BA CIKI BANEHAUSA NOVEL

BA CIKI BANE

Ko da ta fad’awa Momyn ta ce mata tayi cikin da yake jikin ta ne yake mata idan Allah ya kaimu Monday zata fara tafiya asibiti.

Duk da bata jin dad’in jikin ta but hankalin ta gaba d’aya yana wajen Nawaf dan jikin ta yana bata akwai wani abu.

Haka ta kwanta cikin tunani dan kuwa ko ta kira wayan Nawaf baya shiga hakan ne ya tayar matada hankali sosai.

 

 

Su Nawaf kuwa ansha angonci sosai dan sai da ya cire duk wani abu da yake damun sa gaba d’aya sannan ya bar Safnah.

D’aukan Safnah yayi ya kwantar da ita a cinyar sa ya dinga sa mata albarka dan abinda yaji bazai musaltuba dan Nawaf har kuka sai da yayi.
“Allah ya miki albarka Safnah kin shayar dani da madarar ki Safnah Allah ya miki albarka Allah ya bamu zuri’a dayyaba da ke Safnah nagode nagode Safnah.”

Ita kuwa Safnah sai faman narkewa take tana ta faman kuke-kuken shagwa6a.

Ganin kukan ta yayi yawa ne Nawaf yace mata
“Heartbeat kiyi hak’uri ki daina kuka bari na had’a miki ruwan wanka.”

Bata mishi magana ba ne yasa shi d’aura kanta a pillow ya mik’e ya nufi toilet.

Ruwa mai dumi ya had’a mata sannan ya koma ya d’auko ta ya saka ta.

Wani irin ihu tayi dan wani zafi taji ya ratsa ta.

Tun tana jin zafi har yazamo mata ruwan yana mata dad’i sai da taji sauk’i sosai sannan ta fita tayi wanka da kanta dan wani irin tattali Nawaf yake mata.

Wasu kaya ya d’auko ya saka mata sannan ya kwantar da ita sai da ya tabbatar barci ya d’auke ta sannan ya mik’e ya nufi toilet dan shima yayi wanka.

Bayan ya fito ya shirya sannan yazo ya kwanta a kusa da ita ya k’ank’ameta kamar Wanda wani zai kwace ta.

 

Washe gari da asuba suka tashi sukayi sallah sannan suka sake kwanciya barci.

Sune basu tashi a barci ba sai 9:30Am sannan suka tashi dan wani irin gajiya ne ha tashi musu.

Safnah wanka ta shiga shaf-shaf tayi ta fito sannan ta shirya cikin wata atampa riga da siket Wanda ya amshi jikin ta ba wani make-up tayi mai yawa ba tana gamawa ta nufi kitchen.

Nawaf ne yazo ya sameta Wanda shima yayi wanka ya shirya cikin wasu kananun kaya yace
“Amarya ina ke ina girki ai tun da safe Umma ta aiko mana da breakfast muje yana dining.

Haka suka nufi dining suka karya cikin so da k’aunar junan su.

 

Rahma kuwa tunda safe ta shirya akan zata dawo gida amman Mom ta hanata akan sai anjima zata tafi.

K’arfe goma tana cika Rahma ta kama hanyan gidan ta.

Tun a bakin gate take jin wani k’amshi yana dukan hancin ta.

Mamaki take wanne irin k’amshi ne Nawaf ya samu haka.

Tana shiga cikin ta same su zaune a parlour ya d’aura ta a cinya suna hira.

Wani irin firgita Rahma tayi tace
” Nawaf me nake gani haka???”

 

*Taku har kullum Momyn Musaddiq*????✍????????????????????????????????????

???????? *BA CIKI NA BANE!*????????

????????????????????????????????

*WRITTEN BY​​*
*​​MOMYN MUSADDIQ*​​????✍????

​“`DEDICATED TO ALL MY FANS​“`????????❤❤????????????????????????

*​® ​​REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​​​*

​ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ​

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# ​IG PML WRITERS​
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

 

*Page 66~70*

Mik’ewa Rahma tayi tayi wani Uban ashar sannan tace
“Ciki ne da ke Safnah a cikin gidan nan?
Ai wallahi karya kike baki isa ba ‘yar iska.” Ta k’arasa maganar tana mai k’arasawa inda take.

Safnah kuwa amai take sosai dan duk abinda taci sai da ta amayar shi sannan ta d’aga jajayen idon ta ta kalli Rahma sannan tace
“Kwarai ciki ne dani ko wani abu ne?”

Matsowa Rahma tayi kusa da Safnah tana cewa
“Ai kuwa baki isa ki haifi wannan cikin ba sai na zubar da shi yau d’in nan”
Tana gama fad’a ta kaiwa cikin naushi.

Da sauri Safnah ta rik’e hannun ta murd’a har sai da Rahma tasa ihu duk da bata jin dad’in jikin ta take ba sannan tace
“Ke ki dakata ni zaki sa hannu Kice zaki buga?
To ki Sani wallahi baki isa ba kar ki sake gangancin kai hannun ki jiki na.” Tana gama fad’an haka ta juya ta wuce d’akin ta tabar Rahma baki bud’e.

Tana shiga d’aki ta kwanta a kan gado dan wani zazzabin ne yake son zuba mata.

Rahma kuwa zama tayi tana kuka dan wannan babbar masifa ce a wajen ta but ba komai zatayi maganin ta.

D’akin ta ta koma ta d’auki waya ta kira Momyn ta a waya.

Tana d’auka ta fashe da kuka tana cewa
“Momy wallahi ciki ne da ita yanzu ta gama amai a gaba na kuma da bakin ta ta fad’a mun.”

“Ciki da gaske Rahma?”
“Eh Momy.”
“To kiyi hak’uri ki daina kuka ni nasan abinda zamuyi ki kwantar da hankalin ki gobe zan aiko miki da sak’o zan miki bayani ta waya.”

Sai a lokacin taji dad’i tace
“Yauwa Momyna nagode shiyasa nake sonki ina jiran sak’on goben.”

Bayan haka kum sukayi sallama.

Hindu tana komawa gida ta sanar da Hajiya Fatima cewa Safnah ciki ne da ita itama tayi murna sosai da wannan kyauta da Allah yayi musu.

Nawaf bai dawo gida ba sai bayan magriba dan yana tafiya aka bashi wasu aiki sai da ya gama sannan ya samu ya dawo.

Ko da yazo kwance ya samu Safnah jikin ta ya d’au zafi sosai.

Da sauri ya k’araso wajen ta yana cewa
“Sorry Sweetheart wallahi wasu ayyuka ne suka rik’e ni a office tashi kici a abinci kisha magani.”

Cikin rawan murya tace
“A’a Ya Nawaf bazan iya cin komai ba ka barshi sai anjima.”

Kallon ta yayi cike da tausayi sannan yace
“Kiyi hak’uri ki ta6a koda kad’an ne.”

Sake cewa tayi
“Ya Nawaf amai ne yake damuna yanzu haka inajin shi amman kuma babu komai a ciki na.”

Da sauri Nawaf ya ciro wayar sa ya fara neman Dr-Sabir.

Yana d’auka yace
“Hello dan Allah Dr-Sabir kazo gida yanzu jikin Safnah ya sake tashi kuma amai yana damun ta sosai.”

Amsa mishi yayi da cewa
“To ba matsala zan kawo mata maganin da zai tsayar da aman.” Yana gama fad’an haka ya katse wayar.

Nawaf yana zaune yasa mata ido yana kallon ta karan wayar sa ce ta sashi d’auke idon sa.
“Na k’araso ina parlour.”
“OK gamu nan fitowa.”
Yana kashe wayar yace da Safnah
“Sweetheart tashi muje parlour Dr-Sabir yazo.”

Da k’yar ta Mik’e Nawaf ya rik’e mata hannu sannan suka fita.

Sannu yayi mata sannan yace
“Taci abin ci ne?” Ya tambayi Nawaf.

“A’a wallahi bata ciba wai bazata iya ci ba.”

Kallon ta yayi sannan yace
“Kiyi hak’uri kici koda kad’an ne dan bazai yu kisha magani ba abinci a cikin ki ba.”

Ita dai shiru tayi tana kallon su dan wani biyu-biyu take gani tsabar yunwa.

Dr-Sabir ne yace
“Kai Nawaf ka kawo abinci ka bata ko zataci kad’an.”

Da sauri Nawaf ya mik’e ya zubo abinci a plate da ruwa yazo.

A hankali yake bata tana ci a haka har ta gama ci sannan ya karbi maganin ya bata tashi.

Dr-Sabir ne yace
“To yanzu ka zauna da ita anan ta d’an ji saukin jikin ta sannan ta kwanta but karta kwanta yanzu idan ba haka ba maganin bazai mata aiki ba.”

“OK to nagode sosai da kulawar ka Allah yabar zumunci.”

Bayan nan kuma yayi musu sallama ya tafi.

Duk wannan abinda suke a idon Rahma domin duk tana la6e taba jinsu cewa take
“Wato har wani lalla6ata kake ko?
To kuwa zanyi maganin ku baki d’ayan Ku.”

Tana gama fad’an haka ta shigo parlour’n.

Kallon su tayi sannan tace
“Sannu mijin Hajiya sai abinda tace zakayi dan naga har abinci kake bata ta gama asirce ka tsaf.”

Murmushi Nawaf yayi yace
“Eh kinsan ba kowa ne yake iya asirce mutum ba shiyasa ke kika kasa asirce ni.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button