Labarai

Wani Uba ya fusata yayi sandiyyar cirewa jariri dan wata shida hannu

Hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa (NHRaC) da kungiyar mata ‘yan jarida (NAWOJ) reshen jihar Imo, sun yi kira ga gwamnatin jihar da hukumar ‘yan sanda da su gaggauta cafke tare da hukunta wani magidanci mai suna Mr Conidence Amatobi, bisa zargin lakadawa jaririn sa mai wata biyu a duniya shegen duka.

Mr Amatobi ya bugi jaririn mai suna Miracle da abin makale kaya na roba wanda yayi sanadiyyar karyewar hannun jaririn saboda ya hana shi ya samu barci mai dadi. Jaridar News Direct ta rahoto.

Dukan da aka yiwa jaririn ya sanya sai da aka yanke masa hannu

Lamarin ya sanya sai da aka yanke karyayyen hannun jaririn a babban asibitin tarayya dake a birnin Owerri na jihar.

Da take bayyana yadda lamarin ya auku, mahaifiyar Miracle mai suna Mrs Favour Chike, mai shekara 20 a duniya wacce ta fito daga kauyen Idemili na jihar Anambra, tace ta bar jaririn da mahaifin sa domin zuwa bandaki a ranar Juma’a 7 ga watan Oktoban 2022, lokacin da lamarin ya auku.

Favour ta bayyana cewa ta jiyo karar jaririn yana kuka wanda hakan ya sanya tayi sauri domin sanin dalilin da yasa yake tsala kuka, kawai ta ci karo da hannun jaririn na dama ya kumbura kuma kashin ya karye saboda duka da mahaifin sa yayi masa.

Amatobi, ya amsa cewa jaririn ya hana shi barci da kukan da yake yi wanda hakan ya sanya yayi masa dukan tsiya domin yayi masa shiru

“Bayan ya fahimci cewa ya karya masa hannu, yayi amfani da itace da robali domin daidaita karyayyun kasusuwan,” Inji ta

“Da nayi masa magana kan abinda yayi, sai ya kulle mu a cikin daki domin kada na gayama mutane halin muguntar da ya aikata ko na nemi taimako. Ya kwace wayar hannuna don kada na kira makwabta.”

Ta kuma bayyana cewa bayan ta samu ta fita daga gidan, ta kai jaririn asibitin kauyen amma sai suka ki duba shi kafin daga bisani ta tafi babban asibitin tarayya dake Owerri inda anan ne aka ya ke hannun jaririn.

Mahaifiyar yaron tayi kira da gwamnati ta kawo mata dauki

Mahaifiyar jaririn ta bukaci da a taimaka mata ta ceto rayuwar jaririnta inda tayi kira ga gwamnatin jihar da sauran kungiyoyin kare hakkin dan Adam da su taimaka mata ta samo wa jaririn ta adalci.

Shugabar kungiyar ‘yan jarida mata reshen jihar Imo, Mr Dorathy Nnaji, wacce ta gana da ‘yan jarida bayan ta ziyarci jaririn a asibitin inda aka yanke masa hannu, ta tabbatar da cewa raunin da mahaifin yaron yaji masa shine silar da ta sanya aka yanke masa hannu.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button