safnah wacce ta rasa iyayen ta tun tana k’arama.

Sallama sukayi suka shiga parlour babu kowa sai TV da yake ta faman surutu shi kad’ai.

Hindu ce ta sake sallama tana cewa
“Ko ba kowa ne a gidan shiru haka?”

Da sauri Safnah ta fito a kitchen tan cewa
“Sannun ku da zuwa wallahi ban jiku ba” tana fad’an haka ta k’araso inda suke da sauri.

Murmushi Hindu tayi sannan tace
“Girki kike mana ne haka k’amshi yabi ya cika gidan?”

Safnah bata kula taba d’an tasan yanzu zata fara tsokanan ta, durkusawa tayi ta gaida Umma sannan taje ta kawo musu drinks.

Murmushi Umma tayi tace
“Ina Aunty ki ne?”
“Tana ciki bari nayi mata magana nasan bata san kinzo ba” tana gama fad’an haka ta fice tabar parlour’n.

Murmushi Hindu tayi sannan tace
“Umma kinga wallahi Safnah tana da hankali kingan ta ba ruwan ta idan Bro ya aure ta gaskiya ya huta.”

Hajiya ma murmushi tayi tace
“Gaskiya nima naga alamun hakan” tana rufe bakin ta Hajiya Salma ta shigo tana musu sannu da zuwa.

Gaisawa sukayi cikin mutunta junan su sannan Hindu ma ta gaida ta.

Hajiya Fatima ce ta kalli Hindu tace
“Ki tashi ki bamu waje zamuyi magana.”

Ba musu Hindu ta bar parlour’n ta wuce wajen Safnah da take kitchen.

Ajiyar zuci Hajiya Fatima tayi sannan tace
“Daman munzo ne akan maganar auren Safnah da Nawaf” ai kuwa nan da nan tabata labarin abinda sukayi da Nawaf.

Murmushi tayi sannan tace
“To ai Yayan naki ma yana ciki yana wanka ne bari na duba idan ya shirya ya fito ayi maganar da shi, gaskiya naji dad’in wannan labarin.” Tana gama fad’an haka ta shiga bedroom d’in Alhaji ISAH.

Tsaye ta same shi ya saka jallabiya fara yana fisa turare.

Da sallama ta shiga ya amsa mata sannan tace
“Alhaji Hajiya Fatima ce tazo da muhimmiyar magana kai muku jira.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button