BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 86-90

Page 8⃣6⃣ to 9⃣0⃣

Ammar dai har yanzu hankalin shi ya kasa kwanciya duk da saura 1yr ya kammala karatun sa.

duk inda yake tunanin zai samu labarin Jiddah abin ya faskara har Nura sai da ya kira a waya amma yace mai shi fa ko ganin ta baya yi.

har cikin zucyar sa yana tausaya ma Ammar domin haka yasa ya boye mai halin da Jiddah ke ciki dan yasan tabbasa sai idan har yaji to sai ya bar karatun shi ya dawo shiyya duka abokan su ba wanda yake fada masa gaskiya.

Haka suka gama waya da Nura bai samu wata magana akan Jiddah tunda ya ga haka ya tabbatar da ba lafiya ba kuma tunanin yafi karkata akan Asabe idan kuwa hakan ta tabbata ko bai kashe ta sai ta kare rayuwar ta a prision.

kwafa yayi tare da jan wani dogon tsaki wannan karatun shine duk ya sashi a damuwa amma da sai tafi Nigeria ya gano halin da masoyiyar sa ke ciki amma ba komai yana rokon ALLAH ya kare masa ita a duk inda take.

NIGERIA

Fitowar ta kenan daga toilet da alamu wanka tayi kai tsaye zama tayi a bakin gado tare da dauko wayar ta dake ta faman neman agaji dauka tayi amma kuma sai tayi shiru daga can bangaren aka fara magana haba Jiddah sarauniyar mata saboda yau duk na kashe wani aiki dake gabana ku…..katse shi tayi cikin zazzakar muryar ta ta fara magana”na fada maka yau babu inda zan fita amma sai faman naci kake min idan zaka iya jiran next week to idan kuma kaga yayi maka tsawo to sai ka kara haba bansan nacii wallahi.

haba sarauniya ayi hakuri ni ai ko na shekara zan iya jiranki meye wani week allah ya kaimu.

bata gamajin mai zaice ba ta katse kiran har zata ajiye wayan kiran Mansur ya kara shigowa kamar ba zata dauka sai da ya katse ya kara kira sannan ta dauka shima kamar yadda sukayi da wancan haka sukayi dashi zai fara mata magiya ta katse kiran tare da kashe wayan ma gaba daya.

shiri ta fara yi kamar me shirin fita gidan biki mamaki ni,kaina nake yi duk kuma inda tabi sai na bita da kallo ina kara mamakin wai wannan Jiddan ammar ce wannan er karamar yarinya marainiya me sanyin hali ita ce ta koma haka ku kanku readers nasan zaku yi mamaki.

ta zama wata big gurl fatar nan tata glowing kawai take saboda mayuka masu tsada da take using da shi gashin kanta ya kara tsawo dan har ya wuce gadon bayanta sai baki da ya kara gashi sai sheki yakeyi woww gaskiya dole maza su mutu a kan Jiddah domin kuwa ta koina ta hadu bata da makusa.

wani dogon wando tasa baki legis sannan ta dauko wara er top ta saka ta daure gashin ta duk da ba kwalliya a fuskar ta amma tayi matukar kyau.

cikin gida ta nufa inda ta tarar Inna Asabe zaune shirim kamar kayan wanki can nesa da ita ta zauna kafin tace”wai ina su Rabi ne”.

tabe baki tayi kafin tace su indo ni bansan inda suka je ba Rabi gata can har yau bacci take ni na rasa me take sha haka yake saka ta wannan mugun bacci kamar kasa.

dariya kawai Jiddah kafin tace”banda abinki Inna mutum ya wuni a waje me xai hana shi inya dawo gida ya huta ke matsalar ki kenan nima fa haka jiya kika min idan kudi kike so sai kiyi magana da wuri a baki.

tana gama fadin haka ta mike dan wani yalolon gyale da ya tsaya mata iya wuya shi ta yafa a kanta tayi waje a haka da wannan kayan da yake jikin ta.

harara Inna Asabe ta bita dashi tana tuno wani abu kuma ta fashe da dariyar mugunta tabbas boka na nakan tudu aikin ka yana kyau ta nemo min kudi ni kuma in kai maka ka karq lalata rayuwar ta.

isan har Jiddah bata yi yawo tsirara ba to tabbasa ban cika Asabe er halak kuma muje zuwa wannan kadan kika gani.

tafiya take a hankali kamar bata so kuma inda ta wuce sai anyi da ita masu zagi nayi masu addu’ar neman shiriya nayi ita kam ko a jikin ta bai dame ta ba dama gidan maman salaha yau taji tana son zuwa domun taji labarin ammar duka kwana2 har mantashi take.

wata majalisar maza tazo wucewa irin samarin nan area boyz da kallo suka bita kafin wani tsagera daga cikin si ya bude baki da karfi yace karuwar gidah anfito.

maganar ta daki ranta sosai dan har kwallah sai da tarun mata amma kawai ta share ta wuce zuciyar ta na tafasa.

Ur’s princes deejer????
[11/03, 18:00] 80k: ✨✨ BA DON SHIBA ✨✨

     *By*

KHADIJA AHMAD Princes Deejerh

AMEENTA WRITERS ASSOCIATION ????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button