BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO….. 11

Typing????

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

11

…….Ɗin! Ɗinn!! Horn dake nuna alamar isowar dangin amarya Fadwa ya saka Gwaggo juyowa baki a washe tana faɗin, “A to ga masu ganin gidan nan ma sun iso ai? Kai Alhaji ƙarami muje ka buɗe musu ƙofa ɗin saina tarbesu ai ko”.
      A hankali ya lumshe idanunsa da sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Mommy ma bin bayan Gwaggo tayi, suma su Mom sai suka bisu kawai dan abu kaɗan zai iya jawo Gwaggo taita surutu. Har zai bisu ya dawo da baya, zuciyarsace ta bashi shawaran ya sakama ƙofar key, dan haka ya kulle da sauri ya fidda key ɗin ɗakin a cikin keys ya saka aljihu sannan yabi bayansu…
       
       Mota uku ce a jere kai kace jeren kayan sukazo. Motar farko Fadwa ce ta fara fitowa a ciki, sai ƙawayenta uku. Ta biyu kuma ƙannen babanta ne su biyu da cousin ɗinta biyu suma dai duk masu aure ne. Sai aminiyar Gwaggo Haliman. Motar ƙarshe babban yayan Fadwa sauran kuma ƴan kamfanin da zasuyi aikinne dan motarma akwai tambarin kamfanin. Cikin mutunta juna aka gaisa tunda dama akwai alaƙa, kafin su ɗunguma gaba ɗaya zuwa can. Fadwa sai satar kallon Shareff take amma yayi kicin-kicin kamar ma bai ganta ba. Dama tun waccan ranar ko kiransa tai baya ɗagawa, idan tai masa magana koda yana a online kuwa ko buɗewama bayayi. Tabi duk hanyar daya dace su sasanta amma yaƙi kulata dan yayi alwashin koya mata hankali a wannan karon.
     Ko’ina sai da suka shiga kowa na yabawa dan gida kam yayi sai dai maƙiyi. Ma’aikatan kamfanin da zasu saka kayan kuwa nata faman gwaje-gwajensu tunda dama amarya ta gama zaɓar wanda take buƙata tun a gida. Zare jikinsa yay ya koma sashensa batare daya amsa tambaya ko ɗaya ba akan ɗayan sashen dasu Gwaggo sukai magana suma. Shi dariya ma suke bashi da mamaki, ina ruwansu da sashen to tunda basu suka basa kuɗin ginin ba, sashen dama ko ƙarasa masa ayyuka ƙananu ba’aiba ya tsolema kowa ido.
    Baifi mintuna biyar da shigowa ba Fadwa ta biyo bayansa. Bai nuna alamar yasan da shigowar tata ba. Duk da shariyar tasa ta sosa ranta sai ta shanye ta shiga yaba yanda sashen nasa yay matuƙar ƙyau shima. Yanda tsarin ya kasance na black and milk da ratsin ash ya matuƙar ƙayatarwa.
      “Soulmate!”.
Ta kira sunansa a hankali tana kaiwa zaune kusa da shi. Bai amsa ba, bai kuma ɗago ya dubeta ba yanata aikinsa kamar yanda ta samesa. Murmushin takaici ta ɗanyi tana kallonsa, ta lumshe ido ta buɗe akansa zuciyarta na raya mata abubuwa masu yawa dan ba ƙaramin haɗin kayan mata tasha ba. Sake matsawa tai jikinsa a kasalance ta ɗaura kanta a shoulder ɗinsa ta saki kuka.
      Cak ya tsaya da aikin da yakeyi, yaja numfashi ya fesar yana mai rufe idonsa da buɗewa a lokaci guda…..
          “Dan ALLAH kayi haƙuri ka daina fushi dani haka nan Yaya Al-Mustapha. Karka manta kwanaki takwas kacal ya rage mu zama abu guda, ina buƙatar ganin murmushi a fuskokinmu yayinda jama’a zasu fara taruwa dominmu daga gobe. Naji nayi laifi kuma na amsa na kuma bada haƙuri bazan sake ba mijina”.
      Kalamanta sun ɗan saka masa sassauci, sai dai baida alamar cewa wani abu a zahiri. Kanta ta ɗago daga kafaɗarsa tana kallonsa idanunta na rige-rigen matso hawaye, ta riƙo hanunsa dake dafe da lap-top har yanzu sai dai ba aikin yake ba. “Baka haƙuraba ko My Soulmate? Shike nan na baka damar kaimin kowane irin hukunci amma dan ALLAH banda naƙin kulani na tuba”.
       Karon farko ya ɗago idanu ya dubeta, kafin ya maida ga hanunsu dake cikin na juna. Nasa ya janye tare da ɗan bada tazara daga kusancinsu. “Naji ya wuce, sai dai ki tabbata kika sake hukuncin dazan ɗauka bazakiji da daɗi ba. Ni da ke zamu zauna bada iyayenmu ba, dan haka matsalarmu mune ya kamata mu fuskanceta basai wasu sunyi alƙalanci a ciki ba”.
      “Insha ALLAHU zan kiyaye mijina”. Tai maganar tana faɗawa jikinsa ta rungumesa. Hannu yasa ya janyeta. “Nasha faɗa miki bana son ɗabi’ar nan sam. Domin babu wani hallaci daya halatta hakan garemu”.
           “To kayi haƙuri, amma karka manta kwana takwas ya rage kacal mu zama ma’auratan ai ko, kaga kenan akwai banbanci da da yanzun”.
    “Sai ki bari sai mun zama ɗin, a yanzu dai haramunne”.
     “Hummm” kawai ta faɗa dan bata bukatar su sake wani rikicin kuma saboda kar yay amfani da damar yaƙi halartar duk events da suka shirya gara ta lallaɓasa ayi a tashi lafiya karya kunyatata ga ƙawayenta. “My Soulmate bara na ɗanyi using toilet Please”.
     Ɗagowa yay ya ɗan dubeta dan harya sake maida kansa ga aikin gabansa. “Yanzu a barowanki gida har sai kinzo wani waje kin shiga toilet?”.
           Murmushi tayi daya sake ƙawata ƙyawun fuskarta. “Oh My Soulmate nan ɗin aiba wani waje bane na daban, shine fa gidana nanda kwanaki kaɗan zan dawo rayuwar cikinsa. Bawani abu zanyiba part zan canja dan bana iya wuce awa ɗaya da shi a jikina”.
      Idanunsa ya ɗauke daga kallonta, haka kawai yaji wani iri a ransa ganin babu ko ƴar kunya tattare da ita take faɗin part zata canja. Da hannu ya nuna mata toilet na falon.
           “Ah-ah my Soulmate bara dai na shiga bedroom mana. Nan kuma idan cikin su Mommy wani ya shigo fa”. Komai baice mata ba, harta nufi hanyar bedroom ɗin Anam dake barci a ciki ta faɗo masa. Dakatar da ita yayi. “No ki shiga wannan ɗin can ƙofan nada matsala ne, sai angyarasa a rufe yake”.
    “Okay! To bara naje naga bedroom ɗin namu ko?”. A ɗan kausashe yace, “Shi nake nufi”. Ɗan jimm tai tana kallonsa. Sai kuma tayi murmushi cikin rausaya kai ta nufi na falon kawai. Shima aikinsa ya cigaba dayi, a zuciyarsa yana ALLAH-ALLAH su kammala su tattara subar gidan.
       Addu’arsa kam ta karbu, dan koda ta fito bata zauna ba kasancewar ƙanwar abbanta nata faman kiranta a waya akan ta fito zasu wuce.. Tare da shi suka fita, yaji daɗi sosai da su Mommy sukace suma zasu wuce ne magrib na gabatowa.

     Bayan duk wucewarsu ya dawo ciki, kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa, key ɗin daya cire yasa ya buɗe babu zato ko tunanin ta tashi a ransa…. Kusan a tare ƙofofin guda biyu suka buɗe. Shi yana shigowa ita tana fitowa daga bathroom. Wata irin ƙara ta fasa da ƙanƙame guntun towel ɗin data ɗauro a jikinta dake ɗigar ruwa tareda faɗawa saman gado ta cukuykuye zanin gado da duvet ɗin gaba ɗaya a jikinta….
        “you are vary stupid!!”.
Ya daka mata tsawa jin tana barazanar fasa masa dodon kunne.
     “Na shiga uku ni dai ka fita, dan ALLAH ka fita, Yaya wlhy babu ƙyau ganin tsiraicin wani. Wayyo ALLAH Mamie banji maganarkiba nashiga halaka…….
    “Shut up! Stupid!”.
Ya sake faɗa da matuƙar takaicinta. Bedsheet ɗin ta tusa cikin baki tana gyaɗa masa kai ga hawaye na faman mata gudu a fuska kai kace wani abu yace zai mata. Shiko gaba ɗaya idanunsa sun birkice dan takaici, ya ƙarasa takowa gaban gadon yana watsa mata mugun kallo. “Ubanwa ya saki yin wanka anan ɗin? Ko an faɗa miki nan gidan wanka ne?”. Kanta take girgiza masa tana ƙara maƙurewa waje guda, dan ita a yanzu ba faɗan nasa take tsoro ba a yanda ya ganta da a yanda take. “Dan ALLAH kayi haƙuri Yaya. ALLAH zafine ya dameni kamar fatana zai ɗaye zufa ya jiƙani ina ƙyanƙyami shiyyasa nayi”. Rasama mizai ce mata yay, ga jikinta sai rawa yake matuƙa. Tsaki yaja ya juya ya fita kawai. “Mintuna biyar na baki”. Ya faɗa dai-dai yana jan ƙofar har saida ta zabura saboda bugata da yay.
      Kanta ta cusa tsakanin ƙafafunta ta ta sake sakin wani kukan na baƙin cikin ya ganar mata jiki abinda wani mahaluki bai taɓayiba bayan Aunty Mimi da Mamie. Duk da bawai tsirara ya ganta ba a ganinta ƙanƙantar towel ɗin baida maraba da hakan ita kam. Tuna abinda ya faɗa na karshe da yay yasata zabura. Durowa tai a gadon ta nufi ƙofar ta saka sakata, da sauri ta kwashi kayanta duk da ɗunbin ƙyanƙyamin da take musu ta shiga maidawa a jikinta da sauri-sauri. Bata kammala ɗaure igiyar abayar jikinta ba ta fito. A falo ta samesa tsaye sai faman kai da kawo yake tamkar mai safa da marwa. Tai ƙasa da kai dan a yanzu kam babu abinda take gudu kamar su haɗa ido, wani irin matsanancin kunyarsa takeji har ƙarƙashin zuciyarta. Shima bai dubi inda takenba ya nufi bedroom ɗin nasa, bai koyi mintuna biyu ba ya fito da kayansa da sukazo gidan suna jikinsa. Magungunanta da lap-top ɗinsa ya ɗauka yay waje. Da sauri tabi bayansa dan dama kamar jira take ace ar ta kwasa ana kare.
        A motar ma hankalinta ta maida gaba ɗaya waje badan tana fahimtar abinda take kallo ba, sai dan bata buƙatar koda kallonsa. Shima ɗin dai aikin tuƙinsa yake kawai lokaci-lokaci yakan amsa waya har suka iso gida. Yana gama parking ta fice. “Waye zai biki da wannan?!”. Baya ta dawo kanta a ƙasa ta ɗauka ledar magungunanta daya ɗaura saman mota ta wuce har tana harɗewa saboda yanda take tafiya da sassarfa.
     
     ★★★★

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button