BABU SO HAUSA NOVELNOVELS

BABU SO 3

Typing????

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

03

……….Tuni sun tattare kansu a sashen aunty amarya idan ka cire ƴan manya-manyan yaran gidan samari da basu gama dawowa da ga wajen aiki ba da kuma masu shiga school lectures ɗin yamma. Zagaye suke da Anam suna kwasar dariyar hausarta da bata nuna da ƙyau ba. Dan cike take gwamutse da yaren malay da turanci, wai a hakanma Abie na matuƙar ƙoƙarin mata hausar ne shi da aunty Mimi dan Mamie ma ba wani iyawa tai sosai ba harma gara Anam ɗin, tunda dama acan itama ta tashi, ko Nigeria tazo tafi yin turanci da jama’ar gidan. Aysha dake naniƙe da Anam ɗin da suke sa’annin juna dan dama idan tazo bata da ƙawar data wuceta a Nigeria, cike da kulawa take tambayarta dalilin matsar ciki da take famanyi.
       A yatsine Anam ta sanar mata tana jin yunwa ne, dan ta kasa cin duk abincin da aka shirya musu a gidan. Dama can idan sunzo Mamie ce ke musu girki shiyyasa Anam bata da matsala tunda abinda ta saba ci ne, a yanzu ko babu Mamie dole sai abincin Nigeria da har yanzu ta kasa iya ci, ƴan abubuwan da take iya cin ƙalilanne kuma babu su.
      Idanu Aysha ta ɗan waro, cikin harshen turanci take cemata miyasa zata zauna da yunwa bayan abinci da akai domin su tunda sun iske tarin kwanika a sashen Daddy lokacin da sukaje gaida Abie. Sunada tabbacin kuma an shiryasune dan zuwan su Anam ɗin. Fuska a marairaice ta sanarma Ayshan ita bata iyacin duk abincin ba ai. Ba Aysha kaɗaiba duk yaran sai da suka dara, dan sosai ragwantakar Anam ke basu dariya, kodan tana ganinta da ƙaramin jiki ƴar ficika da ita yasa a kullum bata sanin ta girma? Sosai Aysha ta fita girman jiki, sai ma ta saɓeta ta goya dan ita ta kwaso tsayi da garin jikin Mommy mahaifiyarsu.
    Sake ɓata fuska Anam tai kamarzatai kuka, sai faman matse ciki take da cizar lips dan da gaske yunwar takeji, shi kansa Abie yana canne amma hankalinsa na kanta dan yasan bazata iyacin kowanne abinciba da ya gani an tara masa.
      “Am so sorry sweetheart. Kar kiyi kuka faɗi abinda kike so sai a samo miki, ko a kira Yaya ya sayo miki tunda shi yasan inda yake samo abincin naku, dan shima dai ya jima yana wahala kafin ya saba da abincin Nigeria, ko yanzu ma ba komai yake iya ci ba”.
      Fahintar wa Aysha ke nufin za’ama magana ya samo mata abinci ya sakata girgiza kanta, a langwaɓe ta kamo hanun Ayshan cikin nata. “No don’t worry rakani wajen Abie na nidai kawai”.
    Batama bari Aysha tace wani abuba ta miƙe har lokacin hanunsu cikin na juna, ɗayan hanunta kuma nakan cikinta. Wando da rigane a jikinta marasa nauyi, wandon irin mai faɗin nan sosai da ƴan Nigeria ke kira a fantama????, sai fingilar top da tabi jikinta ɗas kamar dan ita aka halicceta, sai siririn veil data sakaya gashinta a ciki sai dai hakan bai hanashi bayyana ta gaba ba saboda veil ɗin daya zama baya.

       Itace ta farayin sallama a hankali cikin sassanyar muryarta, ta dora da faɗin, “Daddy mu shigo?”.
     Murmushi Daddy da Abbah keyi idonsu akan ƙofar. Abba ne ya amsa da “Shigo mana Mamanmu”. Hanun Aysha taja zuwa ciki, sai dai taku uku kacal tai ta tsaya turus fararen idanunta da sukai laushi saboda yunwa tsaye ƙyam akan wanda ke zaune bisa lallausan carpet ɗin falon gab da ƙafafun Abie ɗinta, yayinda hankalin Abie kacokan ke akansa da alama ma bai san da shigowarta ba.
     Sosai ƙirjinta ya harba dan ko kusa batai zaton ganinsa anan ɗin ba, tunma data duro gidan addu’arta shine karma su haɗu kwata-kwata. Zancen Aysha na ɗazun ya tabbatar mata yana ƙasar, hakan kuma na nufin dole su haɗu koda ba yau ba. Amma batai tsammanin yanzu ba. Kamar yanda tai masa kallo ɗaya ta ɓata fuska da gyara yanayinta haka shima yay mata kallo guda duk murmushin fuskarsa ya ɓace, har wani yamutse fuska yay tamkar yaci karo da tutun safiya na cikin sanyi……
      “Mamanmu ƙaraso mana”.
Daddy ya katsesu a tare dan duk yaga irin kallon tsanar da sukaima juna. Shikam ya rasa wannan ƙiyayya ta Anam da Shareff bayan kowa yasan irin dunbin son daya nuna mata tana jinjira har zuwa sanda ya wuce Indonesia, amma a yanzu baka ganin komai sai ƙin juna a tsakaninsu tamkar basu taɓa sanin juna ba. Yitai kamar bata gansa ba taje ta zauna kusa da ƙafafun Daddy, cikin marairaice fuska tace, “Daddy ina jin yunwa sosai”.
       “Ya salam mamana garin yaya haka? duk abincin dake gidan nan ga wasuma ko taɓawa ba’ai ba kuma dan k kawai aka shirya su”.
      Kanta ta girgiza kamar zatai kuka. “Daddy bana son su ban iya ci ba ai”.
          “Sai ki fara koya yanzu ai”.
Abie ya faɗa kafinma su Abba suce wani abu yana hararar Anam duk da kuwa bai kai zuci ba, dan ransa cike yake da damuwar zamanta da yunwar tunda yasan da gasken ba iya cin tai ba.
     Daddy yace, “A’a ba’ayi hakaba ai. Tunda tace bata iyaba da gaske bata iya ɗinba kuma bataso. A bita a sannu zata koya ci insha ALLAH tunda tana nan. Shareff ka ɗauketa kuje a sama mata abinci dan kaine kafi kowa sanin inda kake ciyo abinda ta iya ci”.
       Tamkar saukar aradu haka Shareff yaji saukar zancen Daddy a kansa. Ya ɗago da sauri yana duban mahaifin nasa tamkar a razane. Harara Daddy ya zuba masa. “Lafiya ka tsareni da idanu halan?”.
       Ƙasa ya risinar da idanunsa batare da yace komai ba. Sai dai fuskar ta sake rinewa tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa.
          “Daddy ni dai nama ƙoshi kawai zansha ko tea to”. Anam da itama ta haɗe fuska tana hararsa ƙasa-ƙasa ta faɗa baki a tunzure”.
      Maimakon Daddy ya amsa mata sai ya kira sunansa a tsawace. “Shareff Are you daft?”. Kansa ya girgiza kawai yana miƙewa, idonsa a ƙasa yace, “Zanje na sayo kawai…..”
      “Da ita zakaje ta zaɓa abinda take so”.
     Dady yay saurin faɗa cikin katse masa hanzari. Wani irin rumtse ido yay da ƙarfi da cije lip ɗinsa na ƙasa uwa zai huda shi. Sai dai baice komai ba ya kama hanyar fita. “Basai kaje ɗakko key ɗin mota ba zo ka dauka wannan”. Abbah ya katsesa dan ya tabbatar Mommy ta gansa zata hana itama. Nanma baice komai ba ya dawo ya amshi key ɗin hanun Abban.
       “Maza bishi mamana kuje, ki kuma zaɓo duk abinda kike so kinji”.
    Kanta ta ɗagama Daddy tana murmushi, dan ganin yanda Shareff ɗin keyi yasata jin zama ta bisa kodan ta baƙanta ransa…
        Kasancewar ya fita zafin nama sanda ta iso harabar gidan harya tada motar yana reverse, maimakon ya faka saitin inda take ya ɗauketa sai ya harba motar har bakin gate. Anam tai ƙwafa da taɓe baki, cikin kunƙuni da gurɓatacciyar hausarta tace, “Duk baƙin halin da kake sai naje saika mace idan kasha zuciyanka mugu mai baƙin rai”.
       Oho baima san tanai ba. Cike da wani takun isa tazo ta buɗe murfin ta shiga kanta a gefe. Bawani duban kirki yay mataba a ciki, dan haka bai gama tantance kayan jikinta ba. Tana shiga ya fisga motar da ƙarfi har yanayi kamar zai taka mai-gadi ma, sai da yay tsalle gefe ya bashi hanya cike da mamakin mike damunsa. Dan shi shaidane Shareff mutum ne daya san mutuncin mutane, ko yaya kake a ƙasansa bai yarda ya ƙasƙantaka ba balle wulaƙantaka. Yayi imani da ALLAH ransa a ɓace yake bada son rai yay masa haka ba.
           
      ★ Sosai gidan abincin ya haɗu, ya samu waje yay parking batare da yace da ita komai ba ya fice a motar. Baki taɗan taɓe kaɗan da yima ƙeyyarsa gwalo, sai kuma ta zabura ta buɗe motar tamkar wadda ta tuna wani abu. Yana gab da shiga ta cimmasa saboda da ɗan gudu-gudu take tafiya. Cak ya tsaya, dan haka itama ta tsaya kanta a ƙasa dan duk fitsararta a bayan idone kawai dama.
       “Idan kika bari ƙafarki ta shiga wajen nan sai na ɓallata”. Da yaren malay yay maganar, dan haka komai ya shiga kunnenta tsaf. Baki ta tura fuska a kumbure idonta na tara ƙwalla harya shige tana kallon bayansa ta ƙasan ido. Maimakon ta koma mota sai ta nema waje a gefe tai tsaye tana kallon mutanen dake. a ciki ta cikin glass da aka ƙawata wajen…..
       “Hallo….”
  Aka faɗa a bayanta cikin wani irin sallon daya tilastata ɗago idanunta masu haske, matashin saurayine ƙyaƙyƙyawa fari tas. Sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar karɓarsa ga wani ƙamshi na musamman a tare da shi. A hankali ta janye idanun nata ganin yanda ya tsareta da idanunsa birkitattu. Gefen data maida fuskar ya sake dawowa yana gyaran murya, ta sake ɗauke kanta gefe….
      “Dan ALLAH ki kulani ƙyaƙyƙyawa ”. Ya faɗa cikin marairaicewa da haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo. Baki taɗan taɓe gefe tana yamutsa fuska da kai hannu ta gyara glass ɗin idonta dake ƙara fiddo ƙyawunta duk da tana sakawane badan gayu ba, kamar bazatace komaiba sai kuma dai ta tanka masa saboda ALLAH daya haɗata da shi. “Ka fara koyan sallama tukunna kamar zaifi bature”. Kansa ya dafe, cike da jimami yace, “Am sorry Assalamu alaiki ƙyaƙyƙyawa”. Nan ɗin ma bata amsaba sai da tasha masa ƙamshi tana wani ɗauke kai. “Wa’alaikassalam. kuma ni ba sunana ƙyaƙyƙyawa ba”. “Tabbas sunan shine ya dace dake, sai dai dazanji na yankan zanfi yin farin ciki”. Banza ta masa har kusan minti ɗaya, ganin yana neman matsowa jikinta tai saurin ɗagowa a masife……
       A dai-dai nan Shareff ya fito daga wajen hanunsa ɗaukeda ledoji masu tambarin wajen abincin. Duk da idonsa a kansu ya fara sauka sanda yake buɗe ƙofar sai ya ɗauke tamkar bai gansunba. Sai dai ya sake tsuke fuska. Yazo zai giftasu a fisge yace, “Second ɗaya kika ƙara a wajen nan jikinki sai ya faɗa miki”. Daga ita har saurayin da sauri suka maida dubansu garesa dan ita bama ta lura da shi ba da farko. Ko kaɗan bazaka taɓa cewa shine yay maganar ba. Tuno dukan da sukaci ita da Aysha randa sukaje birthday party ya sata zabura da sauri tabi bayansa bakinta a tunzure tana hararar bayansa, da sauri shima saurayin ya take mata baya. Tana ƙoƙarin rufe murfin motar ya riƙe da hanzari……….✍
      

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button