BA DON SHIBA HAUSA NOVEL

BA DON SHIBA 21-25

Page 2⃣1⃣
to 2⃣5⃣

Sai daya ga ta shige gidan maman salaha sannan ya juyo ya fara tafiya yana saka irin rashin mutuncin da zaiwa haladu da uwarsa,,a bakin layin ya hadu dasu auwal ni kaina sai dana tsorata????ganin irin mutanen dake tare dashi,gaba dayansu ba alamun murmushi a fuskar su jira kawai suke ace kule suce cass…duna ne ya fara magana yana ciccezewa..yadai baba wai aina za ayi operation din ne kasanfa kwana2 ban fede ba,,murmushin mugunta ammar yayi kafin yace ku biyoni muje..duuu kuwa suka bi bayanshi kusan su 15 ne amma duk shine a gaba kowane da makami kuma a hannun sa tun daga nesa da an hango su zaa fara gudu..dan mutane sunsan ba alheri bane ke tafe dasu ba,,wasu daga cikin mutanen kuwa har sun tausayama wanda zasu je gurin shi..domin kuwa ba yau aka saba ganin haka ba sai dai kowa yayi gumm ba bakin magana,,

jidda zaune a acikin dakin maman salaha amma hankalinta gaba daya baya jikinta tana tsoron abinda ammar zaije yayi…da karfi maman salaha ta kira sunanta sannan ta dago a firgece,,ke kuwa jiddah me yayi zafi haka,,cikin kuka ta labarta mata halin da ake ciki,,allah na gode maka maman salaha ta fada tare da kwashewa da dariya..tabbas ammar ya cika dan halak kuma yamin daidai,,da sauri jidda tace amma fa kada su mai wani abu daga baya,,hmm tace kafin ta fara magana jiddah kenan kinsan uban ammar nada kudi ba abinda zasu iya yimai,,sai da ta kwantar mata da hankali kafin taje taci gaba da aykinta

zirga zirga kawai suke a cikin gidan daga ita sai haladu domin su rabi tuni suka fice yawon su amma fa indo ta kullaci jiddah a ranta tun dazu ta aiketa amma bata dawo ba..da tunanin rashin mutuncin da zata mata inta dawo ta fita aranta,,,,,kofar gidan sukaji ana bugawa..da karfi kamar zaa cire inna dake tace kamu ta duro ashar kafin tace wani matsiyacin ne zai ballamin kofa shegu yan bakin cikin unguwa zasuja min asara,,shiko haladu da fitowar sa kenan daga bandakin ya fara zubo nashi ruwan ashariyar dan kuwa karan buga kofar ne yasa shi fitowa ba shiri,,,daga can waje kuwa ammar ne da gang dinsa tsaye mamakin zagin da tsohuwar da danta ne sukeyi ya kamasu duk da shi ammar yasan zasu iya fiye da haka,,,cikin fushi yama kofar zuwa daya sai gata a gefe.shiyya fara shiga cikin gidan sannan sauran suka biyo bayanshi..mute bakin inna asabe yayi ganin ammar da yan jagaliyanshi sai da kirjinta ya buga domin kuwa bata manta warning din daya mata kwanaki ba…shiko haladu me danyen kai zaburowa yayi wai zai naushi ammar zuwa daya ya kamashi hannun ya murda.ihun azaba haladu yasa naushin bakinsa yayi tare da jefar dashi a kasa gwajab kamar kayan wanki,,cikin daga murya ammar yace dasu operation start…aiko basu yi wata wata ba suka fara fasa duk wata roba ko bokiti dake tsakar gidan wasu kuma dakuna suka shiga suka fara tarwatsa kayan tsummokaran data tara kai hatta igiyar shanya basu barta ba,,,tukwanen kuwa sai da duk suka taka su duk suka lauye,,nuna musu haladu yayi dake kwance har yanzu yana jinyar hannun sa,,ku kawo min shi nan dakko shi suka yi suka ajeyi a gabanshi baiyi wata wata ba ya kai mai naushi a fuska sai ga jini nabin gefen fuskarsa,,inna asabe na ganin haka tasa ihu tana neman agajin makota,,,jama’a ku kawo mana dauki ku taimako ga jujal nan da mukarraban sa…naushin da duna ya kai matane ya sata rufe baki bata shirya ba ai ko jini ya fara malala mangareta duna yayi ta fadi kafin su rufe su da dukansu bame ceton wani

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button