FARHATAL-QALB

FARHATAL-QALB 18

PG:18

 Nadra ce ta shiga kitchen din. Hango Umma Hadiza tayi a kwance tanata baccinta hankali kwance, Tausayi ta bata. Ta rufo mata kofar ahankali don kada ta tashe ta.

Tana komawa parlor ba dadewa sai ga mahaifiyar su ta dawo, Dr. Hameedah. Bakinta dauke da sallama,

“Wa’alaykm Salam., Maaa”

“Naam Nadra.” Ta karasa fada a gajiye hadi da zubewa a kan kujera . Saboda madaukakiyar gajiyar data kwaso.

“Ban ruwa mara sanyi Nadra “

“Aha Màa.”

Da sauri ta dakko ruwan a wani mini cooler kaman fridge dake gefen side tables.

“Gashi.”

Karba tayi in da sauri tafara sha bayan tayi Bismillah. Sai data shanye tukun sannan ta yi hamdala.

“Ina Hadiza?”

“Tana bacci.”

“Allah sarki baiwar Allah.”

“Amma kitchen floor fa Maa.”

“Haba Nadra ya zaki bar ta ta kwanta a kitchen ? Bayan ga maids restroom nan .”

“Maa bansani ba fa. Kawai na shiga kitchen an ba dadewa naga tana baccin. “

“Ke tun dazu kina Ina?”

“Moha ne ya dame ni sena solving masa puzzle. So Ina sama.”

“Mtssss ” Dr. Hameedah ta saki tsaki hade da miqewa tsaye tayi kitchen din. Sam bataji dadin kwanciyar da Umma Hadiza tayi a tsakiyar kasan kitchen ba. Bayan ga dakin maaikata nan da suke hutawa da gado da kayan kallo aciki

“Hadiza… Hadiza.”

“Naam Hajia. ” Umma Hadiza ta tashi da sauri. Da ke batada nauyin bacci. Har damkwalin ta ya zame.Kanannadedden gashin fulani baqi wuluk me sheki ya bayyana.

“Kin dawo.,? Sannu da dawowa Hajia. Bacci ya dauke ni. A gafarce ni. ” Ta karasa fada kanta a kàsa.

“Haba Hadiza meye haka? Uhm?”

“Nayi lefi Hajia. Banda sharri na bacci ya kwasheni a wajen aiki na? Dan Allah k.”

“Ya isa haka mana Hadiza bar bada hakuri Dan Allah. Kaman wadda kikayi wani lefi? Dawowata kenan nima. Nake tambayar Nadra kina Ina tace kina bacci a kitchen. Kinji abunda yaban haushi kenan. Taya ga dakin maaikata nan da gado aciki. Meyakwan ta nuna miki. Tayi shiru.”

“Wallahi batada lefi Hajia. Don basusan ma nayi bacci ba Allah. Ni kai na na gama duk abunda zanyi. Sena janyo tabarma dake iska na busawa. Wallahi bansan sanda bacci barawo ya sace ni ba. Don ko a gidah bana wannan baccin. Naurar nan ce masha Allahu take ta busa ni. ” Ta karasa tana mai nuna air conditioner din dake buso sanyi

Dr. Hameedah tayi murmushi kawai.

“Muje na nu na miki dakin.”

“Da girman Allah Hajia baccin nan na gama shi haka nan. “

“Kinyi sallah?”

“A’ah. Anyi ne? Lalle na jima ina bacci.”

“Uku fa ta kusa “

“Kai! Lalle na jima. SubhanAllah; bara nayi alwala. “

“Ga dakin can da bandaki aciki “

“Toh Hajia.”

Bakinta dauke da sallama ta shiga cikin dakin. Kwarai matuka ya tafi da ita. Yanayin tsaruwar sa harda kayan kallo. Tamkar dakin amarya amman ace dakin masu aiki ne?

Ta jinjina kai tana sake yabawa da tsaruwar bandakin bayan tayi addua ta shiga ciki.

Ta kama ruwa hade da dauro alwala bayan ta kuskuro bakinta saboda baccin da tayi.

Tuni har an shimfida mata sallaya da hijabin sallah. Nan da nan ta ta zura ta fara sallah. Cikin nutsuwa da bin ka’idojin sallah.

Tana idarwa ta yi adduointa daga bisani ta mayar da komai yadda yake ta koma cikin parlorn.

“Hadiza kinci abincin dazun?”

“Eh Hajia. Bayan naci nema na kwanta.”

“Ko dan gaba ki dena kina cin abinci ki kwanta. Ki dinga bari se abincin yayi digesting first. “

“Dajastan.?”

“Afuwan. Ina son nace ki bari abincin ya ., Wannan . Sorry. ..Ah”

“Tanason tace ki dinga bari abincin da kikaci ya tsurga. Kafin ki kwanta ” cewar Nassem daya shiga alokacin.

“Oh yes. Tsurga.”

Umma Hadiza tayi murmushi

“Kingane ko Hadiza? “

“Nagane Hajia. Allah ya saka da alkhairi.”

“Aamin ya rabbi “

“Da akwai abunda zan kama kafin na tafi?”

“A’a babu. Ki tsaya kici abincin rana ko zaki tafi da shi kici a gidah ?”

“To Hajiya.”

“Okay great. “

Dr. Hameedah da kanta ta nufi kitchen din. Masu dafa abincin gidan har sun dafa sun kawo. Wata food flask ta dakko me girma ta zuba mata abincin aciki .

“Daga yau ga food flask din abincin ki Hadiza. “

“Hajia du wannan?”

“Eh…”

“Nagode. Allah ya saka da alkhairi. Abincin yayi yawa Hajia. Kinga na dazu ma na rage zan tafi dashi. Da kin rage.”

“Ki dena cewa haka Hadiza. Naga yaran naki ba maza bane. Sai mace daya dake zuwa makaranta ? Ko ta iya girki?”

“Eh su uku ne Hajia. Eh ta iya babu lefi.”

“To banason musu Hadiza. Kije kuci da yaran dan Allah kinji?”

“Toh Hajia. Allah ya saka muku da alkhairi. Yasa a mizani”

“Amin Hadiza “

Dr. Hameedah ta fice daga kitchen din. Yayinda Umma Hadiza ta sharce hawayen farin ciki. Ta zura hijabinta. Hadi da harhada komai ta zura a hijabi.

“To Hajia zan tafi. Sai zuwa da safen ko?”

“Allah ya kai mu Hadiza. Ki gayda yaran.”

“Zasuji insha Allah. “

Ta fuce daga cikin gidan tana mai kambama dattako irin na uwar dakin nata Haj Hameedah.

Har ta karasa gidah. Zuciyar ta bata dena yaba kyawawan halaye na Hajia hameedah ba. Tabbas an nuna mata karamci da tsantsar mutunci .

Ta shige gidan bakinta dauke da sallama. Zainab ta amsa tana kan kujera turmi agabanta tana dakan kuli.

“Umma sannu da zuwa ” cewar Waheedah data fito daga cikin daki

“Yauwa Waheedah. “

“Waye ne … Iyye?” Kande ta shiga kwarara murya fitowarta kenan daga bandaki. Zanin ya dage ana hango jemammun duwaiwukanta a waje. Bayan sarai tasan ummah Hadiza ce.

“Ni ce Marka.”

“Ah ni fa in ce naga anyi wuff an shige. Ashe sarki da nadi ce. An dandalo arziki an boye a kurya.”

“Kayya Marka kiyi hakuri. Ba haka bane.”

Ta yamitsa fuska bayan ta daga hannu ta nana shi a shamilallun cinyoyinta da ba tsoka sai kashi

“Kaji tsoron mutum. Wato Hadiza tunda aka samo miki aikatannan kike wani daga kai kina hura hanci. To bari kiji hurerar bappajo (mahaifiyar Umma Hadiza ) itace tsarar cacar baki na ba ke ba. Dande ta mutu ne da girman Allah da yau har gidan bappajon senaje mun kwashi yan kallo da ita. Mtssss! Aikin kawai.” Ta karasa fada hade da kwafa ta koma cikin bandakin

Jikin ummah Hadiza a sanyaye ta shige cikin dakin su. Waheedah nata rarrashinta. Duk yadda taso ta cije sai data kasa. Wasu zafafan hawaye suka shiga reto a fuskar ta. Domin dan aikin nan data samu ya tsolewa Marka idanu har bata iya boye hassadarta .

Dakyar da temakon Waheedah Umma Hadiza ta dena kukan . Ta kasafta abincin. Kuskus ne da jar miya dataji kaji da daffaffen kwai guda 3 . Ta ware musu nasu. Sannan ta dibawa Marka da na MalamNalado da na Inna Sa’adatu.

Ko da aka kaiwa Marka sam tace ba zata karba ba sai an canza mata da kashin hakarkari an saka mata cinya mai tsoka. A Kuma kara mata miyar.

Babu ma. Sai takan abicinta Umma Hadiza ta kalato ta karawa Markan Waheedah ta mayar mata ta karba. Tana danna loma tana aibata su

Inna Sa’adatu ma da Waheedah ta kai catai ba zata karba ba. Karamun dan tah hamisu yasa kukan seyaci. Sai data talle masa keya sau 3. Da karin rankwashi biyu a tsakar kansa. Sannan ta dungurar masa abincin a gaban sa hade da doriyar lailayo ashar ta dura masa

Su kuwa su Waheedah sunaci kunnuwan su na motsawa. Ga karin na safe na Zayn da aka barwa Umman na su dana kitchen da akace ta hade.

Su Najib sai yagar nama suke suna hadawa da abincin. Farin ciki marar misaltuwa ya bayyana a fuskokin su. Ciki harda Kamal da ke kwance a gefe shima yaci ba laifi.

Umma Hadizan nata basu labarin yadda ake mutinta ta agidan na THE ADAMS FAMILY!!!

❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????❤‍????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button