BA CIKI BANEHAUSA NOVEL

BA CIKI BANE

Hindu ce tace
“Sorry Bro idan na 6ata maka rai.”

Umma ce ta kalli Nawaf tace
“Alhamdulillah munyi magana da iyayen Safnah an baka idan Allah ya kaimu gobe za’asa ranar bikin ku idan Abban ku ya dawo zan sanar da shi sai ya fad’awa Baffan ku .”

Wani irin dad’i ne ya ziyarci zuciyar Nawaf sannan yace
“Kai amman nagode sosai Umma Allah ya kaimu goben.”

“Ameen sannan sai Ka shirya dan ba rana mai tsayi za’a saba bazai wuce 1 mouth ba.”

“A shirye nake Umma ko da sati biyu za’a saka.”

Kallon sa Hindu tayi tace
“Bro baka yafe mun bane?”
Kallon yayi sannan yayi murmushi yace
“Haba My sweet Sis ai nasan kece a gaba wajen Nema mun auren Safnah Kinga kuwa air bazan miki fishi ba ko ban sameta ba.”

Dariya Hindu tayi tace
“Ai kuwa kamar Ka sani nice nasha wahala.”

Umma kam tana zaune tana kallon su sannan tace
“To yayi kyau tunda kece kika sha wahala sai kije ki daura auran.”

Gaba d’ayan su ne suka kwashe da dariya.

Umma ce tace to “yanzu ya zakayi Ka sanar da Rahma?”……..

*Nima dai abinda nace kenan*????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

 

*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????

???????? *BA CIKI NA BANE!*????????

????????????????????????????????

*​​WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ*​​????✍????

​“`DEDICATED TO ALL MY FANS​“`????????❤❤????????????????????????

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*​Page 31~35*

Shiru ne na dan lokaci ya biyo baya sannan yace
“A’a Umma bana son taji cewa nayi aure har sai ranar da aka kai Safnah.”

Kallon sa Umma tayi sannan tace
“Bakada hankali ne Nawaf!
Ya zama dole Ka fad’a mata saboda shiga hakk’in ta.”

Hindu da Nawaf ne suka had’a ido sannan Nawaf yace
“Umma kinsan idan aka fad’awa Rahma ba zaman lafiya nasan ita da mahaifiyar ta bazasu ta6a bari ayi bikin nan cikin kwanciyar hankali ba.”

Shiru tad’an yi sannan tace
“Kuma haka ne amman Kuna ganin ba matsala?”

Hindu ce tace
“Ba wani matsala insha Allah Umma.”
“To Allah ya sanya alkhairi.”
Gaba d’ayan su suka amsa da
“Ameen thumma Amen.”

 

Rahma kuwa tayi wanka tayi kwalliya ba wani kaya ta saka ba bra ne kawai da pant a jikin ta tana zaune a parlour tana jiran angon ta dan kuwa tayi amfani da maganin nan sosai yau.

Tana zaune tana jiran sa har 11:00pm bai dawo ba haka har ta gaji ta shiga d’aki tayi ta kiran sa tayi tayi a waya amman me baya shiga kwata-kwata haka har ta gaji ta kwanta barci yayi gaba da ita.

Shi kuwa Nawaf lokacin da ya shigo gidan ne yaji wani hayak’i mai wari ya turnuke shi waje ya samu ya tsaya sannan ya kama duk wata addu’a da yazo mishi haka yasa mu har sai da yaji dai-dai tukun ya koma baya ya shiga d’akin sa ta d’ayan k’ofar baya da zai kaika d’akin sa ba sai an ganka ba.

Bayan ya shiga Sallah yayi ya zauna addu’a akan Allah yasa auren nan da yasa gaba Allah ya tabbatar mishi da alkhairin sa.

Bayan kuma wayar sa ya d’auka ya fara Neman Safnah.

Ai kuwa yayi sa’a ya shiga ringing yake amman ba’a d’auka ba sai da yasake kira a na biyu sannan ta d’auka.

“Assalamu alaikum” tace cikin siririyar muryan ta.

Lumshe ido Nawaf yayi dan har cikin ranshi yaji muryan ta abinda ya dad’e bai jiba.
Jin anyi shiru ne yasa ta cewa
“Hello waye?”
Sai a sannan ya gyara murya sannan yace
“Wa’alaikis salam Gimbiya ta.”
Jin muryan Nawaf Wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskan ta amman sai ta juyashi da cewa
“Sorry ban gane waye ba.”
“Ikon Allah amarya ce take cewa bata gane angon ta ba?” Ya tambaye ta cikin tsigar tsokana.

Murmushi tayi sannan tace
“Ango kuma please waye ne? inada abin yi.”
Murmushi yayi sannan yace
“Nawaf ne.” Kawai yace.

Murmushi tayi tace
“Au Ya Nawaf kai ne?
Shine Ka tsaya kana b’oye mun kanka.”
Murmushi yayi sannan yace
“Ai nasan kin gane ni kawai dai kina son jan class ne.”

Dariya tayi sannan tace
“A’a Ya Nawaf
Ina Wuni.”
“Sorry Gimbiya ta ashe ko gaisawa bamu yi ba,
Lafiya k’alau ya su Aunty.”

“Lafiya k’alau,
Ina Aunty Rahma?”
Shiru ya d’anyi sannan yace
“Lafiyan ta.”

Safnah ta fahimci haka but sai ta waske da cewa
“To yayi kyau Ka gaida ta.”

Gyaran murya yayi sannan yace
“Safnah d’azu su Umma sunzo gidan ku akan maganar mu, gaskiya naji dad’i yanda kika amsa musu da kina sona kamar yanda nake son ki Safnah, insha Allah zan zama mutumin da zan kore maraicin ki duk da yanzu ma bak’ya ciki, insha Allah Safnah zan za jigon rayuwar ki muna tare har Abadan a badada ina fatan kema zaki kula da ni har izuwa k’arshen rayuwa na?” Ya tambaye ta.

Ajiyar zuci tayi sannan tace
“Insha Allah Ya Nawaf ina tare da kai duk rintsi duk wuya ina tare da kai fata na shine kazama mai adalci a tsakanin mu ni da Aunty Rahma, insha Allah zan zama mai biyayya a gare ka zan kula da kai iya gargadona.”

Murmushi jin dad’i yayi sannan yace
“Alhamdulillah daman hakan nake son ji a gare ki sannan kinsan cewa gobe za’a sa ranar biki kuma ba wani time mai tsayi za’a d’auka ba 1 mouth ne kawai idan kina buk’atar wani abin sai ki fad’a mun saboda ba time.”

Murmushi tayi sannan tace
“Ya Nawaf 1 month baiyi kad’an ba?”
Da sauri yace
“Kai nida nake ji yawa ko so kike nace na rage?”
“A’a ni wai sai nake ji kamar zai takura mana.”
“A’a babu wani takura zamuyi bikin mu cikin farin ciki da k’aunar juna.”

Haka dai sukayi ta hira a tsakanin su sai kusan 11 sannan sukayi sallama ko wannen su ya kwanta cikin farin ciki.

 

 

Washe gari kamar yanda suka fad’a haka iyayen Nawaf sukaje aka saka ranar biki sai da suka gama komai sannan suka dawo gida.

Nawaf kuwa ba k’aramin farin ciki yake ba dan kuwa abin k’aunar sa takusan zama Matar sa.

Duk wannan abin da ake Rahma bata San komai ba ita da Hajiya Saratu sai zuwa wajen boka suke ana kara basu wasu magungunan akan Nawaf but har yanzu baiyi wanka da shi ba.

Abin ba k’aramin 6atawa Rahma rai yake ba dan ita yanzu har ta fara gajiya abu har yanzu ba nasara gashi tabar sallah har na tsawon kwana uku duk da haka bataga canji ba.

Hajiya Salma kuwa ba k’aramin gyara Safnah take ba dan gida da kishiya sai an gyara yarinya ciki da waje.
*(Nidai nace ba irin Rahma ba wacce bata San mai yake mata ciwo ba asalima ciki ne d’auke a jikin ta na wani banza)*

Nawaf da Abokin sa Dr-Sabir tare suke duk wani abu da ya danganci bikin ko da Rahma taga Nawaf yana gyara gidan sa bata kawo komai a kanta ba sai ma cewa tayi saboda son da yake mata ne yake gyara mata gida.

Hindu kam duk wani kaya da Nawaf zai siya na ak’watin Safnah da ita aka tafi dan ita take za6a musu ita da Rahma komai iri d’aya.

Ko ita Hajiyar Nawaf tafi jin dad’in auren Safnah da Nawaf itama shiri take sosai.

 

Kowa shiri yake musamman su Hajiya Salma saboda itace ‘yar su guda d’aya tilo.

Safnah kam tasha gyara har ta gaji dan har wani canzawa tayi tayi kyau abin ta.

Yau take Alhamis ranar kamu biki na alfarma akayi dan abin ba k’aramin tsaruwa yayi ba.

Haka sukayi kamu cikin kwanciyar hankali dan ba wani abu da ya faru.

Rahma kuwa batasan me ake ba tana ta fama da cikin ta dan yanzu yakai 4mouths tana son ta fara tafiya awu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button