BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 32

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

32

………..Itama Aysha a ranar ta dawo gida da dare, shine ma ya kawota tare da Fadwa. Anam najin sanda suka shigo gaida Mamie ta maƙale a ɗaki har suka fita bata leƙo ba. Washe gari Mom tazo da mai gyaran jiki. Ba hajiyan bace zatai mata da kanta, ma’aikatan ta ne, amma saboda Mom tai alƙawarin shigowa kullum ayi a gabanta insha ALLAH. Ita dai Anam bata damu da wannan zancen gyara ba tun amsar da Mom ta bata a waccan ranar, dan haka koda suka korata a falo da zasuyi magana ko’a jikinta tama nufi can cikin gida wajen Aysha dake fushi da ita ta barsu. Da wannan damar su Mamie sukasha hirarsu dan Hajiyar Sudan tasan Mamie ɗin sukan haɗu idan ta shigo Nigeria.
      


       Tun daga wannan ranar aka farama Anam gyaran jikin mai inganci. Yayinda a cikin gida aketa shirin biki gadan-gadan babu wasa. Ita da Shareff dai haɗuwa ta gagara. Da zaran taji ya shigo gidan zata bar falo idan har tana zaune ne ma. To yanzu ma gyaran da ake mata babu dare ba rana yasa bama zaman falon take sosai ba saboda dokar Hajiyar sudan. Randa Maheer ango ne dai ya iso ta kasa haƙuri sai da ta fito cike da farin ciki suka gaisa. Sai dai yanayinsa ya saka mata sanyin jiki dan duk ya ɗan rame gashi babu fara’a tattare da shi.
    Washe garin da Maheer ya dawo biki na saura kwanaki goma sha biyar da daddare Shareff yazo gidan ya samu iyayensa a falon Daddy. Sune sukace yazo sunada magana da shi. Bai wani damu ba dan duk zatonsa maganar dai bata wuce akan Maheer ba daya kasa kwantar da hankalinsa akan auren nasa.
Bayan ya gaishesu Daddy ya fara bayani kai tsaye kamar haka. “Shareff mun kiraka nanne matsayinka na Babba ga duk yaran gidan nan. Da farko dai akan maganar auren ƴan uwanka ne, Maheer ya samemu jiya akan yanada wadda yake so ba wannan da ake shirin masa aure da ita ba, sai dai mahaifiyarku tace bazai aureta ba, hasalima ta haramta masa auren yarinyar. Munyi-munyi da shi yaƙi ya sanar mana wacece, sai dai ya roƙemu mu roƙa masa ita ta amince masa dan ALLAH. To kai tsaye dai mun amsa wannan roƙo nasa, sai dai munce yayi haƙuri a ɗaura wannan ɗin tunda an riga an gama magana karmu kasance ƙananun mutane, munga rauni a tare da shi, duk da baiyi jayayya damu ba. Dan haka munaso ka kasance da shi dan hankalinsa ya sake kwanciya. Sai auren Aysha da shima aka ɗaga kamar yanda dangin ango suka buƙata, duk da dai bakama san da zancen ba dama mun bari sai ka dawo a sanar maka”.
Numfashi Shareff ya sauke a hankaki, kansa a ƙasa cike da girmamawa yace, “Insha ALLAH Daddy zanyi hakan, ita kuma ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi, duk yanda kukayi dai-dai ne ai”.
“Amin ya rabbi. Magana ta gaba kuma akan ƙanwarkane itama Mamana”.
Gabansa ne ya faɗi, amma sai ya cije bai nuna alama ba, sai ma ruwa daya ɗauka ya ɓalle murfinsa ya kai baki.. Daddy ya cigaba da faɗin, “Wasu dalilai sun sa mun yanke shawarar aurar da ita itama rana ɗaya da na Maheer ga wani bawan ALLAH da muke da tabbacin zai riƙe mana amanarta da izinin ALLAH. Itama an gama tsaida komai….”
Gaba ɗaya ya watso ruwan daya gumtsa har yana fesama Abbah dake a kusa da shi. “Subahanalillahi” Abba ya faɗa yana yana riƙo ruwan dake neman subucewa a hanun Shareff ɗin. Daddy da Abie kam sannu suka shiga masa dan bayan fesar da ruwan tarine mai ƙarfe ya sarƙesa. Idanunsa da sukai masifar kaɗawa da ja cikin ƙanƙanin lokaci ya ɗago yana kallon Daddy.
Sannu Daddyn ya ƙara masa hakan ya sashi maida idanun ya risinar. Daddy ya cigaba da faɗin “Karka damu munyi bincike mai zurfi a kansa kafin yanke wannan hukunci, sannan munada dalilai masu ƙarfi akan hakan. A matsayinka na babba saika sanya albarka a lamarin duk da yazo a ƙurarren lokaci ko”.
Kansa ya ƙara ɗagowa da ɗan haɗiyar yawu yana murmushin yaƙe. “ALLAH ya sanya alkairi”. Ya faɗa a takaice yana maida kansa ya dukar. Da amin suka amsa masa, daga haka suka cigaba da bayanin abinda yasa suka kira san. Bai bar wajensu ba sai kusan goma da rabi, ko’ina bai shigaba dan yasan duk sunyi barci ma yanzu ya shiga mota jiri na kwasarsa ya bar gidan….

   ★Ranar laraba aka saka amaryar Maheer a lalle, ga Anam dai babu abinda ya danganci hakan sai baƙi da suka fara cika gida. Sai a ranar alhamis ne da safe Abie da Mamie da Aunty Mimi da Abba da Daddy suka zaunar da ita. Bayan gama mata nasiha suka koma lallashinta, sai dai gaba ɗaya bata fahimtar wani fari ko baƙi a zantukan nasu, dan da alama brain nata ta raba tafiya da ƙwaƙwalwarta wajen yin aiki. har suka gama lallashinta taron ya tashi babu alamar numfashinta na fita daga gangar jikinta, a da kamar bata damu da auren ba, sai a ƙwanakin nan kuma jikinta ke mata matuƙar sanyi, rauninta na bayyana a zahiri. Bata samu damar fashewa da kuka ba sai da Aunty Mimi ta kamota suka komo ciki dan da suna a falon Abie ne.
  Mamie dai kasa tsayawa tai, sai aunty Mimi ce ke lallashinta amma kuka ya gagara tsayawa. Gaba daya ta birkice cikin ƙanƙanin lokaci har takai idanunta sun fara daina gani da ƙyau. Hankalin su Mamie ya tashi, amma basu yarda kowa ya sani ba wani abokin Abie amintaccensa doctor ne na ido yazo ya dubata. Ya tabbatar musu damuwace ta kawo hakan, dan haka ya basu shawarar ai mata allurar barci ta huta. Wannan shine dalilin hana yin kamun amarya a yau da aka shirya sai dai anyi ɗan shagali duk da ba kowa yasan minene ya hana ɗin ba. A take ƙananun magana suka baje gida musamman ga su Mommy.
 Duk da sun kasa gane kan zancen sunji farin ciki, har Gwaggo ta kasa haƙuri sai da tabi diddigin jin ba'asi, jin amarya Anam ce babu lafiya sai gata itada Mommy da Fadwa wai duba Anam ɗin lamarin zam-mamaki. Suna fita kuwa suka sanya dariya. Dan dama tun jiya suke dariya da ƙananun maganar rashin kawo lefen Anam gidan, acewarsu wane aurene haka kamar auren sadaka. Duk da zancen nasu ya koma kunen su Mamie harda su Daddy ma babu wanda yace komai.  
 Suna tsaka da wannan farin ciki Dr Jamal ya kira Fadwa yace tazo gida. Sagale tai tana kallon wayar dan ya yanke, kamar zata share sai kuma dai ganin da number ɗin Shareff ya kirata ta yanke hukuncin zuwa duk da kuwa a cikin tashin hankali suke da shi a kwanakin nan. Tadai danne ne kowa bai sani ba sai kawayenta su Sima dake ƙara tunzurata da tabbatar mata itace mai gaskiya.
  Tasan bama suba duk wanda zataima bayani dole zai bata gaskiya. Dan kuwa ita dai babu abinda tai masa a kwanakin nan ya ɗorama kansa wani irin baƙin rai da yafi halinsa data sani. A gaba ɗaya satin nan baya fita aiki kullum yana gida kwance, da farko ta fara lallaɓashi da son jin minene matsalarsa? sai ya dinga daka mata tsawa da faɗin karta damesa, ta shanye na farko dana biyu ana uku takaici da ɓacin rai yasa tai fushi itama ta sharesa. Sai shekaranjiya da Dr Jamal yazo ya dubasa wai bashi da lafiya, haka ta haɗiye taje ta masa sannu ta kula da shi kuma, amma hakan baisa ya sake mata ba. Zuciyarta ta ƙara tunzura tun a jiya ta haɗo kayan tahowa nan gidan biki, gudunma karya ƙara ɗaukar azaba ya ɗora mata ta sanarma Mommy ta masa magana akan zata dawo nan gidan har sai an gama biki, bata san yaya sukai Da mommy ba tadai kirata tace ta taho, koda taje masa sallama bai tanka mataba sai hannu kawai ya ɗaga mata, itako tai fushi tai fitowarta ta barosa duk da taga kamar baida lafiya, ga wata rama da yayi a ƙanƙanin lokaci. Amma murnar Anam zatai aure yasa takejin dolene ta zam gaba-gaba a bikin nan ai, shiyyasa ta tsallakesa tai tafiyarta........✍

Tofa, su kawu Sharuffudden mike hwaruwa ne haka da ciwo kuma?????????????????

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button