BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 13

Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

13

……….Gab da magrib aka kawo amarya Fadwa, kamar yanda Daddy ya bada umarni nan gidan aka kawota wajen Mamie. Hakan ba ƙaramin zafar Mommy da su Gwaggo Halima da aka kira aka sanarwa abun yayi ba. Gwaggo kuwa kasa shiru tai sai da ta tanka, Daddyn yace ya gama yanke hukunci, miye ma abin magana bayan gobe idan ALLAH ya kaimu za’a maidata gidanta. Badan rigimar ta kwantaba akai daiyi shiru kowa yaje ya fara shirin tafiya dinner.
     Bayan sallar isha’i aka fara kwasar mutane inda za’a gudanar da dinner, sai dai har aka gama kwashe kowa babu Anam babu alamarta. Hasalima tuni taje tai kwanciyarta a falon Abie batare da kowa ya sani ba. Wajen dinner ya ƙayatar matuƙa. Amarya da ango sunyi ƙyau har sun gaji. Anci ansha ƙawayen amarya sun sami yanda sukeso suda amarya wajen daukar hotuna da videos wasu har live suke ɗauka ana kaiwa tiktok. Nera tayi kuka kamar yanda aka zubar da mutunci galan-galan dan anci rawa casss da warrr ƙawayen amarya ta rashin mutunci, amaryar kanta ta cashe kamar babu gobe, sai dai rashin yin rawar ango ta jawo cece kuce sosai dan wasu na ganin amarya Fadwa ta zaƙe da yawa. (Komadai miye ni ina ganin ranar farin cikin tace a barta ta shana????). Ƙarfe sha biyu taro ya tashi lafiya aka kwaso jama’a aka dawo gida.

    WASHE GARI aka gudanar da walima tare da yinin biki anan gidan, yini guda babu wanda zaice yaga Anam sai Mamie kawai da aunty Mimi, dan tana falon Abie kwance babu lafiya zazzaɓi ta kwana da shi har sai da doctor yazo ya dubata da safe ma, dan haka yau ko kwalliyar bikin ma batai ba abinta. Lokacin da taji sallamar Shareff zai shigo falon wajen Abie tashi tai ta gudu bedroom ɗin Abie ɗin, tanaji yana faɗama Abie baida kafiya shima da ciwon kai ya kwana kuma har yinin yau ɗin bai sakesa ba yana ganin hayaniyar nan ce. Baki ta taɓe cikin rashin damuwa tai kwanciyarta har sai da taji ya fita. Har dare bata sauka ƙasa ba dan bata buƙatar ganin Fadwa har tabar gidan. Hakan kuwa akayi, dan washeri lahadi akai buɗan kai bayan sallar azhar. Anayin la’asar aka ɗunguma raka amarya Fadwa gidanta, yayinda a bangaren ango yaketa ƙoƙarin sallamar abokansa na nesa da zasu wuce gida yau. Hakama baƙin nan gidan wasu daga rakkiyar amarya bazasu dawo nan ɗin ba…
       Gidan amarya kam sai sambarka. Komai yaji zam masha ALLAH. Har kusan bayan magrib sannan mutane suka gama watsewa aka barta ita da ƙawayenta kawai dake jiran abokan ango…..

      ★★

  “Wai nikam wane irin ango ne kai Al-Mustapha? A irin wannan ranar irinka ɗoki da zumuɗi baya barinsu amma kai tun ɗazun sai fama ake da kai ka shirya a rakaka kanata jamana aji”.
        Duk da sarai abinda Dr Jamil ɗin ke faɗa yana shiga kunnensa tunda a kusa da shi yake amma babu alamar zai motsa. Sai cigaba da danne-dannen tab ɗinsa yake hankali kwance. Fharhan dake faman musu dariya ya miƙe ya fige tab ɗin. Ɗagowa yay yana harararsa da miƙa hannu, Isma’il ya amshe tab ɗin daga hanun Fharhan shima yana dariya. “ALLAH baza’a baka ba. Garama ka tashi kaje ka shirya mu miƙaka muma muje musa haƙarƙarinmu a katifa matanmu na jiranmu.”
       Isma’il ɗin ya kafe da idanu kamar zaiyi magana sai kuma ya girgiza kai kawai. Dr jamil ya dafa shi, “Wai nikam Musty ko tsoron amaryar kake ne? Idan akwai matsala inada kayan gyara masu inganci wlhy da zaka baje kolinka babu ragi babu ragowa”.
      Naushi ya kaima Dr Jamil, da sauri ya duƙe yana dariya su Fharhan na tayasu. Hararsu yay da miƙewa ya shige bedroom. 

       Jin gidan ya rage hayaniya sosai ta sakko downstairs. Su Mamie ne kawai zaune da ƙannenta, gaishesu tai kowa na tambayarta ya ƙarfin jikinta. Tace da sauƙi tana zama gefen Mamie ta kwantar da kanta a kafaɗarta. Ko mintuna uku batai da zama ba suka shigo da sallama. Shine a gaba cikin ɗanyar shadda milk color sai ƙyalli take harda hula a kansa. Sai su Fharhan biye da shi. Jitai kusan su dukansu idanunsu akanta suke kamar ta tashi ta arta da gudu, sai dai ta dake dan bata fatan sake tafka abin kunyar datai a ranar ɗaurin aure????.
       Sai da suka gama gaisawa da su Mamie Dr Jamil dake jin kamar ya haɗiyeta fuska ɗauke da murmushi yace, “A’a Anam banda ke a kai amaryar kenan?”.
      Kanta ta jinjina masa tana ɗan murmushi batare data kallesu ba. “Banda lafiya ne shiyyasa”. Ta faɗa a hankaki tana ƙara sinne kanta jikin Mamie.
          “Ayya ai ban sani ba dana kawo ɗauki. Yaya jikin yanzun?”.
  “Na samu sauƙi”. Ta faɗa a taƙaice tana ɗan ɗagowa. Cikin idonsa natan suka shige, tai saurin janyewa ƙirjinta na bugawa da ƙarfi….
      “My son kuje kar dare yayi an bar ɗiyata ita kaɗai, ALLAH yay muku albarka, ya bada zaman lafiya na har abada. Ayi haƙuri ayi haƙuri ayi haƙuri. Mu mata a duk inda muke haƙuri ake damu akan komai dan halittane masu wahalar sha’ani. Banda yanke hukunci cikin fushi, duk abinda aka gani ba dai-dai ba abu asannu a ruwan sanyi a kawo maslaha a cikinsa. Ayi ƙokurin sauke duk hakkin da ALLAH yace duk da bani da damuwa a kanka game da wannan. ALLAH ya azurtaku da zuri’a masu albarka”.
      Gaba ɗaya suka amsa da Amin. Anam dai ma ta maida hankalinta ga wayarta kamar bata jinsu. Ƴan uwan Mamie ma sun masa tasu nasihar suka sallamesu dan dare na ƙarayi. Dai-dai yana mikewa suka ƙara haɗa ido da Anam data ɗago itama. Wani kasalallen kallo suka sakarma juna. Ta kauda kanta tana taɓe baki zuciyarta na mata zafi. Shima iska ya ɗan furzar yana janye nasa a wani yanayi. Bata sake yarda ta ɗago ba har suka fice Dr Jamal na faɗa mata sai yazo dubiya ta musamman. Bata tankasa ba, sai Aunty Nasara dake kamar ƙanwar Mamie ta bashi amsa cikin dariya.
      Tsam ta mike tabar falon dan ji take wani ɗan zazzaɓi ma na neman rufeta, ta nufi ɗakinta da fatan su Aysha su kwana a cikin gida yau bata bukatar su anan……

MONDAY MORNING

          Tana tsaka da barcinta na safe mai daɗi kasancewar bata samu yin na dare ba sosai saboda zazzaɓi mai zafi data sake kwana da shi aunty Mimi ta tasheta akan ta tashi ta shirya za’a aiketa.
      “Wayyo aunty ina su Aysha ki aika a kira miki su suna cikin gida fa ALLAH bana jin daɗi”.
         Hararta Aunty Mimi tayi. “Ai nasan dasu Ayshan na tasheki. Maza tashi kina ɓatamin lokaci. Da ƙyar ta miƙe ta shiga bayi kamar zatai kuka. Wanka tai da ruwa mai ɗumi dan duk son sanyinta kuma bata wanka da ruwan sanyi. Gudun masifar aunty Mimi ya sata shiryawa a ɗan gurguje cikin shigar da tafi so a ko yaushe wando da riga ta ɗaura abaya pink a sama ta naɗa veil ɗin abayar. Tayi ƙyau sosai sai zuba kamshi take duk da bawani kwalliya tai mai yawa ba. A falon ƙasa ta sameta har su Mamie wanda suka makara nata breakfast. Gaishe dasu tai tana karasawa inda Aunty Mimi take.
      “Yauwa ɗiyar albarka. Ai jeki kawai waje ga Ikram can na jiranki a mota da driver ”.
    “To aunty saƙon fa?”.
“Yana wajensu a motar”.
Kai kawai ta jinjina taima su Mamie sallama ta fita. Baya ta buɗe ta shiga yayinda Ikram ke gaba tanata zubama driver surutu da hausanta da bata iyaba wai ita a dole koyan hausa takeyi. Itace autar aunty Mimi shekararta goma sha uku, kasancewarta girman turai sai take abu kamar wata yarinya ƙarama ga tabara ta autoci.
      “Good morning aunty Anam”.
Ta faɗa lokacin da Anam ke ƙoƙarin rufe murfi. “Morning dear how are you?”.
    “Am fine, sai ƙafana dake ciwo saboda rawan da mukai a wajen dinner ranar”.
         “Good for you”.
“Kai aunty maimakon kimin sorry”.
    “Tunda ni na aike ki”.
Dariya Ikram tayi. Sai kuma ta shiga bata labarin yanda shagalin dinner ya kasance. Shiru Anam tai mata, da taga zata isheta sai ta buɗe bag ta ɗakko bluetooth ta saka waƙa har suka iso gidan da bazata taɓa iya mantawa ba. Kasa motsi tai balle magana har driver yay horn maigadi ya buɗe masa gate suka shige. Jitai kanta na juyawa, ta dafesa tana ambaton sunan ALLAH. Da tasan nan aunty Mimi zata aikosu da duk ma yanda zatai taƙi zuwa ALLAH da sai tayi. Yanzu kuma tana ƙin shiga wannan akku sarkin zancen zataje ta bazata a fassarata a mai baƙin ciki. Siririn tsaki taja da buɗe motar a fusace ta fita dan Ikram tuni ta fice har driver ya buɗe mata booth suna fidda kayan breakfast da sukazo da shi. Ƙin daukar komai tai sai driver da ikram ɗinne suka kwasa.
        Daga can baya ta tsaya Ikram ta shiga yin knocking tana kiran sunan Yaya Shareff. Sun kai kusan mintuna goma sha sannan aka buɗe har ta gama yanke shawarar juyawa ta koma. Shine ya buɗe ƙofar Ikram ta riƙo hanunsa cike da shagwaɓa. (Wayyo Yaya ƙafafuna har zafi suke da hannuna”.
      Kanta ya dafa da rufe idonsa daya nuna alamar a barci ya tashi yana buɗewa. Ya matsa mata alamar ta shigo yana maida dubansa ga Anam datai tsaye tana kallon wani waje daban. Kusan minti ɗaya yana kallonta ko ƙyaftawa babu sannan yay magana.
    “Tsaiwar ta miye?”.
  Baki ta taɓe tana ƙara tsuke fuska. Batare da tace komai ba ta nufosa. Harta ƙaraso idonsa na kanta yanzu ma. Ya ɗan matsa mata alamar ta shiga itama. Ɗagowa tai suka haɗa ido, tai saurin janyewa da raɓashi ta shige tana murguɗa baki. Shine ya shiga da kayan cikin falon da kansa, Ikram sai faman yaba falon take dan babu ƙarya naira tayi kuka. Itako tana tsaye tamaƙi zama, ta dai jingina da bango tana daƙilar wayarta.
    “Ina kwana”.
Ta faɗa batare data yarda ta kallesa ba. Bai amsata ba, sai hankalinsa daya maida ga Ikram da bakinta yaƙi shiru. Haushi ya ƙara kume zuciyarta, gashi ta fara gajiya da tsaiwar, amma sai ta cigaba da daurewa. Kusan mintuna biyar yana biyema shirmen Ikram tamkar ma ya manta da ita a falon. Ƙaton agogon dake bangon falon ya duba, tare da dawo da kallonsa gareta.
      “Bani plate a kitchen”.
   Kallonsa tai da mamaki, sai kuma ta sake ɓata fuska. “Ni ban san kitchen ɗin ba”. Da hannu ya nuna mata ya ɗauke kansa. Kitchen ɗin ta nufa wani haushi na ƙara turniketa, cikin taɓe baki take bin ko’ina na kitchen ɗin da kallo. Tabbas yayi ƙyau, sai dai hakan ba yana nufin wani abu na cikinsa ya burgeta ba. Abinda ya aikota ta nufa ta ɗauka, sai dai ta nufi sink dan ta ɗauraye, sai ƙunƙuni takeyi da bazaka iya sanin mitake faɗa ba. Juyowa tai tana jan tsaki, da sauri taja baya har plate ɗin na neman suɓuce mata. Duk ta daburce dan sam bata san ya biyo bayanta ba, ga idanunsa masu kaifi daya kafeta da su. A hankali ya tako gabanta duk hannayensa cikin aljihun jallabiyar jikinsa, ya tsaya dab da ita har tana iya jin hucin numfashinsa. Sai taji gaba ɗaya kwarjininsa ya cika wajen har bata shaƙar numfashi a wadace…
      “Ya jikin ki?”.
   Yay maganar cikin taushin muryar da bata taɓa ji daga garesa ba. Kasa jurewa tai sai da ta ɗago ta kallesa. Har yanzu idanunsa a kanta suke, tai saurin janye nata tana girgiza kanta. Muryarta da ɗan rawa tace, “Alhamdulillahi”.
      “Kin tabbatar?”.
   “Nifa zazzaɓi ne dama kawai Yaya MM”.
       Jin baice komaiba ta ɗago ta dubesa, still dai har yanzu idonsa a kanta. (Ya ALLAH! lafiyarsa kuwa?) ta ayyana a ranta tana ƙoƙarin son barin wajen. Amma sai furucinsa ya sakata dakatawa babu shiri.
          “I’m sorry”.
    Kasa yarda tayi daga bakinsa furucin ya fito, musamman da babu alamar shi ɗin ya faɗa a yanayinsa. Sannan bata san dalilinsa na faɗarba. Kamar ya fahimci ƙarin bayani take buƙata sai ya bar wajen cike da basarwa. “Zoki dafamin lipton”. Shiru bata motsa ba, da alama bata tare da tunaninta ma. Ya juyo ya dubeta fuska a tsuke. “Badake nake magana ba!”. Itama fuska ta haɗe, sai dai cikin sanyin murya tace, “Yaya matarka fa?”.  Ido ya tsura mata na wasu sakanni, sai kuma ya janye. “Nasan da ita ai na sakaki. Sannan ganin amarya a kicin irin wannan ranar kema kin san bamai yuwuwa bane”.
      Da hausa yay maganar, dan haka ba komai ta fahimta da ƙyau ba. Amma sunan amarya kawai daya shigo ciki ya saka yanayinta ƙara canjawa. Sai dai bata sake cewa komai ba, ta ɗauka tunkuyar daya fiddo mata domin dafa shayin ta ɗauraye, ruwa ta zuba dai-dai shan mutum ɗaya, tana ƙoƙarin rufewa taji tsaiwarsa a bayanta, kafin tayi wani yunƙuri ya janye hanunta da sake buɗe murfin ya buɗe fanfo ya ƙara ruwan.
      “Nadai bazan dafama wata ƙatuwa shayi tana kwance tana barci ba”.
  Karon farko ya saki murmushi, sai dai komai baice ba ya rufe mata tukunyar. Zata sake magana ya dakatar da ita. “Zakimin abinda na saki ko tsiwa? Trouble maker!”.
      “Ga babbar Trouble maker can ka bari a ɗaki”. Tai maganar ƙasa-ƙasa yanda bazaiji ba. Da kansa ya kunna mata gas ɗin, ta ɗaura tukunyar sannan ta ɗiba kayan ƙamshi da lipton da duk ya fiddo da kansa ta zuba. Flask daya fiddo a kwali shima ta ɗauka ta ɗauraye tare da kofi duk yana tsaye yana kallonta. Baiyi mamakin yanda take komai a tsaftace da kuma tsari ba, dan sai dai ya bama wani labarin Mamie badai a bashi ba, yasan kuma hakan duk tarbiyyar data samune daga gareta. Yana kitchen ɗin harta kammala komai, ya sake ɗaukar kofuna uku ya ɗauraye da kansa ya haɗa da wanda ta wanke. Bata tanka masa ba, ta ɗauka flask ɗin kawai ta fita. Shine ya ɗauka sauran kayan ya fito da su, samunta yay tanama Ikram masifa akan ta tashi su wuce gida, ashe da wayarsa ya haɗata shi ya tafi neman magana kitchen..
      “Sai kun karya, tunda tace bakuyi breakfast ba kuka fito”.
    Ranƙwashi takaima Ikram ɗin, amma sai ta kauce tana dariya da faɗin, “Wlhy Yaya ita a barci ma aka tasota gara ni nasha tea”. Wani ranƙwashin zata sake kaimata ya zuba mata hararar data sata dakatawa, sai dai tayi gefe da kanta tana ƙunƙuni.
       “Oya zauna ki haɗamin yunwa nakeji”. Ya faɗa yana ajiye ledar dake ɗauke da kayan tea da abokansa suka rako shi da su a daren jiya tare da kaza. Batai magana ba, shima kuma bai sake maganar ba ya nufi ƙofar fita yasa key sannan ya wuce kitchen. Harara ta dinga zubama Ikram tana haɗa tea ɗin, tsabar mugunta ta zabga masa sugar. Ikram ta mikama nata tana faɗin, “Makwaɗaiciya kawai, daga zuwa gidan mutane”.
     Ikram tace, “Ni banyi kwaɗayiba tunda gidan Yaya ne”. Fitowarsa ta hanata bama Ikram ɗin amsa, ya dire babban plate dake ɗauke da kaza sai turiri take alamar ɗumamata yay. Zata miƙe yace, “Koma ki zauna.” babu wasa a lamarinsa dole tabi umarni, sai dai idonta harya fara tara ƙwallar takaici. Hanyar corridor ɗin da take ƙyautata zaton bedrooms ne ya nufa, cikin jin haushin da babu dalili ta raka bayansa da harara. Wayarta ta ɗauka ta cigaba da daƙila, kusan mintuna uku sai gashi ya fito, zama yay a ƙasan carpet ɗin shima kamar yanda take zaune. Yace, “Bani tea”.
    Batai magana ba, ta ɗauka flask ta zuba masa ruwan zafin akan kayan tea ɗin data haɗa a kofin. Sai da ta juya ta tabbatar sugar ɗin ya haɗe sannan ta miƙa masa. Duk da yaga bata haɗa nata ba sai baice komai ba yaja nasan gabansa da ƙyau, kaɗan ya ɗiba a cokali yakai baki dan yaji yaya test ɗin. “Ya ALLAH!”. Ya ambata da sauri. Tasan tsiyar da tai dan haka taƙi ɗagowa. “Kina hankalinki ƙuwa zaki saka min wannan sugarn?”.
     “Toni Yaya nasan yanda kake so ne?”.
   Idanu ya zuba mata kawai tsahon wasu sakanni. “Idan ma mugunta ce harda kanki zaki mawa, ba wadda take cikin gidan kawai ba, dan duk dodo ɗaya zaku yima tsafi”. Komai bata fahimta a zancensa ba. Wani kofin ya ɗauka ya raba shayin biyu, ya ƙara kayan tea ɗin banda sugar ya sake zuba ruwan zafi. Ikram dake ta faman latsa waya tana shan nata tea ɗin yace ta sakko.
     Duk yanda Anam ta so nuna ta ƙoshi bai saurareta ba. Haka ya tilasta mata karyawa tare da shi da breakfast ɗin da suka kawo da kazar daya ɗumama. Sai dai ita taƙi cin kazar ko sau ɗaya. Ikram kam komai sai da taji yakai mata sannan tai hamdala. Tayi niyyar suna gamawa su wuce, amma sai taga babu dacewar barin kwanikan, ita ta kwashe komai zuwa kitchen, ta ɗauraye kwanikan da suka ɓata. Koda ta fito bata samesa a falon ba, tacema Ikram ta tashi su wuce gida.
       “Lah aunty Anam Yaya yace mu jirashi zai fito muje tare”.
     Harara ta zuba mata, “Shi kuma driver daya kawomu fa yake zaman jiranmu?”.
      Fitowarsa ta hana Ikram bada amsa. babu abinda ya canja a jikinsa sai key ɗin mota daya ɗakko, ta ɗauke kanta gefe harya ƙaraso ya amsa wayarsa a hanun Ikram. Suna gaba tana binsu a baya har wajen mota, bataga driver ba, ba kuma ta tambaya ba. Ganin Ikram ta shige baya itama tai yunƙurin shiga….
        “Waye driver ɗinku?”.
   Fuska ta tsuke tana hararar Ikram kamar itace tai maganar. “Malama koma gaba”.
     “Ni dai aunty ki barni anan nafi son baya cikina ya cika da yawa zan kwanta”. A fusace ta ƙara yunƙirin yin magana ya dakatar da ita. “Bana son shirme fa kina ɓatamin lokaci nabar matata tana barci kowane lokaci zata iya tashi, ganina kusa da itane kuma abinda tafi buƙata a yanzun”.
      Tamkar saukar aradu haka furucinsa ya daki ƙirjin Anam saboda da yaren malay yay maganar yanda zata jisa ta fahimta da ƙyau. Idanunta ta rumtse ta buɗe motar ta shiga batare datace masa komai ba. Shima bai sake cewarba ya harbar motar zuwa waje dan maigadi dama ya wangale masa gate tuni……..✍

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button