BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 66-70

Page6⃣6⃣to7⃣0⃣

Haka fatima da muhammadu suka cigaba da rainon cikin da ba wanda yasan dashi domin kuwa kullum da hijab take kuma dama cikin nata bamai girma bane

Ranar wata talata da safe fatima ta fara nakuda bata sha wata wahala da kanta ta santalo lafiyayyar ya’rta mai kama da larabawa dan kuwa fara ce jajir babu ta inda ta bambamta da uwartt,,,farin ciki kuwa gurin muhammadu bai irguwa da kanshi yaje har gidan su ya taho da kanwar innarta ita tayi mata komai ta yanke ma jinjirar cibi ta wanke ta tass sannan aka nadeta a wani farin towel,,sannan ta hada ma fatima ruwan itama da kanta tayi mata wankan,,kafin ta dumama mata tuwaon dawa ta kawo mata,,,idan kaga fatima ba zaka ce itace ta haihu ba dan kuwa lafiyarta kalau ita da jaririyarta,,,muhammadu ne ya shigo dakin hannun sa rike kayan tea da siyo mata gurin ya nufa tare da daukan jinjirar fuskar nan fal farin ciki da annushuwa,,sai da yayi ma yarinyar addu’a kafin yayi mata huduba da suna HAUWA’U JIDDAH,,,fatima tayi matukar farin ciki da yasa mata sunan innar ta,,,sai a lokacin mutane suka fara shigowa gidan suna yi mata barka suna santin kyan yarinya,,,ita dai saidai kawae tayi murshi idan mutane na tambayar ta wai dama ciki gareta,,,ko en uwanta da suka zo mamaki suka rinka yi tare da godema allah,,,

shigowarta kenan gidan taga mutane wasu na fitowa daga dakin fatima wasu na shiga ga kuma en uwanta zazzaune a kofar dakin,,,mamaki takeyi tow meye akayi haka da har dangin mayyar can suka zo suka wani cika musu gida da hayaniya inama mutuwa shegiyar can tayi ai wlh da sai ta kira masu kidan kwarya sun buga mata ta cashe,,,sallamar muhammadu ce ta katshe mata tunanin da takeyi ko amsar sallamar bata yiba ta tsaya kallon shi ganin sai wani washe hakora yake,,,katse yayi tare da fadin amm… asabe munfa samu karuwa yau a gidan nan,,,,be tsaya jin me zata ceba ya cigaba da fadin dazu fatima ta haihu mun samu ya’ mace jiddah,,,tana zaunau a kan kujera ertsugunne amma sai data wuntsila tare da bajewa a dakin tayi zaman yan bori,,,cikin zaro ido tace wata fatiman,,,hanyar waje yayi yana fadin fatima nawa garemu a gidan tareda ficewa,,,yana fita ta zube a kasa burgima ta fara a tsakar dakin ta rasa inda zata tsoma ranta kawai saita fashe da kuka da wannan ranar ai gara mutuwar ta malam ya cuceni ya yaudareni,,kuka takeyi kamar karjmar yarinya,,,fatima ce wai ta haihu ta kara maimaitawa wallahi sai naga bayanta ita da shegiyar ya’r tata,,,

Haka akayi suna cikin kwanciyar hankali rago biyu manya manya muhammadu ya yanka mata bayan kaya da ya dinka mata itama jiddah ya saya mata kaya sosae ga kuma wanda dangin fatima suka mata komae dae alhamdulillah,,,tun mutane na tambayar fatima ina kishiyar ta take har suka bari,,dan asabe bakin cikin ta take nunawa kiri kiri ba abinda ta taba ko taci wanda ya danganci haihuwar fatima kuma bata fasa bin malaman ta daka ganta kasan bata da kwanciyar hankali…

taron suna ya watse kowa na sam barka fatima ta cigaba da renon yarta itada muhammadu,,,asabe saidai ido dan ita kadai tasan tsiyar data shuka kuma tasadm tabbas wannan sai tayi nasara domin wannan ba irin wancan bane…

Wata ranar sati muhammadu ba zai taba manta ta ba da kuma iyayen fatima da en uwanta,,,a safiyar da aka nemi fatima sama ko kasa aka rasa ba inda baa je nemanta ba a kauyen kiyawa har makotan su amma ko sawunta ba’a gani ba,,muhammdu suma yayi sai da ya kusan awa biyu kafin ya farfado ,,,yana farfadowa ya tashi tare da nufar kofar gida mutane suka rike shi amma ina turjewa yakeyi yana fadin abar shi yaje ya nemo fatimar sa,,,basu kara shiga tashin hankali ba sai da jiddah ta fara kukan yunwa aka rasa yanda zaayi innar fatima ce ta amshi yarinyar tana jijjigata amma ko alamun yin shiru batayi,,,fashewa da kuka kowa yayi ganin muhammadu na kuka wiwi kamar mace,,a yau asabe tayi rawa tayi juyi tayi hawayen farin ciki burinta ya cika,,dama sabon malaminta yace kurciya zaa mata itada dawowa garin kiyawa har abada,,,

Tsawon sati biyu kenan ba fatima ba labarinta jiddah kuwa tana gurin innar fatima itake renonta a yanzu kudi muhammadu ya bada isassu aka siyo madarar jarirai kuma da akayi saa tanasha sosae,,,muhammadu a yanzu rayuwa kawae yake domin kuwa asabe saida ta mallake shi tsab komai sai idan ita tace yayi tsoronta yake matuka yanzu,,kudi take amsa a gunsa koda yaushe tana wadakarta ita da yaranta shiko ya zama konko yanzu

BAYAN SHEKARA DAYA

a yanzu kam muhanadu baida komai asabe ita da ya’ya’nta sun gama cinye kudin shi tsab yanzu shagon da yake zuwa ma ankwace saboda rashin biyan kudin haya,,,

jidda kan yanzu shekarar ta daya tana gudun ta koina har anyaye ta,,yarinya me kyau me shiga rai ga gashinta dogo baki sidik daka ganta kasan jikar fulani ce,,,

A wannan lokacin ne kuma muhammadu ya samu aiki a garin kaduna na gadi saboda haka duka zasu tafi harda asabe da yaran yaso yabar jiddah amma asabe ta rura wuta sai da ya amsota,,,

haka suka tattara suka koma garin kaduna da zama a gidan suke zaune a BQ a lokacin ne jiddah ta fara shiga matsalar rayuwa duk da kuwa kankantar ta amma haka asabe ke mata mugunta kalakala,,ana cikin haka ne malam muhammadu ya sayi wani dan karamin gida da kudin da yake ajiyewa suka koma can,,,sun koma ba dadewa malam muhammadu ya fara ciwon ajali kwana2 yayi yace ga garin ku nan,,,asabe tayi kukan mutuwar shi nadan lokaci ta share ta cigaba da rayuwas itada yaranta,,,

mutuwarsa tasa jidda kara shiga matsalar rayuwa asabe sai taga damar bata abinci yawo take kamar almajira a cikin unw a lokacin shekarta 12 su rabi kam a lokacin anza entayi galan ana kawowa inna asabe kudi tana amshewa tana murna

ana cikin irin wannan rayuwar ne ALLAH ya jefo ammar cikin rayuwar jiddah ganin farko daya mata yaji ta shiga ranshi ga kuma tausayinta da yakeji saida ya tuntubi makota suka bashi labarinta tofa tunda ga wannan rana ammar ya fara kula da jidda da kansa ya sata a makaranta ya dinka mata uniform,,shike bata duk wata kulawa,,,inna asabe zata mai rashin mutunci ya nuna mata nashi rashin mutuncin yafi nata haka nan ta hakura badan ranta na so,,,,,

CIGABAN LABARI ku biyo a next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button