AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 51-52

 ??51 and 52??

ViOHW????

Cike da mamaki momy tace “kamarya baki saniba?” Abba yayi gyaran murya momy tajuyo gurinsa, abba yace “kedaina tambayarta kijira ta samu natsuwa daga baya maji sauran zancen a gurin mijinta”

momy taso tayi magana sai kuma tafara domin tasan tana musa masa zai hau masifa, saita kame bakinta,
Suna zaune malam yashigo, yatarar da ameelah ta farka, godiya yayiwa Allah sannan yayiwa abba bayanin zasu iya tafiya da ita, taje cen gida takara samun natsuwa, abba yaciro bandur na kudi yabawa malam sannnan yayi godiya suka dauki ameelah,
Gidan hilal suka wuce da ita, hilal yabude gidan suka shiga momy ta rikata suka karasa har cikin dakinta, saman gado ta ajiyeta sannan sukayi sallama dasu suka tafi,

A mota momy tafara masifa anhata taji matsalar yarta wlh ba ai mata adalciba, abba shiru yayi ko kulata baiba yaci gaba da tukinsa, harsuka kasa gida masifa take, suna shiga harabar gidan abba yakashe motar ya rigata fitowa zuciyarsa cike da takaici ya nufi cikin gidan,
*** **** ***
Hilal kuwa kamar jira yake su momy sufita, suna fita ya shigo dakin ameelah, tsaye yayi akanta yana kallonta, cike da bacin rai, fuskarsa a murtuke,

Yana yinsa kadai ameelah ta kalla tagane cewa akwai matsala, taja jiki takarasa bakin gado, “mijina meya matsalar”
Hilal ya tsuke fuska daman jiran yake tafar magana wayarta ya dauko yanuna mata, nan yafara fada cike da hargowa “daman abubuwan da kike aikatawa kenan a cikin wayarki, daman cin amanata kike.. Ehhh ameelah kifada mana?” yakarasa maganar cike da hargowa, da kuma zafin zuciya,

Ameelah tayi rau rau da edo, tsoro yakamata matuka, kaku yasoma kubuce mata, muryarta na rawa tace “daman …. Ehmm..ehmm… “

” daman me Kifada mana, kifada…. Ya nuna kansa da dan yatsa “me kika rasa a gurina, kulawa, soyayyah, addini , ko kuma me, menai miki kike cin amanar aure na” yayi shiru yana jiran ameelah tayi magana amma takasa kuka kawai take,
Hilal yadaga wayar cike da zafin rai “babu matakin dazan iya dauka akanki domin bazan iya sakin kiba amma nasan wannan ce koh, wannan ce matsalarmu koh, to daga yau babu ke babu kara rike waya”

Da karfi ya narka wayar a kasa, saida ta tarwatse gabaki daya,
Ko uffan bai kara cewa ba ya juya yabar dakin yana huci,

Yana fita ameelah ta share hawayenta daman na munafincine, dukawa tayi tadauko fasanshiyar wayarta, taduba sim dinta taga yana nan, ajiyar zuciya tayi, tace “alhamdulillah, daman ni saki kawai nake tsoro, amma tunda baka sake niba, da sauki” tayi murmushi takara kallon wayar kafin tace ” hilal kenan kaida kanka zaka kara siyomin wata nasan yadda zanyi dakai”

Nan ta kwashe sauran fila2 wayarta ta ajiye gefe, sannan ta koma kan gado ta kwanta,
*** ***
A gefen afham kuwa, tun lokacin dayayi yiwa amal wulakanci momy tai masa magana, tun daga ranar yake gaba da momy, ya daina mata magana, koya ganta saidai ya sunkuyar dakai ya wuce, duk abinda yakeso saidai yasa aneesah ta kawo masa, (hmm kunji yayan zamani masu gaba da iyayensu, yanzu hakan wasun suke, da zaran iyayen sun sun musu fada to shikenan gaba ta shiga tsakaninsu, su ala dole ba a musu fada, hmm Allah dai ya kyauta)

Momy ce zaune a bakin gadon dakin abba tana kallonsa yana shiri, hulla yake sakawa yana duban mirror,
Damuwa ce tattare a fuskar momy tace “maganafa nake maka amma kayi banza dani, abubuwan yaron nanfa sunfara yimun yawa” tana karasa maganar tayi shiru,
Saida abba ya kammala saka hularsa sannan yajuyo gurin momy fuskarsa a daure yace ” afham yana ina” momy tace “yana dakinsa mana ” abba yafara taku “zomuje ” yanufi hanyar fita, momy uffan baka kara cewaba tabi bayan sa,

Direct dakin afham suka shiga, abba ya turo kofar da karfi yana kiran sunansa, yanajin shigowarsu ya mike tsaye, abba yatsaya yana kallonsa, afham ya sunkuyar da kai, abba yafara masifa “ka kyauta, kuma kayi daidai, wato kai dan zamani koh, kana gaba da mahaifiyarka saboda tayi maka magana akan Amal, to shikenan nima saika shirya yin gabar dani domin wlh bazan janye maganar aurenka da amal ba, idan zaka shirya kashirya domin munsaka ranar aurenku nan da sati daya, marar mutunci kawai ” abba yakarasa maganar cike da bacin rai, yajuya yabar dakin,
Kafin momy tafita saida ta dallawa afham harara, sannna tafita,

Afham ya duke kai yana kuka, sai bayan sunfita sannnan yazauna yafara masifa “Allah dai yasani nidai banason amal, auren dole saikace wata macce, wlh bazai yuyuba saidai nabar musu gidan su zauna sukadai, kuma suje su samo wani dan su aura masa amal, wlh gidan zan bari…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button