BA CIKI BANEHAUSA NOVEL

BA CIKI BANE

“Yaushe tazo ta?”
“Yanzu ne bata dad’e ba.”
“Ok ina zuwa.”
Haka ta wuya ta futa suka zauna a babban parlour’n suna jiran sa.

Da sallama ya shigo suka amsa masa sannan suka gaisa.

Nan da nan suka fara tattaunawa akan maganar auren Alhaji Isah ma yayi murna sosai dan daman shine burin sa.

Alhaji Isah ne yace
“To yanzu kun sanar da Safnah ne?”

 

*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????

???????? *BA CIKI NA BANE!*????????

????????????????????????????????

*​​WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ*​​????✍????

​“`DEDICATED TO ALL MY FANS​“`????????❤❤????????????????????????

*KUYI HAK’URI YAU BAN SAMU NAYI DUK ABINDA KAYI….. BA SAI GOBE IDAN ALLAH YA KAIMU INA FATAN ZAKU MUN AFUWA*❣❣❣❣❤❤

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*​Page 26~30*

Hajiya Salma ce tace
“Ai daman Safnah tana son Nawaf tun ba yanzu ba amman dai bari muji ta bakin ta.”

Alhaji ne yace
“To yanzu ki tashi kije kiji idan tana son sa sai muji.”

Haka ta tashi ta nufi kitchen d’in da suke.

Hindu a kitchen ta samu Safnah tana girki.

Da sallama ta shiga sannan tace mata
“Amaryan mu sannu da aiki bari na tayaki.”

Da mamaki Safnah take kallon Hindu sannan tace
“Ban gane amaryar ku ba?”

Murmushi Hindu tayi sannan tace
“Safnah maganar gaskiya Bro yana matuk’ar k’aunar ki yanzu haka ma munzo neman auren ki ne dan Allah ki amince da dan uwa na wallahi yana cikin wani hali please Safnah.”

Har zuciyan ta Safnah taji dad’in hakan amman sai ta 6oye farin cikin ta da cewa
“Hindu gaskiya bazan iya auren Ya Nawaf ba.”

Da sauri Hindu tace
“Haba dan Allah Safnah kar kice haka ki amince da kudirin mu dan Allah ki taimaka nasan ke da kanki kina son Bro Allah baiyi auren ku da wuri ba sai yanzu dan Allah Safnah ki taimakawa Bro kar yashiga wani hali.”

Kallon ta Safnah tayi sannan tace
“Yanzu ke kina ganin wanne hali zan shiga had’a kishi da Rahma?”

Murmushi Hindu tayi sannan tace
“Safnah kenan!
Ai Rahma bata da wani matsala kuma ita da kanta tasan daman Kuna soyayya da Bro kawai dai Allah ya rubuta da sai anyi nata sannan za’ayi naki.”

Murmushi Safnah tayi amman ta kasa cewa komai Hindu ce tace mata
“Yadai kinyi shiru ina fatan kin amince?”

Murmushi ta sake yi sannan tace
“Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.”

Runguman ta Hindu tayi sannan tace
“Ameen thumma ameen Auntyna.”

Ture ta Safnah tayi tace
“Bana so kar ki sake kirana da Aunty salon ki tsufar da ni.”

Dariya Hindu tayi tace
“Oh i’m sorry.”

Tana gama fad’an haka Aunty Salma tayi sallama ta shigo tana cewa
“Wai har yanzu baku gama girkin ba?”

Hindu ce tace
“Mun gama Aunty wanke-wanken ne ya rage.”

Cewa tayi
“OK” kallon Safnah tayi sannan tace
“Safnah wajen ki nazo.”

Kallon Aunty nata tayi sannan tace
“To Aunty.”

“Daman anzo Neman auren ki wa Nawaf ne to shine muke so muji ta bakin ki kina son sa?” Ta tambaye ta.

Sunkuyar da kai Safnah tayi sai faman murmushi take amman ta kasa cewa komai hakan ne yasa Hajiya Salma cewa
“Ke fa nake jira kinyi shiru.”

Hindu da take gefe ce tace
“Aunty ai wannan shine amsan.”

Hajiya Salma harara tayiwa Hindu tayi mata alamun tayi shiru sannan ta sake cewa
“Ok bari naje na fad’a musu cewa bak’ya son sa.” Ta k’arasa maganar tana mik’ewa.

Da sauri Safnah tace
“Ina son sa Aunty.” Sai kuma ta rufe fuskan ta da tafin hannun ta.

Dariya Hajiya Salma tayi sannan ta wuce zuwa parlour.

Zuwa tayi ta zauna sannan tace
“Na tambaye ta kuma tace tana son sa.”

Wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyar su sannan Alhaji yace
“Alhamdulillah daman hakan muke son ji yanzu idan kika koma gida sai kuturo da magabatan sa sai a saka time na bikin.”

Cikin farin ciki Hajiya Fatima tace
“Insha Allah zasuzo dan bikin ma bama so yaja lokaci.”

Alhaji yace
“To shikenan mu a shirye muke ba matsala anjima zanje na sanar da dangin mahaifin ta idan yaso ko gobe za’asa ranar bikin.”

Haka dai suka tattauna sai byana magriba sannan suka koma gida.

Tunda Nawaf ya fita Rahma ta rasa me yake mata dad’i wayan ta ta d’auka ta kira mahaifiyar ta d’auka tayi tace
“Hello Rahma ya kuke?”
“Lafiya ba lafiya ba Momy.”
Gyara zama Hajiya Saratu tayi sannan tace
“Meye ya faru Rahma maganin baiyi aiki bane?”
“Momy yayi aiki amman na lokaci k’alilan jiya ne kawai ya fara amman dare yana tsalawa abin yabar aiki Yau da safe ya kusan duka na ma.”

“Kai wallahi kin cika gaggawa Rahma, kiyi hak’uri a hankali komai yake dai-dai ai, jiyan me yayi miki?” Ta tambaye ta.

Ai kuwa nan da nan ta fara bawa Momy labarin irin kud’in da ya kashe mata.

Hajiya Saratu dariya tayi har da shewa sannan tace
“Aiki yayi kyau kenan wannan shine alamun nasara a aikin nan yanzu shawaran da zan baki kici gaba da aiki a maganin nan kuma kar ki kuskura kiyi sallah ko da wasa kina jina ko?”

“Eh Momy ina jinki ba abinda zai sani yi saboda nima na fara jin dad’in wannan aikin.”

“Yauwa ‘yar albarka shiyasa bake son ki,
Yauwa Suraj ya kira ki ne?”
“Eh ya kirani bamu dad’e da yin waya da shi ba.”
“To abinda nake so da ke kar ki fad’a mishi abinda zai 6ata mishi Kinga dai d’an uwan ki ne, kuma yana matuk’ar k’aunar ki so bana son abinda zai 6ata mishi.”

“To Momy insha Allah bazan 6ata mishi ba,
Yace zai turo mun kud’i zuwa anjima.”

Washe baki Saratu tayi sannan tace
“Yauwa kingani ko? Yana turo miki kar kiman ta da ni dan nima ina buk’atar kud’i kunji ko?”
“Momy kar kidamu yanzu haka akwai wani kud’i na Nawaf zan aiko miki.”
“To ‘yar albarka ina jiran ki.”

Haka dai suka d’an yi hiran su sannan sukayi sallama.

Nawaf kuwa da ya fita a gidan Hajiya ba gidan sa ya nufa ba ziyara ya tafi wa ‘yan uwa da abokan arzik’i.

Bayan yayi sallan magriba ne ya dawo gidan Hajiya amman su har yanzu basu dawo ba hakan me sashi zama ya jira su.

Bai dad’e a zaune ba sai gasu nan sun zo Hindu ce tace
“Bro har kazo?”
“Eh wallahi Sis kinsan na damu sosai.”

Umma ce ta shigo hakan ne yasa Nawaf cewa
“Sannu da zuwa Umma.”
Waje ta samu ta zauna sannan tace
“Yauwa sannu Nawaf.”

Zama Hindu tayi sannan tace
“Bro sai dai fa kayi hak’uri dan kuwa Safnah tak’i yarda da auren ka” ta k’arasa maganar cikin sun kuyar da kai dan dariya ne ya zo mata.

Da sauri Nawaf ya d’aga kai yace
“Dan Allah Umma ki taimaka mun wallahi Safnah tana sona kamar yanda nake son ta” sai kuma yayi shiru ya sunkuyar da kai dan ji yake kamar yayi kuka.

Umma kam kallon ikon Allah ta tsaya yi dan ita Nawaf har mamaki yake bata dan bata ta6a ganin sa haka ba akan soyayya.

Hindu ce wacce ta kasa rik’e dariyar ta tayi harda rik’e ciki kallon ta Nawaf ya tsaya yi dan bai gane me take nufi ba yace
“Ok ni kikeyiwa dariya ko?”
Kallon shi tayi sannan ta sake fashewa da dariyar tace
“Sorry Bro wallahi Kaine Ka bani dariya kuka zakayi dan Safnah tace bata son ka? Ai ni banga abin damuwa ba kawai Ka samu wata ko kuma Ka zauna da matar ka.” Tana k’arasa maganar ta sake fashewa da wani dariya.

Wani irin bakin ciki ne ya rufe Nawaf sannan yace
“Ke bana son rai ni!
Ni kike fad’awa haka?
Lalai kin raina ni amman zanyi maganin ki.” Yana gama fad’an haka ya mik’e da niyyar fita Umma ce tace
“Ina kuma zaka bayan bamuyi magana ba ko daman Hindu kasa taje gidan nasu?” Ta tambaye sa.
Sai a lokacin ya tuna ashe basuyi maganar da Umma ba hakan ne yasa shi dawowa ya zauna gefen Umma.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button