Labarai

Gwamnatin ta raba biliyan 101 ga asibitorcin sha-ka-tafi 7,600

Gwamnatin ta raba biliyan 101 ga asibitorcin sha-ka-tafi 7,600

 

Gwamnatin tarayya ta raba naira biliyan 101 ga cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko guda 7,600 daga asusun samar da lafiya da ga tushe, BHPF.

Asibiti

Dokta Chris Isokpunwu, sakataren kwamitin da ke sa ido kan ayyuka na ministoci, kan aikin BHCPF, a ma’aikatar lafiya ne ya bayyana haka a Abuja, a wani taro na kwanaki biyu da kungiyar gyara harkokin kiwon lafiya, HSRC, ta shirya a Abuja.

 

Taron bitar ya samu tallafi da ga Cibiyar Kasafin Lafiya ta Afirka, AHBN, da sauran abokan hulda.

 

Mista Isokpunwu ya ce an sakar wa BHCPF kuɗin ɗari bisa ɗari daga gwamnatin tarayya.

 

“Ya zuwa yanzu an raba kudaden ga cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko 7,600 a fadin kasar nan.

 

“Mun samu kuɗin da zai ishe mu rabo har zuwa Oktoba. Wannan ya kai kusan kashi 83 cikin 100 na kudaden da za a fitar a bana.

 

“Mun kuma samu ci gaba wajen yin rijistar adadin wadanda suka amfana da kuma bayar da kudade ga cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko 7,600 a fadin kasar nan.

 

“Duk da cewa ba za mu dauki rajistar wadanda suka ci gajiyar tallafin ba ko kuma bayar da kudade ga cibiyoyin kiwon lafiya a matsayin nasara, mun yi imanin cewa mun fara ganin tasirin wannan kudade,” in ji shi

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button