BABU SO HAUSA NOVELNOVELS

BABU SO 10

           ★★
  
     “To Alhmdllhi, indai banyi kuskure ba nan shine gidan”. Yaseer ya faɗa yana duban Anam da tunda suka baro asibiti ta kwantar da kanta jikin sit ta lumshe ido. Shiru bata motsa ba, yaɗan leƙa fuskarta yana murmushi da ɗan bubbuga gefen kujerar. Idanun ta buɗe a hankali ta kallesa. Kamar yanda yake mata murmushi itama saita ɗan sakar masa mai kama da yaƙe….
      “Nan ne ko?”.
Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa da narke mata idanusa. Janye nata tai daga garesa a ɗan daburce ta kalli gate ɗin. “Nan ne, na gode sosai ALLAH ya bada ladan zuminci”. Murmushi ya mata kawai ya buɗe ya fita. Side ɗinta ya zagayo itama ya buɗe mata. “Thanks”. Ta faɗa a hankali da ziro ƙafarta ƙasa zata fito idonta ya sauka akan Shareff da shima fitowarsa kenan daga gida hanunsa riƙe da key ɗin motarsa dake anan waje fake, ita sam bama ta lura da motar ba sai yanzu daya danna key tai ƙara. Ganin yanda ya kafeta da idanunsa ya sata yin ƙasa da nata ta ƙarasa fitowa gabanta na faɗuwa. Ɗan baya tai kamar zata faɗi saboda jiri Yaseer yay azamar kai hannu zai riƙota, dafe motar tai da sauri ta tsaya da ƙafafunta. “Ayya sorry Friend”. Yaseer ya faɗa a hankali yana janye hanunsa da bai kai ga taɓata ba.
     Ɗan satar kallon inda Shareff yake tai, yanzun kam zaune yake cikin motar sai dai ƙafafunsa a waje yana danna waya tamkar bai san da wanzuwarsu a wajen ba…..
     “Wancan ba Yaya bane?”.
Yaseer ya katseta yana fuskantar inda Shareff yake. Kanta kawai ta jinjina masa. “A to bara naje mu gaisa ko?”. Nanma batace komai ba, ganin ya nufi inda Shareff ɗin yake ita kuma gashi kwanciya kawai take buƙata, ga hararar daya mata sai kawai tai shigewarta gida…
         Shiru gidan babu gittawar kowa. Ta nufi sashen Mom da tunanin ko barci suke. Nan ɗinma shiru har ɗakin Mom ta leƙa bata samu kowaba, kitchen ta nufa inda take ɗan jin motsi. Iyami kawai ce tana ƙoƙarin ɗaura girkin rana. Gaisawa sukai kafin ta tambayi su Mom da hausarta da Iyami bawani fahimta take da ƙyau ba. Iyami ta bata amsa da cewar dukansu sun fita harsu Gwaggo amma batasan ina suka tafi ba. Fitowa tai ta shige ɗaki ta kwanta, ko mintuna biyu bata cika ba aka buɗe ƙofar, a tunaninta Iyami ce, sai dai kuma ƙamshin turaren da taji ya sata buɗe idanunta da sauri…
       Ido suka haɗa tai saurin janye nata ta maida ta rufe.
   “Tashi”.
  Sake buɗe idanun tai kamar zatai kuka, sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska yasata kasa musa masa ta tashi zaunen. Hanyar ƙofa ya nuna mata. Saita waro idanunta da suka canja launi na mura ga ƙwalla a cikinsu.
    “Banda lafiya fa Yaya. Ina zanje?”.
   Ganin ya nufota ta miƙe da sauri hawaye na sakko mata saman kumatu. A falo ta kusa faɗuwa saboda jirin dake ɗibarta, a bazata taji tattausan hanunsa cikin nata. Gaba ɗayansu sai da tsigar jikinsu ta tashi, sai dai babu wanda yay yunƙurin cirewa musamman ita dake buƙatar taimako dama. A haka suka fito har waje, ya taimaka mata da kansa ta shiga mota sannan ya zagaya nasa mazaunin, tana sonyin magana tana jin shakka dan haka tai shiru, saima ta kwanta abinta jikin sit ta lumshe idanu..
       Wani clinic ya kaita dan a dubata. Data sanar masa sunfaje asibiti wata muguwar harara daya wulla mata bata sake magana ba. Doctor ya rubuta musu magani fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallonsu da faɗin, “To amarya ALLAH ya ƙara afuwa kafin biki”.
     Idanu taɗan waro da kallon Shareff da shima kallonta yake, zatai magana ya harareta yana miƙama doctor hannu. “Thanks you doctor”.
     “No babu damuwa ango ALLAH ya ƙara lafiya sai ranar ɗaurin aure kuma”.
      Shareff ya saki murmushi yana jinjina masa kai. Yanzu kam bama ta jira sun jera ba tai gaba da sauri, koda ya fito harta buɗe mota ta shiga abinta. Sai da suka baro anguwar gaba ɗaya ya tsaya a wani babban pharmacy ya sayi magungunan da aka rubuta, ya kuma shiga gidan abincin dake gefen pharmacy ɗin yay mata takeaway. Duk batasan hidimar da yake ba saboda tunda suka baro asibitin barci ya ɗauketa, dan haka batasan inda suka dosa ba har sai da suka iso. Gefen kujerar yaɗan bubbuga, a hankali ta buɗe idanunta, ganin har ya fita ta yunƙura ta tashi, fitowa tai tana dube-duben inda suke “Yaya MM ina ne kuma nan?”. Bai tanka mataba, ya rufe inda ta fita yay gaba abinsa. Ƙara bin gidan tai da kallo, dagani dai sabone dan duk ma ga botikan fenti nan a tsakar gidan da kayan aiki, gabanta ya shiga faɗuwa, cikin zuciyarta take tambayar kanta (ina kuma ya kawota nan?)…..
       “Idan kika bari na dawo nan ALLAH sai kinyi kuka”. 
    Da ƙyar ta iya ɗaga ƙafa ta nufi inda yake, koda ya buɗe ƙofar da key matsa mata yay ta fara shiga, ƙamshin sabon fenti dana sabbin furnitures ya daki hancinta. Sosai falon yay mata matuƙar ƙyau, danma ciwon kai ya hanata damar kallon komai da ƙyau. Ganin tana neman kaiwa kwance ya dakatar da ita. “No tashi kici abinci kisha magani first”.
       “Yaya banajin yunwa kadai ban maganin kawai”.
     “Dole kici abinci, kin taɓa ganin ansha magani ba’aci abinci ba”.
Yanda yay maganar babu wasa yasata yin shiru. Ya buɗe mata abincin tare da tura mata gabanta, “Kafin na fito ki tabbatar kinci”. Da kallo kawai ta bisa harya shige ƙofar daya buɗe….. Kusan mintuna goma sai gashi ya fito, ganin ya canja kaya yasa ta kasa haƙuri. “Yaya Shareff ina ne nan?”.
      Batare daya kalleta ba yakai zaune cikin kujera da faɗin, “Gidan ƴan shan jini”. Shiru tai, dan tasan baƙar magana ya mata. Ɗagowa yay yaɗan kalli abincin, ganin taci sai baice komaiba yaja ledan magungunan. Da kansa ya ɓalla ya bata, duk ta amsa tasha dan sam bata tsoron allura bare ƙin magani. Ganin zata kwanta a kujerar ya sashi faɗin, “Tashi kije ciki ki kwanta”. Kallonsa tai kamar zatai magana sai kuma ta haɗiye abunta ganin yanda kicin-kicin da fuska. Ya bita da kallo ta ƙasan ido harta shige, ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido ya buɗe yana furzar da ɗan huci. Sai kuma ya miƙe ya fita.
      Gidan ya shiga zagayawa, dan jiya masu fenti suka ƙarasa na katanga. Bai kuma samu shigowaba sai yanzu. Komai yayi masa yanda yake buƙata, shi kansa ya yaba da gidan duk da shine ya zana abinsa companynsa kuma ya fidda kayan aikin ginashi. Yanzu amarya kawai gida yake buƙata nanda kwanaki bakwai insha ALLAH. Motarsa ya nufa ya ɗauka lap-top ya koma ciki. Haka kawai yake jin nishaɗin zama a cikin gidan yau, saɓanin ƴan kwanakin nan da duk yake jin ransa a dagule, dan kayan sashen nasa ma sai da Mommy ta masa jan ido ya bada damar shirya masa su dan ita da kanta tai order ɗin komai tamkar itace mai aurar da macen ba namiji ba. Komai saida ta haɗa masa. Tunda kuma aka shirya kayan baizo ya zauna kamar haka ba……
    Ring da wayarsa tai ya sashi katse aikin da yake famanyi a laptop ɗin ya ɗaga. A tausashe yace, “Mommy barka da rana”. Daga can Mommy ta amsa masa da “Barka dai son kana ina ne?”. Ɗan jimm yayi kafin yace “Mommy kina son ganina ne?”.
      “Eh to kusan haka, amma idan zaka iya aika wani gidanka ya kai mana keys ma basai kazo ba. Dan gamu a hanya zamuje dasu gwaggo gidan, sannan Halima tai kirana ma danginmu na wajen baban Fadwa zasuzo da masu Company da zasu shirya kayanta su auna komai, shiyyasa muka yanke shawarar muzo muma ɗin kawai dan babu daɗi dangin uba kawai ko?”.
        Tun fara maganar tata zuciyarsa ke faman bugu da sauri, ya ture laptop ɗin cinyar tasa gefe, cikin dauriya da danne halin daya shiga yace, “Okay Mommy! kuna inane yanzu haka?”.
       “Ai gamu ma mun shigo street ɗin gidan naka kamar dai in ban mantaba”.
     Goshinsa ya dafe yana ambaton “Ya ALLAH a hankali”.
         “Mi kace?”.
  “No Mommy, canai ALLAH ya kawoku lafiya ai inama gidan nima na shigo ganin aiki daga nan na ɗan huta”.
     “Kaji ja’iri, bama ka bari iyayen naka su kaika ganɗoki muje biki”.
    Ƴar dariyar yaƙe kawai ya mata da faɗin, “Sai kun iso”.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button