MADADI 1-END

MADADI Page 31 to 40

Sai bayan ishai ya shigo gidan, a lokacin itama tayi sallah taci abinci tana zaune suna hira da Hajiyan, ba tare da ya zauna ba ya kalli hajiyan da fad’in “To hajiya sai da safe.” Hajiya ta kalli Naja’atu da fad’in “Tashi kuje ki kara hakuri insha Allahu zakici ribar hakurinki.”ta kalli Abba Abbas din da fad’in ” Kai kuma ina fatan kaji abunda na fada maka ko.” Yace.”Naji hajajju Allah ya shige mana gaba.” Ta amsa da ameen.” ya juya ya fita, ita kuma ta mike a sanyaye tasa takalmanta hajiya tace”To Allah ya tsare insha Allah zansa a kawo ni gidan naku.” Tace.” Tom Hajiya sai kinzo.” Kafin ta fita sai da ta shiga dakin hajia Rabi kishiyar Hajiyar tayi mata sallama Hajiya Rabi ta bata kayan islamic irin na mata masu kyau. ta kar’ba tana godiya tayi mata sallama tabi bayansa.Tare ta gansu da Abba Magaji a jikin mota suna magana, gabanta ya fadi ganin Abba magaji duk sai ta tsorata kai a sunkuye tana kokarin bude mota tace”Abba Magaji ina wuni.” Ya amsa fuskarsa a sake, dan shi gabadaya bai san wai yaji tayi ba tunda shi Abbah Abbas din bai fada masa komai ba….Bude mota tayi ta shiga tana zazzare ido addua take Allah yasa Abbah Abbas din ya shigo su tafi dan gabadaya jikinta yayi sanyi tasan da Abba magajin yasan abinda ta aikata sai ya ‘bata mata rai.

Motsin bude motarsa taji sai ta nutsu tayi kasa da kanta gabanta na fad’uwa. Ya shiga motar ya zauna ba tare da kalleta ba a nutse yaja motar suka bar gurin…….gabadaya hankalinsa nakan draving din da yake bai ko kalli inda take zaune ba. ita kuma ganin yanda ya sha kunu ne yasa duk tsoro ya cika mata zuciya. kire ne ya shigo Wayarsa dake gaban aljihunsa, ya dauka yana dubawa yaga Halisa ce, ya kara wayar a kannunsa tare da amsa sallamarta, tace”Abbah Mufida yau shuru baka shigo gida da wuri ba nace Allah yasa dai lafiya sannan kuma ina so na fada maka cewar yarinyar nan Naja’atu tun safe bata gidan nan.” 

Yace.”Kada ki damu gani nan tare da ita taje gidan Alhaji ne.” Halisa tace”Au! to ai da da zata tafi sai ta fad’a mana nida yara duk hankalinmu ya tashi wallahi.”

Yace.”Nima bata fad’a min saboda tana da iko da kanta na dawo daga kasuwa na sameta a can.” Halisa tace”Ikon Allah.” Yace.”Ganinan shigowa yanzu.” Cikin kissa tace”Allah ya kawo ka lafiya.” Kashe wayarsa yayi a mayar aljihu ya cigaba da draving dinsa …..Naja’atu taji ciwon yanda ya banzatar da ita tana ganin ai kamata yayi ya rarrasheta tunda ita akayiwa laifi amma saboda bata da wata daraja a gurinsa laifinta ma yake gani….Itama sai ta dinga kauda kanta tana kallon hanya, tana kuma kokarin mayar da hawayen dake so ya zubo mata.

Dai dai asibitin Hasiya bayaro yayi parking ya fito ya tsallaka titi naga ya nufi wani ke’bantaccen gurin gasa kaji da sauransu ya jima a ciki kafin ya fito hannunsa rike da ledoji masu dauke da sunan gurin, tana ganin zuwansa ta juyar da kanta ya bude motar ya shiga ya zaune, ‘kin juyowa tayi har ya tayar da motar suka bar gurin fuskarta na kallon hanya sai zumbura baki takeyi, a haka sukaje gidan babu wanda ya kula dan uwansa.

Yana parking ta bude motar tayi gaba, ya girgiza kansa tare da fitowa daga motar yabi bayanta da ledojin a hannunsa.

Halisa da yaran suna zaune a palo suna kallo kamar dai koda yaushe yaran suka iske inda yake suna masa sannu da zuwa, mussadiq ya kar’bi ledojin hannunsa yana kokarin kai masa daki, yace.”Bani guda d’aya sauran naku ne kowa ya dauki daya.” Mussadiq yace.”Mungode Abbah.” Mussadiq Ya mikawa kowa nasa, Halisa kuwa mi’kewa tabi bayansa dakin.

Naja’atu kuwa dama data shigo gidan babu wanda ta kula kai tsaye daki ta nufa..tana jin wani irin kunci na dawowarta gidan a duniya ta tsani ta budi ido ta ganta a gidan ji take tamkar tana kurkuku! Mussadiq ya shiga dakin da ledarta a hannunsa a sanyaye yace.”Yaya Naja’atu ga naki.” Girgixa kai tayi tace”Jeka hada ka cinye naci abinci gidan hajiya.” Yace.”Yaya Naja’atu gidan Hajiya kikaje me yasa bakije dani ba.”? Murya na rawa tace”Ka bari idan zan sake zuwa zai je da kai.” Yace.”To nagode amma dan Allah ki kar’ba kici ni ba zan iya cinyewa duka ba.” Tace.”To ka ajiye gobe sai ka tafi dashi skull.” Yace.” Uhum!uhm ni dai nafi so kici hankalina zaifi kwanciya.” Kar’bar ledar tayi ta bude tana dubawa, taga gashashiyar kaza da sauran kayan ciye ciye….Tace”To zauna muci tare.” Yace.”To bari na dauko nawa.” Da sauri ya fita daga dakin.

Halisa kuwa cikin kissa da kisisina ta dinga bugun cikin Abbah Abbas din, saboda tana so tasan dalilin da yasa yarinyar tafiya gidan Hajiya, shi kuwa ba tare da tunanin komai ba ya fada mata dalili…..Ta ri’ke bakinta tana jimantawa tace”Amma gaskiya yarinyar nan bata kyauta ba, yanzu kamarka zata kai ‘kara gurin hajiya! hummm! gaskiya ta bani mamaki kuma a yanda kake kauntarta da nuna kulawarka a kanta bai kamata tayi maka hakaba, kuma wallahi karya take Yaya Ramlatu bata doketa ba sharri kawai tayi mata! dan haka kada ma kace zaka tunkari Yaya Ramlatu da wannan maganar idan haka ta kasance Yaya Ramlatu zataga kamar kafi kaunar matarka a kanta kuma kasan karfin zumunci yafi gaban a hadashi da komai. ni a ganina yarinyar zaka hukunta ba wai ita Yaya Ramlatun ba.”

Yace.”Koma dai menene insha Allahu ya kusa zuwa karshe, sannan bana daukar wasu abubuwan da yarinyar nan take da zafi dan saboda nasan akwai karanci shekaru a tare da ita gaba kadan idan ta kara hankali ba zatayi ba…..Ta’be baki tayi tace”Babu wani kuruciya tsabar iskanci ne wallahi.’ Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta da fad’in “ki duba cikin rigar dana cire ki dauki key din motarki.” Halisa ta ru’kun’kume shi tana dariya.” Shima dariyar yake yana mamakin murnar da take, Halisa ta dauko key din tana ta washe bakinta, mikewa yayi yace.”Gobe zan kaiki ki d’auko motar a inda na siya miki.” Tace”To nagode sosai Allah ya saka da alkairi.” tare suka fito daga dakin, ya zauna a gurin cin abinci Halisa ta had’a masa abincin data girka wanda ta barbade shi da maganin mallaka, shi kuwa kamar koda yaushe yayi bisimillh sannan ya soma cin abincin ba tare da ya kawo komai a cikin ranshi ba.

 Naja’atu kuwa bayan sun gama cin abinci da Mussadiq wanka tayi tasa doguwar riga mai botira ta gyara gashinta hula tasa sannan ta dauki hijabinta tasa ta nemi guri ta kwanta, abinda duniya ya isheta, ‘yar wayar dake d’ebe mata kewa babu, ita kuma ba zata fita palo ta zauna a cikinsu ba tasan a irin wannan lokacin yana zama a palon tare da yaransa, fuskarsa ma bata son gani gabadaya wata irin tsanarsa takeji a cikin zuciyarta…..Bacci ne ya soma fizgarta taji shugowar yaran zasu kwanta zaune ta mike tana kallon Mussadiq yana kokarin daukar pillow tace”Zo ka kwanta a gadonka.” Sauka take kokarin yi. Yaron ya ajiye pillow a kasan kafet kamar yanda yayi jiya yace.”A’a Yaya Naja’atu ki kwanta ke.”

Tana kokarin yin magana Mufida ta shigo tace”Yaya Naja’atu wai kije inji Abbanmu.” Taji wani fad’uwar gaba ya rikota mata, tace”Yana ina.”? Yarinyar na kokarin sa kayan baccinta tace”Yana palon.” Ajiyar zuciya ta sauke taji dadi ai ta dauka yana dakinsa ne shiyasa gabanta faduwa.

Kai tsaye palon ta nufa….Loptop ta sameshi yana dubawa Ta dan tsaye daga nesa da fad’in “Abbah gani.” Ba tare da ya kalleta ba yace.”Zo ki zauna muyi magana.” Jim! tayi kafin taje ta zauna!

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button