BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 33

Typing📲

  *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

BABU SO👉🏻AREWABOOKS

33

………Mommy ce ta shigo falon tare da aunty Iklima, batare data lura da halin da Fadwa ke ciki ba tafara magana cikin raba hankalinta biyu. “Fadwa a fiddo gift ɗin nan dan yanzu nake son ku wuce gidan wankin amarya ɗin nan ke da Bintu kafin sauran su biyoku a baya”.
      “Mommy inaga sai dai aunty Bintun tayi gaba. Dr Jamal ne yay kirana asibiti”.
    “Asibiti kuma? Mi ake acan É—in?”.
“Inagafa jikin Soulmate ne, dan nata kiransa dama É—azun bai É—agamin ba sai nai tunanin baĆ™in ran nasa ne bai gama sauka ba”. Ganin tana tafiya tana magana Mommy ta riĆ™ota da sauri. Kafin tace komai Fadwa ta rigata magana da Ć™oĆ™arin yin gaba. “Mommy wlhy hankalina a tashe yake idan na dawo mayi magana”. Sakin nata Mommy tayi, Fadwa ta Ć™arasa fita da sauri. Cikin sa’a ta samu napep data ajiye wasu mata.

        Azalzalar mai Napep data dingayi yay gudu ya sakasu isowa da wuri, ta miĆ™a masa dubu, yana mata maganar ga canjinta bama ta sauraresa ba tai gaba dan a rikice take. Tana tafiya tana kiran Dr Jamal, cikin sa’a ya É—aga ya sanar mata inda zata samesa, sai dai bata gane ba. Dan haka ya turo mata Nurse ta shiga da ita.
       Yana kwance samÉ“al Dr Jamal na gyara masa ledar Ć™arin ruwan da ake masa. Ta Ć™arasa cikin sassarfa gaban gadon, idanunsa a lumshe suke alamar barci, yayi wani fayau da shi saboda ramar da yayi sosai, wadda ita sai ma yanzu ta sake ganinta a bayyane garesa…. Dr Jamal da gaba É—aya yake cike da haushinta ya juyo yana kallonsa babu walwala tare da shi. “Fadwa yanzu kinyi dai-dai kenan? Mijinki na a cikin irin wannan halin amma kika tsallake kika tafi gidan biki kika barsa?. Badan ALLAH ya kai Khaleel gidan ba kin san kuwa komai zai iya faruwa?”.
      Kukan da take rikewa ta saki, ta kai duĆ™e gaban gadon tana kamo hanunsa da babu Ć™arin ruwan. “Doctor ni ban san jikinsa yayi tsanani hakaba wlhy, duk ta inda na É“ullo dan nasan damuwarsa ya kasa bani damar hakan..”
           “Amma sai ki sanar a gida tunda ke yaĆ™i ya sanar miki….”
    Shigowar su Abba ya hanata bashi amsa. Khaleel dake gaba ya watsa mata harara ya É—auke kansa. Taga harar tasa amma sai ta É—auke kanta, tare da zare hanunta daga cikin na Shareff. Abba da Abie dai sai maimaita sunayen ALLAH suke a bakunansu, dan yanda Shareff É—in yay fayau na rama a Ć™anĆ™anin lokaci ya basu tsoto. Dr Jamal ya gaidasu, tare da kwantar musu da hankali akan su masa addu’a dan jikin nasa da sauĆ™i. Addu’ar fatan Ć™ara samun sauĆ™in sukai masa, tare da jajanta al’amarin. Abie ya kalli Fadwa dake gefe tsaye, faÉ—a ya fara mata akan miyasa bata sanar da kowa Shareff É—in baida lafiya ba. Shiru tai taĆ™i tankawa, sai ma fuska data É—aure tamau dan kamanin Anam data gani tattare da dattijon ya bata tabbacin shine baban Anam É—in kuma Ć™anin Mamansu da suke uba É—aya. Duk da cikin taushin murya da sauĆ™aĆ™awa yake mata faÉ—an sai ta murguÉ—a baki, babu wanda ya lura da abinda tayi sai Abie. Maimakon yaji haushi amma sai yay Murmushi kawai.
    Abbah da jin bata amsawa Abie É—inba ya dubeta shima ransa a É“ace, baida faÉ—a amma in aka kuresa shima É—an babu sauki ne. Aiko ya balbaleta da masifa yana zaginta akan shiru dataima Abie É—in. HaĆ™uri Abie ya fara bashi amma yaĆ™i saurarensa, sai da yayi mai isarsa har Fadwa ta fara share hawaye sannan ya Ć™yaleta dalilin dawowar Dr Jamal É—akin.

      Cikin Ć™anĆ™anin lokaci rashin lafiyar Shareff É—in ta shiga kunnen kowa. WaÉ—an da basu riga sun wuce wajen kamu ba sai suka zarto asibitin dubasa. Babu wanda aka bari ya shiga wajensa dan ba’ason masa hayaniya. Sai Mommy data matsa ita da Gwaggo suka leĆ™asa. Har dare anata shigowa asibitin duba san, dan wandama sukaje gidan kamu daga can nan suka dinga zartowa. Hakan sai ya tabbatarma da jama’a mara lafiyan É—an dangi ne. Har sha biyu bai farka ba, anata ma Ć™ara masa ruwa har lokacin, dole kowa ya tattara ya tafi aka bar Khaleel da Maheer a wajensa duk da Fadwa harda kukanta itace zata zauna da shi.  A can gida ma Anam tana kwance rijif da zazzaÉ“i duk da doctor yazo ya dubata bayan na ido. Haka dai aka kwana zukatan mutane da yawa babu daÉ—i.

       Washe gari aka tashi da shirin É—aurin aure duk da rashin daÉ—in da ake ciki akan ciwon Shareff dan na Anam ba kowa ya sani ba. Da sassafe Fadwa ta wuce asibiti ita da Mommy data zillema mutane da Ć™yar. Sun samu ya farka har Maheer ya taimaka masa zuwa bayi yayo alwala. Yana cikin yin sallar daya makara ne suka shigo. Sun É—anji sanyi a ransu. Suna zaune harya idar, suka shiga jera masa sannu yana amsa musu da kai dan sam baya son yin magana. A dai-dai lokacin suma su Abba suka shigo harda Daddy, kamashi su Khaleel sukai ya koma saman gado, cikin magana Ć™asa-Ć™asa da bata fita da Ć™yau ya gaida su. Cikin kulawa duk suke amsa masa da tambayar Ć™arfin jikinsa. Ya amsa musu “Da sauĆ™i” akan laɓɓansa. Abba ya fara masa faÉ—a akan ya akai ya zauna da ciwo haka babu wanda ya sani? Sai kace wanda baida kowa?.
       ĆŠan murmushin Ć™arfin hali yayi na yaĆ™e, murya Ć™asa-Ć™asa yace, “Abba zazzaÉ“ine kawai shiyyasa. Kuma naji sauĆ™i Alhamdulillahi”.
     Abie ya girgiza kansa yana mai dubansa da tausayawa. “Wannan yafi Ć™arfin zazzaÉ“i kawai my son. Kaga kuwa yanda ka rame? Sannan a kwanakin nan gaba É—aya babu mai ganinka, mu duk mun zata aikine ya maka yawa shiyyasa”.
          ĆŠan murmushin yake ya kumayi sai dai baice komaiba anan ma. Idanunsa da sukai wani irin kaÉ—awa jazur ya lumshe da jingina a jikin filon da Khaleel ya saka masa. Ya buÉ—esu a hankali ya saci kallon Mommy da Fadwa dake zaune kowa ya zuba tagumi. A hankali ya furta “Mommy inajin yunwa”.
        Kai Mommy ta jinjina masa, tare da taÉ“a Fadwa datai zurfi a duniyar tunani. Numfashi ta kawo mai haÉ—e da ajiyar zuciya ta kalli Mommyn. “Kira su Bintu muji wai ba’a kammala abincin bane gashi yace yunwa yake ji”. Da to ta amsa. Tana shirin kiran waya sai ga sallamar Mom da Mamie. Su Abba ne kawai suka amsa da Khaleel. Suka shigo Maheer biye da su É—auke da basket, sai Mubarak da carton na ruwa. Daga Mom har Mamie fuskokinsu sun kasa É“oye damuwarsu akan yanayin Shareff É—in, suka shiga masa sannu da jera masa addu’a su Daddy na amsawa da amin. Mommy da Fadwa dai sunyi kamarma basu san da zuwansu ba. Abba ne ya bada umarnin Maheer ya zuba masa abincin dasu Mom É—in suka kawo tunda yace yunwa yakeji daman…
        Shigowar Doctor ta sakasu duk suka fito, Daddy ya dubi agogo, ganin lokaci yaja gashi yau juma’a ga É—aurin aure yace su ai gara su wuce gida ma Khaleel da Fadwa sai su zauna a waje sa, dan dama acan gida sune suka hana kowa zuwa har Gwaggo. Cema mutane akai kawai an ma sallamesa dan haka kowa ya dakata da yunĆ™urin zuwa aka maida hankali ga shagalin biki. Fadwa da Khaleel aka bar masa, su kuma gaba É—ayansu suka wuce gida, sai dai Maheer bai so hakaba, soyay shima a barsa anan basai yaje É—aurin auren ba. Amma babu yanda zaiyi su Abba suka korashi, ga Mommy sai zabga masa harara takeyi…..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button