BABU SO 21
21
……Sosai Anam taji kamar ta fashe da kuka. Sai dai bata iya jayayya ba. Dan haka tabi umarnin Mom bayan tayi wanka taci abinta ta haɗa kayan da basu wuci kala bakwai ba, sai abinda ba’a rasa ba. Dan tanajin da wahala zamanta yay nisa a gidan basu kwashi ƴan kallo da Fadwa ba. Aysha ce ta shogo, ganin ƴan kayan data haɗa tace bata isaba. Canja jakkan kayan tai zuwa babban akwatinta, ta dinga ɗibo kaya a wadrobe tana zubawa, duk da dakatar da ita da Anam keyi taƙi saurarenta, dan harda kayan da aka ɗinka mata da ko sakasu ta kasa farayi har yanzun. Aysha da taƙi saurarenta taja a kwatin tana faɗin, “Yaya har yazo, kiyi maza ki kammala kin san sa da azalzala”.
Harara ta wulla mata batare data amsaba. Aysha ta fice tana dariya. Dole itama ta miƙe ta karasa kimtsa abinda ya rage mata. Sannan ta fito yima Mom sallama.
A can ɓangaren Mommy sai yanzu tasan harda Anam za’a zauna gidan Shareff. Ranta ya ɓaci, dan haka kai tsaye tace bata aminceba in har itace ta haifi Shareff. Shi dai baice komai ba, sai Daddy ne yace bata isaba, idan kuma tai wasa zai matuƙar ɓata mata rai ne. Ganin sunata cacar baki Aysha taje ta sanarma Gwaggo duk da tasan itama ɗin dai sai a hankali ce. Dandanan ko sai gata tazo, da yake Aysha ta faɗa mata abinda ke faruwa koda tazo sai ta goyi bayan Daddy akan tabar Shareff ɗin ya wuce dasu Aysha dare nayi, ai zaman Anam ɗin acan ba komai bane. Rai ɓace kuma cikin mamaki Mommy take duban Gwaggo. Gwaggo ta kyafta mata ido alamar kartaji komai ta sallama. Shiru tayi kawai amma har sannan ranta na mata suya, sai dai tama ƙagara su tafin taji dalilin Gwaggon nayin haka.
“Kai tashi ka ɗaukesu ku wuce dare nayi”. Daddy ya faɗa yana duban Yaya Shareff da kamar bashi a falon. Mikewa yay kuwa yay musu sallama. Aysha tabi bayansa suka fice. Bai shiga kowane sashe ba, dan zai dawo da safe musu sallama kafin ya fice tunda bada sassafe zai wuce ba Khaleel ne ma zai kaishi airport. Suma su Ayshan dan yana son suje tun a yau ne ya haɗasu da Fadwa yay musu gargaɗi tunda yasan da gaske za’a dinga samun saɓani ne tsakanin Anam da Fadwa. Aysha ce ta shiga ta kirawota.
Doguwar riga ce jikinta mara nauyi, sai ƙaramin veil data yana a kanta. Tana riƙe da ƙaramar jakar data haɗa kayanta na ciki da Aysha bata kwaso ba saboda sauri. Ta gaida sa batare data kallesa ba. Ɗauke kansa yay yana amsa mata, tare da buɗe motar ya shiga. Aysha tai wuff ta shige baya, zata shiga itama ya hararesu. “Dalla malamai ni drivern ku ne?!”.
Aysha ta tura Anam dake ƙoƙarin shigowa. “Blood kefa na barma can ki shiga”. Baki ta buɗe zatai magana ya juyo a fusace. “Bana son shashanci fa, kuna ɓatamin lokaci”. Hararar Aysha dake mata gwalo tayi, batare da tace komai ba ta zagaya ta shiga gaban ta zauna. Motar yayma key ya fice bayan sunyi sallama da maigadi.
A hankali yake driving ɗin kamar baya so, motar shiru babu mai ko motsin kirki. Dan ita Anam ma har ta fara gyangyaɗi kasancewarta mai barcin wuri musamman idan waje da sanyi. Yanzu kam sanyin acn ke ɗibarta dama ga gajiyar aiki. Karatun alkur’ani ya kunna har suka iso, gidan shiru kamar babu kowa, sai maigadi dake sauraren taskar labarai a redio. Yayma uban gidansa sannu da zuwa bayan ya buɗe masa gate.
Shi da kansa ya fiddo musu akwatinsansu a booth, Aysha taja ɗaya tana turama Anam ɗaya. Hamma tayi cikin ɗan layin barci ta jingina da motar tana dafe akwatin. Ita da akwatin yayma kallo ɗaya ya ɗauke kai, batare da yace komai ba ya sama motar lock da key ya ja akwatin yay gaba. Baki taɗan tunzura sannan tabi bayansu cikin ɗan layin barcinta.
Basu sami kowa a falon ba, hatta da tv a kashe take, Aysha ta kallesa cikin zumuɗi tana faɗin, “Yaya Aunty Fadwa fa?”.
Gitta ta yay kamar bazai amsa ba, sai da ya kai akwatin ƙofar ɗakin da zasu zauna ya juyo. “Maybe ta kwanta, na barta kanta na ciwo”.
“Ayya ALLAH ya bata lafiya”.
Amin ya faɗa kan laɓɓa idanunsa akan Anam data zauna a hannun kujera ta kwantar da kanta dan da gaske barcin takeji. “Ki tadata kuje ku kwanta kuma kawai”.
“Okay Yaya sai da safe”.
Kasancewar tayi wankanta tayi salla tun a gida suna shiga ɗakin ta faɗa kan gado tai kwanciyarta, addu’a ma sai Aysha ce ta mata tana mintsininta cikin tsokana da kiranta kasa anji sanyin ac. Hannunta ta buge, ta juya taci gaba da barcinta.
__★
“Gwaggo nifa wlhy duk kin sani a duhu. Ko kin mance wai yarinyar nan ce dana tsana ita da iyayenta fiye da komai a rayuwata”.
Murmushi Gwaggo tai irin na makircinsu na tsoffin hannu. Ta dafa kafaɗar Mommy. “Daɗina dake gaggawa. Kema kin san bazan amince da zamanta can ba in babu wani abu a ƙasa. Dan haka kwantar min da hankalinki da safe zakiji komai…”
“Miyasa ba yanzuba Gwaggo?”.
“Saboda idon mijinki yanzu akanmmu yake.” Kai kawai ta jinjina badan taji sauƙi a ranta ba. Gwaggo tai mata sai da safe ta fice tana murmushin da sam Mommy ta kasa fassarashi a kowane mizani….
WASHE GARI
Shine ya musu knocking ƙofa da zai wuce massallaci da asuba, sai da ya tabbatar sun tashi sannan ya fice. Ana idarwa gida ya dawo, azkar ma sai da ya zo yayita a gida bayan ya sake tada Fadwa dake barci duk da ya tadata kafin ya fita amma bayan fitarsa ta koma ta kwanta. Tana mitar ita har yanzu kanta ke ciwo ta nufi bayi tayo alwala. Bai tanka mata ba harta zo ta kabbara salla. Bayan ta idar ta tashi ta koma gadon, a jikinsa ta lafe tare da sumbatar laɓɓansa. “Good Morning my Soulmate”.
“Good morning wife ykk ya baby?”.
Murmushi tai da kamo hanunsa ta ɗaura kan cikinta, murya cike da shagwaɓa tace, “Gashi har ya fara kewar Daddynsa”. Murmushi ya saki a karon farko, ya sumbaci laɓɓanta shima. Cikin ɗage mata gira ɗaya yace, “Nima cike nake da kewarsa shi da mamansa. Amma karya damu bazan jima ba zan dawo garesa insha ALLAH”. Rungumesa tai sosai, tare da fara bashi wasu zafafan salon da ya sashi biye mata. Bayan komai ya lafa tana kwance a jikinsa idanunsa a lumshe ya kirayi sunanta.
“Uhhyim”.
Ta amsa tana ƙara ƙanƙamesa. Cigaba yay da shafa kanta har yanzu idanunsa a rufe. “Jiya nazo da su Aysha da zasu tayaki zama. Koda wasa bana son jin wata fitina. Ki riƙe girmanki da mutuncinki. Idan naji wata fitina kezan fara hukuntawa matsayinki na babba”.
“Insha ALLAH babu abinda zai faru, Ayshan ita da Hussaina ne?”.
Kansa tsaye yace, “Da Anam”.
Baima gama rufe baki ba ta miƙe zumbur zaune. Shima sai ya buɗe idanu yana kallonta. Kai take girgiza masa hawaye na ciko mata ido… “Ni gaskiya bazata zaunamin gidaba, taje kawai Aysha ta isa”. Idanunsa ya kauda yana tashi zaune ya jingina da fuskar gadon. “Karki ɓatama kanki rai a banza. Juwairiyya da Aysha zasu zauna tare dake, shima Khaleel anan zai dinga kwana….”
“Bazai yuwu ba”.
“Sai ki hanasa yuwuwar mu gani tunda gidanki ne”. Ya faɗa a fusace yana sauka a gadon. Da sauri ta yayibi bedsheet ta sakko tana ƙudindine jikinta a ciki tasha gabansa. “Dan ALLAH ka tsaya muyi magana. Wlhy iya gaskiyata nake gayama na tsani yarinyar nan bazan iya zama inuwa ɗaya da ita ba har abadan dan zan iya halaka ta”. Sosai yake kallonta cikin tsakkiyar ido. Ya riƙe ƙugu da dukkan hannayensa yana ƙoƙarin danne fushinsa. “Zaki iya halaka ta? To sai dai in ki halakata ɗin, dan babu fashi zata zauna anan tunda ba dake na haɗa kuɗin na gina gidana ba. Ki bari mu rabu lafiya Fadwa!!..” Ya ƙare maganar cikin tsananin zafin rai ya ɗan banjajeta ya ficewarsa.
Zubewa tai a wajen ta fashe da kuka. Itakam ta shiga uku wannan shegiyar yarinya ta zamewa rayuwarta jaraba. Wayarta ta ɗauka tai kiran Mahmah, sai dai kuma a kashe, Mommy ta kira, bugu ɗaya ta ɗauka. Ko sallama babu balle gaisuwa ta fashe mata da kuka tana faɗa mata ita dai inhar da Anam zata zauna to sai dai ta koma gidan su. Sai da ta gama surutanta sannan Mommy tai magana..
“Fadwa na fiki shiga ɓacin rai da zaman wannan yarinyar anan gidan, dan a daren jiya banyi barcin kirki ba saboda baƙin ciki. Amma ina son ki kwantar da hankalinki Gwaggo tace tanada plan akan zaman nata….”
“Mommy Shi plan ɗin baza’a iya aiwatar da shi tana nan ba dole sai ta raɓu da gidana?”.
“Nima na faɗa miki ba son hakan nake ba. Amma mu saurari mi Gwaggon zatace zuwa anjima. Yanzu dai ki daure ranki ku rabu lafiya da mijinki bayan ya tafi anjima kaɗan zan zo gidan ai”.
“Mommy….!”
“Kiyi yanda nace”.
Mommy ta tari numfashinta a fusace tana yanke wayar, dan ƙara hasalata Fadwan take ma……….✍