BA CIKI BANE

Ranar juma’a Walima suka kayi abinsu ranar asabar kuma aka d’auka auren Safnah *(Amina Muhammad)* da Nawaf *(Ibrahim Khalil)* haka aka sha biki aka watse.
Da yake ranar d’aurin aure za’ayi gere Nawaf yace da Rahma taje gidan su ta gaida Hajiya idan anjima zaizo ya d’auke ta Yau ana abikin abokin su.
Ita kuwa da taji haka sai tayi tsammanin magani ne ya fara aiki da har baya son barin ta gida ita kad’ai.
Haka akazo aka gerewa Safnah kayan ta ba k’aramin kyau parlour’n ta da d’akin ta sukayi ba da yake gidan ko wacce tanada nata parlour’n da kitchen sai babban parlour da yake shine a tsakiya.
Koda suka gama gera kayan Safnah har babban parlour’n suka gyara suka share sukayi moping sannan suka saka turaren wuta nan da nan gidan ya gauraye da k’amshi. *Abinda gidan ya manta da akwai shi a duniya*
Haka suka koma gida dab magriba a lokacin har yan d’aukar amarya sunzo.
Ba k’aramin nasiha akayiwa Safnah ba akan zama da kishiya da yanda ya kamata su had’a kansu su zauna da yiwa miji biyayya haka dai sukayi ta mata har aka tafi da ita tana ta faman kuka.
Rahma kuwa tana gidan su jikin ta ba dad’i hakan ne yasa ta kiran Nawaf a waya tace
“Hello Nawaf.” Sunan da yanzu take kiran sa kenan ba ko kara.
Amsa mata yayi da “Na’am.”
“Banajin dad’in jiki na ne inason zan kwana a gidan Hajiya dan bazan iya zuwa ba.”
Wani irin farin ciki ne ya mamaye Nawaf sannan yace
“Ayya sorry ba matsala duk lokacin da kika ji sauki sai ki dawo.”
Da “To” kawai ta amsa mishi ta kashe wayar.
Shi kuwa nawaf dad’i ne ya cika mishi ciki dan daman hakan yake nema kuma gashi ya samu.
Haka aka kawo amarya Safnah tana ta kuka dak’yar aka samu tayi shiru sannu ‘yan kawo amarya suka watse aka barta daga ita sai k’awarta Raihana.
Sallaman Ango da abokin sa ne yasa su nutsuwa waje d’aya.
*Washhhh wllh na gaji*
*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????
???????? *BA CIKI NA BANE!*????????
????????????????????????????????
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*????✍????
“`DEDICATED TO ALL MY FANS“`????????❤❤????????????????????????
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 36~40*
Sallamar Ango da abokin sa ne yasa su nutsuwa wajen d’aya.
Nawaf ne yazo ya zauna a bakin bed d’in sannan shi abokin nasa ya zauna a d’aya daga cikin kujerun d’akin.
Kallon sa Nawaf yayi ciki zolaya yace
“Yadai kasamu waje ka zauna ai tafiya ya kamata kuyi kai da ita.”
ya gama maganar yana nuna Raihana.
Kallon sa Raihana tayi sannan tace
“Kai Nawaf ko irin kunyar nan babu kana koran mu?
To nidai kwana zanyi sai dai abokin ka ya tafi.”
Dariya yayi yace
“Cab ai kuwa baki isa ba!
Bazaki hanani jin dad’i da amarya ta ba maza Ku tashi na raka ku Allah ya kiyaye hanya.”
Kallon sa Dr-Sabir yayi sannan yace
“Lalai kuwa abokina abin naka azimun ne bari muyi maza mu tashi kar asa mana duka.”
Dariya sukayi sannan Raihana tace
“Gaskiya naga alamun haka ka tashi muje ka sauke ni a gida dan naga wallahi abokin naka ba kirki gare shi ba tsaf zai mana abinda bazamu ji dad’i ba.”
Dr-Sabir ne yace
“Hmm koma menene auren nan dai zamuyi shi.”
Raihana ce tace
“Insha Allah.”
Safnah kuwa tana zaune tana jin su ita tsoron Nawaf ne ma ya kamata dan yanda yake zumud’in har yayi yawa kamar bai ta6a aure ba.
Haka dai suka d’an zolaye shi,
Bayan nan kuma suka Mik’e da niyar tafiya.
Raihana ce tace
“Amarya ni natafi dan mijin ki korana yayi sai wata rana.”
Rik’e hannun ta Safnah tayi amman batayi magana ba.
Raihana ce tace
“Yadai amarya ki barni mu tafi dare yanayi Angon ki a matse yake.”
Dariya sukayi gaba d’ayan su sannan Dr-Sabir yace
“Kwarai kuwa kamar kin sani ki barta mu tafi.”
Haka kuwa suka tashi suka tafi Nawaf ya raka su bakin gate sannan ya dawo gida.
A inda ya barta a nan ya dawo ya same ta zaune ta wani nan nad’e a wajen kamar mai tsoron wani abu.
Zuwa yayi ya zauna a kusa da ita sannan yace
“Amarya ta bazaki bud’e mun fuskan naga kwalliyar ki ba?”
Ita dai gaban ta ne yake dukan uku-uku hakan ne yasa ta yin shiru.
“To idan bazaki bud’e ba bari na bud’e abu na.”
Sauri tayi ta yaye mayafin da yake fuskan ta.
Murmushi yayi yace
“Ki tashi muje muyi alwala mu gabatar da sallah raka’a biyu na godewa Allah na wannan ni’imar da yasa mu cikin ta.”
Ba musu Safnah ta tashi suka nufi toilet sukayi alwala suka fito suka gabatar da sallah.
Addu’a Nawaf yayi musu sosai sannan yayi mata tambayoyi akan addinin musulci ta amsa mishi.
Bayan ya shafe addu’a tashi yayi ya tafi kitchen ya d’auko ledan da suka ajiye a kitchen sannan ya had’a da plate da cups ya taho musu da shi d’akin.
Gashasshen kaza ne da tsire wanda yasha had’a sai k’amshi yake tashi sai juice masu sanyi da fresh milk.
Bayan ya zuba musu janyo Safnah yayi jikin sa yace mata
“Nasan cewa kina jin yunzu dan Allah kici ki koshi.”
Kallon shi tayi tace
“Ya Nawaf na k’oshi bani da yunwa.”
Sake janta yayi jikin sa sannan yace
“Ai kuwa baki isa ba nasa kina jin yunwa kiyi maza kici mu kwanta.”
Haka ya dinga d’auka yana bata tun tana jin kunya har ta fara ci bai daina bata ba sai da taci ta k’oshi sannan shima yaci nasa.
Tashi tayi ta fara tattare kayan da suka ci abincin rik’e mata hannu yayi yace
“Haba dai amarya ta a ina kika ta6a ganin amarya tana aiki?
Ki bari ni da nakawo na mayar da su inda na d’auko.”
Kallon sa tayi sannan tace
“A’a Ya Nawaf ka bari na tattara su ko baka son na fara samun ladan auren tun yanzu?”
Girgiza mata kai yayi alamun
“A’a”
Sannan tace
“To kabari na kwashe su kaji.”
Murmushin jin dad’i yayi sannan yace
“To shikenan ki tattara.”
Haka ta had’a kayan nan ta kai kitchen ko da taje sai da ta wanke ta maida ko wanne inda yake sannan ta dawo.
Ko da takoma d’akin bata ganshi ba motsin sa taji a toilet da alama dai wanka yake haka ta samu waje ta zauna tayi tagumi kamar wacce aka aiko mata da mutuwa.
Bayan ya gama wanka towel ya d’aura ya fito ya same ta zaune.
Zama yayi a kusa da ita yace
“Habbity ki tashi kije kiyi wanka Kinga dare yayi.”
Kasa daga ido tayi ta kalle sa dan wani irin kunyan sa ne ya kamata dan bata ta6a ganin namiji haka ba.
Katse ta yayi da cewa
“Ki tashi kinji.”
Mik’ewa tayi ta nufi toilet bayan tayi wanka bata San ya zatayi ba idan idan ba towel ba komai a toilet d’in.
Ta dad’e a tsaye tana tunanin fita haka but ba yanda ta iya haka ta fito duk cinyoyin ta a waje.
Yana zaune a bakin gadon yana jiran ta ganin ta fito haka ne yasa shi tsayawa yana k’arewa halittan Allah ido.
Wani irin abu yaji yayi mishi shock a jikin sa baki d’aya.
Ita kuwa duk tabi ta tsure da irin kallon da yake mata jiki yana rawa ta k’arasa wajen akwatin da zata cire kayan barcin ta sai ji tayi ya wani fizgota.
Yana janta jikin sa ya fara wasa da duk wani gaba na jikin ta.
Romantic yake mata sosai wanda sai da ya fiddasu a hayyacin su gaba d’ayan su.
Sai da ya rabata da kayan jikin gaba d’aya sannan ya d’auke ta zuwa gado.
Hmmm ganin abin yafi k’arfi na yasani ja musu k’ofar d’aki.
Rahma kuwa tunda taje gidan su hankalin ta ya kasa kwanciya dan wani irin fad’uwa yake mata.