BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 40

Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

40

………..Ya jima tsaye a ƙofar sashen tamkar mai nazari, kafin ya ɗaura hanunsa akan handle ɗin ya murɗa a hankali. Ƙamshi dai da aka sani da sashen kowace amarya ne ya fara tarbarsa, ya shiga da sallama kan lips ɗinsa idonsa na zagayawa kan komai na falon. Ya turo numfashi mai ɗan ƙarfi ta hancinsa, cikin tafiya kamar mai irga steps ya nufi bedroom ɗin da yake saka ran samunta, dama 3bedrooms ne a sashen iri ɗaya dana Fadwa ne, sai kitchen, store, falo, bedrooms biyu suna facing juna a corridor guda, ɗaya na a can gefe kusa da dining alamar dai na baƙine. Nan ɗin ma dai sai da yay ɗan jimm sannan ya tura ƙofar, babu kowa, sai dai shima yasha kaya tsaff. Maidawa yay ya rufe, ɗayan ya buɗe.
Kwance take ta dunƙule waje ɗaya, tare da lulluɓe duka jikinta da bargo. Hawaye take sosai ga rawar sanyi alamar zazzaɓine a jikinta. Ya ɗau tsahon minti uku yana kallonta duk da ba fuskarta ce a buɗe ba kafin ya cigaba da takawa cikin ɗakin sosai fuskarsa a tsume har yanzu da takaicin su aunty Lawusa, dan ma baiji abinda suke shiryama Fadwan ba kenan..
Isowarsa gab da gadon ya bashi damar jin yanda take sauke ajiyar zuciya a jajjere har tanayi kamar zata shiɗe. Sai kuma rawar sanyin da takeyi har yana iya ganin kaɗawar jikinta duk da a lulluɓe take. Hannu ya kai ya yaye bargon baki ɗaya, hucin zafi sosai ya bugesa…..
“Shiii!! wayyo sanyi-sanyi….” ta faɗa tana ƙoƙarin riƙo bargon da ya janye ɗin, bai bata damar yin hakan ba, ya kai hanunsa na dama saman goshinta. Sosai kan nata ma ya ɗauki zafi. Zumbur ta miƙe, dan sai yanzune ƙamshin turarensa ya kai ga hancinta, gaba ɗaya tama shafa’a da inda take. Tai saurin gyara glass ɗinta da ya sirranta kumbiri da jaan da idonta sukai tana ja da baya…
“Kina tunanin hakan da kika zaɓama kanki shine maslaha? Duba yanda jikinki yay zafi, idanunki suka kumbura saboda kukan da bazai miki amfani ba bayan kin san hakan a gareki matsala ce babba. Garama ki nutsu domin kukanki da borinki bazai canja komai ba”.
Wani irin kuka ne ya kufce mata na takaici da ƙara jin zafinsa. Yaja siririn tsaki da juyawa ya fice a ɗakin. Fillo ta ɗauka ta wurgama bayansa duk da ya riga ya fita sai ya samu ƙofa, ta ƙara ɗaukar wani ta jefa. Sai da ta jefa uku sannan ta zame ta kwanta tana cigaba da kukanta da ita kanta ta gaji da yinsa. Kusan mintuna bakwai ya dawo, akan fillos ɗin data wuwwulo ya fara sauke idanunsa, ya ɗan girgiza kansa kawai ya tsallakesu. Cup ɗin da ɗauke da tea ya ajiye tare da magani, batare da yace mata komai ba ya sake fita, bai jimaba ya dawo da goran ruwa.
“Tashi zaune” ya faɗa cikin bada umarni, dan yasan idan yay mata laku-laku bayin yanda yake so zatai ba. A yanzu ɗin ma duk da a yanda yay maganar sai da ya sake maimaita mata a ɗan tsawace sannan ta tashi. Da kansa ya gyara mata filo jikin fuskar gadon ya kuma taimaka mata ta jingina da ƙyau. Kusa da ita ya zauna yana mai kallonta tamkar mai nazari. Ita dai taƙi yarda ko sau ɗaya ta kallesa. Numfashi ya ɗan furzar da ɗakko kofin shayin ya miƙa mata. Cikin ɗashewar muryarta tace, “Ni na ƙoshi”.
A karon farko ya saki guntun murmushi dan shi dariya ma take bashi, yana dannewa ne kawai. Ya ɗan rufe idonsa ya sake buɗewa a kanta. “Shi borin naki ya shafi har cikinki da lafiyarki kenan?”. Ya faɗa cikin sauƙaƙa muryarsa har yanzu da murmushi akan fuskarsa. Baki ta tura gaba da ƙoƙarin zamewa zata sake kwanciya ya riƙota. Son zame jikinta take amma ya hana hakan, sai ma jawota da yay gaba ɗaya ta dawo jikinsa. Tsuma jikinta ya farayi, murya na rawa tace, “Nidai ka sakeni bana so”.
“An gaya miki nima ina so ne?”.
Yay maganar a hankali cikin kunenta. Da sauri taso janye jikinta amma ya hana hakan, murmushin dake son sake kufce masa ya danne, ya ɗakko cup ɗin shayin ya sake miƙa mata, ɗago idanunta da suka cika da ƙwalla tai ta kallesa, ganin ganda yay kicin-kicin da fuska ta maidasu ƙasa. “Bacci nake ji gashi kina ɓata min lokaci”.
So take ya fita ya barta dan haka ta amsa, ya ringa ya gama wucewa, dan haka ta kafa kofin a baki tai masa shan ruwa. Shi da kallonta kawai yake, ta miƙa masa kofin zata sake zamewa ta kwanta ya riƙota. Zatai magana ya harareta, baki ta murguɗa masa a kaikaice sai dai sarai ya ganta, baibi takanta ba ya ɓalla magani da ruwa ya bata. Tana gama sha bata yarda ta kallesa ba tai wuf ta kwanta tare da jan bargo ta rufe har saman kanta. Shima baice mata komai ba ya ɗauka wayarsa yana dubawa. Sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sannan ya ɗauka kofin data sha tea ɗin ya fito bayan ya kashe mata wuta….
A hankali ta sauke ajiyar zuciya dan likimo dama tayi ba barcin take ba. Ta ɗanji ƙarfin jikinta dama akwai yunwa tare da ita, sai dai duk da hakan jiri na ɗan ɗibarta kaɗan-kaɗan. Ƙofar ta tashi ta sakama key sannan ta cire kayan jikinta ta saka masu sauƙin nauyi, toilet ta shiga tayo alwalar kwanciya ta dawo ta haye gadon dajan bargon ta ƙudundune dan har yanzu sanyin bai gama sakinta ba.

  Daga shi har ita makara sallar asuba sukai, haka ya sashi yin salla a gida, yana kuma idarwa ya koma ya kwanta kamar yanda itama a nata ɓangaren kwanciyar ta sakeyi. Barcine cike da idonta, da alama maganin daya bata yana saka barci.
Ƙarfe kusan sha ɗaya ta farka. Alhmdllhi babu zazzaɓin hakama ciwon kan. Sai dai jikinta babu ƙarfi kamar yanda zuciyarta babu daɗi. Ɗakin ta gama ƙarema kallo da yaba ƙoƙarin iyayenta duk da batajin zatai tsahon zangon zama a wannan gidan. Ta wuce toilet tana sake tabbatarma kanta taƙaitaccen zama zatai. Da ruwa mai ɗumi sosai tai wanka, koda ta fito har ta gama shiryawa babu motsin kowa, taci alwashin bazata ƙuntata kanta ba, ba kuma zata sake yarda tayi kuka ba zatai yaƙin barin gidanne da ƙarfin zuciya dana ƙwanji, dan haka ta gyara gadonta sannan ta fito falo. Anan ɗin ma komai ya mata ƙyau dan an saka kalar da tafi so ne a rayuwarta. Tai ɗan murmushi tausayin iyayenta na ratsata, da sun sani basu wahal da kansu ba ma. Kitchen ta shiga shima ta ƙare masa kallo har store dake cike da kayan abinci na gara. Ta shiga ɗayan bedroom ɗin nan ma komai abin birgewa. Tunawa da wayarta data baro bedroom ya sata komawa, ta ɗakko ta fito ta tuna bata shiga ɗayan ɗakin dake facing nata ba. Kanta tsaye ta shiga kamar ko'ina, tai turus da ganin wanda batai zaton gani ba a ciki. Zaune yake a bakin gadon da alama yanzu ma ya tashi a barci, buɗe ƙofar ya sashi ɗago idanunsa. Ita ta fara janye nata cike da basarwa taja baya da nufin maida ƙofar ta rufe tana ɗan tsuke fuska da faɗin “Good morning”.
 Bai amsa mata ba, bai kuma janye idanun nasa a kanta ba harta maida ƙofar ta rufe. Cikin ɗan ƙunƙunini da murguɗa baki tabar wajen. Falo ta koma tai zamanta ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kunna wayarta. 
 Agogon dake ɗakin ya kalla, ganin har goma da rabi tayi ya sashi miƙewa ya fito a ɗakin, harya nufi hanyar falo sai ya tsaya cak, da baya ya dawo ya buɗe ɗakin data kwana ya shiga. Bai damu da rashin samunta a ciki ba ya shige toilet ɗinta, wanka yayi tare da ɗaukar cikin sabbin brush ɗinta ya buɗe ɗaya yay amfani da shi. Towel ɗinta ya ɗauro, ya riƙo wani a hannu yana goge jikinsa. Gaban mirror ɗinta ya ƙarasa yana bin kayan kwaliyyar dake kansa da kallo ɗaya bayan ɗaya, iska ya ɗan furzar daga bakinsa, sai kuma ya nufi ƙofa, kaɗan ya leƙa kansa duk da yasan bawai zai iya hangota bane....
 Har yanzu tana falon zaune abinta tana buga game hankali kwance, kai kace ba ita bace ta gama bori da rusar kuka ba jiya da sauran kwanakin da suka gabata. Jin kamar ana kiran sunanta ya sata ɗagowa takai dubanta ga hanyar corridor ɗin. Baki ta murguɗa jin ya ƙara kiranta cikin ɗan daga murya, cikin magana ƙasa-ƙasa da ba'ajin mi take faɗi ta miƙe. Harta nufi hanyar ɗakin data barsa ɗazun ta dakata sakamakon jin gyaran muryarsa a nata ɗakin, idanu ta zaro da riƙe ƙugu tana duban ƙofar, ta cije lip ɗinta na ƙasa cikin takun fusata da tsaurin ido ta nufi ɗakin tana wani ɗaure fuska ita a dole bazata masa ta sauƙi ba........✍

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button