Labarai

Babban Burina Na Zama Shararriyar Mawakiyar Hip Hop -Lady Hany

Aminiya ta zanta da matashiyar mawakiya wadda ta zabi fannin wakar zamani da ake kira “Hip-Hop” wato gambara, inda ta bayyana yadda ta fara da kalubalen da take fuskanta da sauransu.

Ki bayyana mana takaitaccen tarihinki

To, sunana Ummi Kabir wacce aka fi sani da “Lady Hany” a masana’antar wake-waken Hausa na zamani. An haife ni a Unguwar Fagge Dogon Layi da ke
Kano. Na yi karatun firamare da sakandire a Fahad Memorial College.

Daga nan na shiga makarantar kiwon lafiya (School of Hygiene) ta nan Kano, inda na yi difloma a fannin Tsaftace Muhalli. Daga nan sai na shiga Jami’ar Maryam Abacha mai hadin gwiwa da Amurka dake garin Maradi a Jamhuriyar Nijar. Na karanta digirin farko a dai fannin kiwon lafiyar.

Mahaifina dan asalin Jihar Katsina ne. Ya fito daga zuriyar Sankaya, wato, gidansu Iyan Katsina Hakimin Mashi. Mahaifiyata Hausa Fulani ce ’yar Jihar Kano.

Yaya aka yi kika shiga harkar wakar?

Na fara sana’ar waka a fannin Hausa Hip-Hop tun 2018. Na hadu da Ricky Ultra wato, El Yakub Isma’ il. Fitaccen mawaki ne a masana’antar Hausa hip hop. Shi ne mutum na farko da ya fara
taimako na akan duk wani abu akan waka.

Ina matukar godiya a gare shi saboda ya yi mani taimakon da ba zan taba mantawa da shi ba a masana’antar wakoki.

Ke nan shi ya kwadaita maki shiga harkar wakar?

A’a. Tun ina yarinya nake da sha’awar wakoki domin ina sauraren wakoki kala-kala. Hakan ya sa har na fara sha’awar in ga na zama mawakiya.

Sannan dalilin yawan jin wakoki ya sa na fuskanci kalubale da yawa a rayuwata, musamman a lokacin da na fara wakar Hausa Hip-hop, wato gambara. Ka san kowace irin sana’a ta duniya tana da kalubale sosai, musamman a ce ka kai wani matsayi, to dole sai ka hada da hakuri da jin maganganun mutane. Sai ina zaune haka kawai wasu za su kira a waya ta bayan fage su rika zagina.

Kalubale na biyu da na samu a wannan
fanni shi ne, ina ji, ina gani, aka so raba ni da ubangidana. An je an same shi aka rika yi mani batanci a wurin shi. Da yake Allah Ya ga zuciyata ba ni da hakkinsu har ya kaddara ya daina daukar zugar da suke masa a kaina. Wannan shi ne kalubalen dana samu a harkar waka. A matsayina na mace a wannan fanni na sana’ar waka, gaskiya burina yana da yawa. Na farko ina son inyi sunan da duk wata kafa a duniya zata ji ni.

Me ake nufi da wakar Hausa Hip-hop?

Waka ce wadda ake rera ta kamar ta gambara. Tana da bambanci da wakar nanaye. Ita wajar nanaye za ka ji salonta daban ce. Ita wakar nanaye ana yinta domin nishadi, soyayya, ko fadakarwa.

Ina shi ubangidan naki, har yanzu kuna tare?

(Murmushi) Ai tun daga ranar da na hadu da Ricky Ultra na ji ya shiga zuciyata saboda halayensa masu kyau. A wurina, a duk fadin masana’antar wakoki babu mutumin kirki sama da Ricky Ultra.

Mawaka da yawa sun yi kokarin su shiga tsakanina da shi amma Allah bai ba su sa’a ba. Yau mun kai shekara biyar da haduwa da shi. Ina kuma yi masa addu’a Allah Ya kara daga darajarsa.

Kun taba yin waka tare?

Yanzu haka mun fitar da sabuwar wakarmu mai suna, “Zuma” kakashin jagorancin “Kry Music”, wanda a halin yanzun wakar tana ci gaba da zagawa a fadin duniya. Ricky Ultra ya fitar da ni a duniyar waka.

Ina batun yin aure, ko har yanzu fara tunani a kai ba?

Ina da burin aure, amma na fi son in auri ma’aikacin gwamnati. Kuma ka san shi aure lokaci ne. Ina addu’a Allah Ya kawo lokacin.

Ko akwai wasu nasarorin da za ki ce kin samu ta fuskar waka?

Sosai. Daga cikin nasarorin da na samu har da ta lashe gasar “WAAMA 2021” wadda aka yi a Babban Birnin Jamhuriyar Nijar. Na samu lambar a matsayina na mace mai kokari mawakiyar Hausa Hip-hop wadda aka zabo ta hanyar cancanta.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button