BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 91-100

Page* 9⃣0⃣ to 1⃣0⃣0⃣

Jefa kafar ta kawai take ba tare da tasan inda take nufa a da gidan maman salaha tayi niyyar zuwa amma yanxu saboda takaici da bakin cikin da take ciki yasa ta fasa kuma bata da niyyar komawa gida tana tunanin zuci tana share zazzafan hawayen da ke kwaranyo mata wai ita yau ake kira da karuwar gida kuma a gaban ta tabbas tasan ana zagin ta amma bata taba jin zafi irin na yau ba.

tsayawa tunanin ta yayi cak ganin wata tsohuwa kwance kamar mara lafiya a gefen titi ga yara na ta jifan ta wasu kuma suna watsa mata ruwa.

karasa tayi da sauri ta kori yaran yaran a wajen domin lokaci daya taji tausayin matar ya kamata.

bata nuna tana kyamar ta haka ta tallabo kanta wanda yake kamar tarin kudaje saboda dattin sa ko tsakar ba’a gani kayan jikin ta duk sun yafe kafar ta ko takalmu babu kana kallon ta kasan mahaukaciya ce.

tallabo kanta tayi jikin ta zafi rau sai rawar sanyi take sai da Jiddah ta zubar da hawaye saboda tausayi.

kirqm mansu take shirin yi a waya sai kuma ta tuna ai tabar wayar a gida dakyar taja,matar gefen wani gida sannan tace”mamah ki jira ni anan yanxun nan zan dawo bata jira amsar ta ta juya da sauri ta koma gida.

duk basa nan ba bata lokaci ta dauko wayar ta ta kunna number diin mansur ta fara dialing ta fada inda zai sameta abinka da me nema a duhu ba musu ya amsa da sauri.

yqndq tabar ta haka ta tarar da ita anan kwqnce kudaje sau bin ta suke saboda daudar dake jikin ta tausayin tane ya kara kamata.

tanq zaune haka sai ga mansur ya iso ganin ta da yayi a firgice haka yasa shi tambayar ta ko lafiya.

bayani take masa fuksa daure tana fada masa asibiti zasu kai wannqn baiwar ALLAHn ganin da yayi ba wasa a fuskar ta yasa shi amsawa da tow ba don ranshi ya so ba dan banda wari ba abinda wari ba abinda ke tashi jikin matar.

suna sakata a bayan mota suka nufi asibiti da sauri aka amshesu gado aka bata a aminity aka gama komai aka daura mata drip ba wqni abu bane ke damun illah yunwa abinda likitan ya gama fada musu kenan.

tayi alkawarin ba zata kara bari hakan ta faru ba tana jin matar a jikin ta kamar jinin ta kuma tqna tausayin ta matuka.

wuni curr tayi a asibitin sai yamma tayi niyyar tafiya gidah,saboda asibitin baa kwqna.

sai da ta tabbatar tabar komai da za’a bukata sannan ta tafi.

BAYAN SATI BIYU

A yanzu kam sai dai muce ALHAMDULILLAH jikin Anty yayi sauki sunan da Jiddah ke kiran ta dashi kenan domin kuwa yanzu fess take ba abunda ta rasa da kudin take mata komai.

amma yanzu an tabbatar da mahaukaciya ce hakan bai hana jiddah kaunar ta dan har ta gane ta wani bin zatayi hauka da ihu amma da zarae Jiddah taxo shikenan komau zai lafa.

duk wannan abinda ake inna asabe bata dq labari hankalin na gun Rabi dake kwanxe ba lafiya kuma an rasa me yake damun ta yanzu indo ce ke tashen iskanci shiyyasa inna bata lura ba.

antyn jiddah taji sauki saboda haka likitoci suka ce a kaita gidan mahaukata tayi na’am da hakan kuma.

daga nan asibitin suka wuce an gama komai an bata kaya dakyar aka raba su da jiddah itama kuka take dakyar aka lallaba suka rabu ita kuma ta wuce gidah.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button