BABU SO 42
Typing????
*_❤????BABU SO....!!❤????_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
BABU SO????????AREWABOOKS
42
………Tsitt gidan ya koma bayan wucewarsu, sai ta sake komawa sukuku da ita. Cikin dauriya ta ƙarasa saka turaren wutar dasu Amrah suka fiffido mata da fresheners masu ƙamshi ko’ina ya ɗauki ƙamshi dama sannan ta wuce bedroom yin wanka. Koda ta fito shiri tai cikin doguwar riga mara nauyi ta ɗan gyara fuskarta da sakama jikinta ƙamshi ta tada sallar magrib. Bayan ta idar ne wani tsoro ya dinga tsikarar zuciyarta, dan shirun gidan yayi yawa matuƙa, sauƙin ma akwai wutar nepa dan anguwar suna samun wuta sosai. Bata damu da rashin ganin Shareff balle tunanin ya dawo gidan ko bai dawo ba. Tana nan zaune saman sallayar taji tsoronta na ƙara girma, sai ta ɗauka wayarta ta fara karatun alkur’ani a ciki…..
A daidai nan motar Shareff ta shigo gidan, a gajiye yake matuƙa saboda yau yayi yawo ne sosai cikin wani katafaren aikin babban estate da companyn su ke aikin ginawa. Yana China aka fara aikin, tunda ya dawo kuma ciwo ya kwantar da shi bai samu zuwa ya duba ba sai yau. Kai tsaye sashensa ya nufa, mamaki ya kamashi ganin ko'ina tsaf an gyara, ga wani ƙamshin turaren wuta na musamman na tashi ba irin wanda ya sani ba. Hatta da toilet ɗinsa tsaf yake sai ƙamshi ke tashi, ya ɗan saki huci wani kaso na gajiyarsa na raguwa dan shi mutumne mai tsaftar tsiya da kuma son tsafta. A gurguje ya zura jallabiya ya fesa turare ya fice massallacin anguwar tasu da ake ƙoƙari tada salla....
Tun daga shigowarsa ta farko har fitarsa a idon Fadwa ne dake leƙe ta window, taji matuƙar farin cikin ganin sashensa ya nufa ba sashen Anam ba. A ranta tace, (anya wannan amaryar kuwa ta cika amarya?) sai kuma ta bushe da dariya ranta fes, musamman data tuna sanda take cin nata amarcin yanda ya dinga nanan da ita kamar ƙwai. Amma sai gashi yau harda fita aiki bai kuma tashi dawowa ba sai yanzu. Gaskiyarfa su aunty Malika hayaƙi ba nata baneba, dole ta kwantar da kai taga da mi shegiyar ta shigo, shima kuma ina ya dosa... Falonta ta sake kalla taga komai tsaf ga ƙamshi na musamman irin wanda ta saka a sashensa na tashi, hakama jikinta babu wata makusa wando da rigar sun matuƙar amsarta. Ta sake sakin murmushi da ɗaukar sweet ɗinta mai ƙamshi ta jefa baki ta koma cikin kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana daukar ɗan guntun bidiyo da zata poster a tiktok kodan maƙiya da suka tasota gaba da izgilin an mata kishiya a watanni biyar kacal.. Tana tsaka da editin ɗin bidiyon ya shigo falon da sallama. Da sauri ta fito daga tiktok ɗin tana ajiye wayar fuskarta da ɗan murmushi tace, “Sannu da dawowa”.
Sosai mamaki ya ƙara neman kashesa, dan kuwa ya jima baiga Fadwa cikin irin wannan tsaf ɗin ba ita da sashenta. Cikin ɗan salo ta tashi tsaye tana faɗin, “Soulmate wai mi kake kallo ne haka kamar baƙo a sashen?”.
A karan farko ya ɗan ware idanunsa a kanta da sakin guntun murmushi, kansa tsaye dan bai iya ɓoye-ɓoye ba yace, “Dama da gaske ne mata idan aka musu kishiya sunfi yin hankali da tattalin miji?”.
Duk da maganar ta mata zafi sai ta dake, cikin murmushi ta matso kusa da shi ta rungumesa. “Haba Soulmate kamarya? Da bana tattalinka?”. Hannayensa duka biyu yasa ya ɗago fuskarta ya riƙe a tafin hanunsa, yayinda itama nata hannayen ke zagaye da shi sun manne da juna. Kallonta yake cikin ido, kaifinsu na sake narkar da ita a soyayyarsa da ƙaunarsa harma da kishinsa mai tsanani, dan tasan mijinta irin mazan da mafi yawan mata basa kalla su kauda ido ne saboda abubuwa da yawa daya tara musamman miskilanci dake saka mafi yawan mutane shakkarsa har ita a karan kanta... A hankali ya hure idanunta, tai saurin rimtsewa ta sake buɗewa cikin nasa da har yanzu suke a kanta. “Da gaske kin canja, haka nake so ki kasance mai yawan kula akan komai my love. Indai kika riƙe zaki mallaki Al-Mustapha a tafin hanunki cikin sauƙi”.
Wani irin shauƙin daɗi ne ya ratsata, ta sake rungumesa da jin kamar su dawwama a haka. Lallai kwallin idonka idona ɗin nan yayi, cikin ƙanƙanin lokaci ga aikinsa kai babu abinda zatace da su aunty Safarah sai ALLAH ya biyasu. A hankali ya janyeta a jikinsa, da sumbatar goshinta. “Bara naje naga ƙanwarki itama, dan ina son na zauna daku yanzun nan”.
Kanta ta gyaɗa masa tana murmushin yaƙe, bai sake cewa komaiba ya fice ransa na ƙara sanyi da canjawar tata......
Bayan ta idar da sallar isha'i har shafa'i da wutirinta tayi, batajin wata yunwa dan haka ta yanke shawarar shan yogurt kawai da Mamie ta sakko a cikin drinks ɗin da aka kawo mata, fita tai da nufin ɗakkowa ta dawo bedroom ɗin, da tasha zatai kwanciyarta dan ita dama akwai saurin barci. Koda ta ɗakko yogurt ɗin sai ta haɗo da dubulan guda ɗaya dan tana matukar sonsa balle wannan da yasha riɗi da zuma mai ƙyau. Daga wutar falon har ta kitchen duk kashwa tai, sai dai kuma rashin sabo yasa ta manta da rufe ƙofar falon ta wuce bedroom, tamkar jira tana shiga ana ɗauke wuta, dai-dai nan shima ya ɗaura hanunsa a handle ɗin ƙofar falon nata ya shigo. Ƙarar data saki ce ta ratsa masa dodon kunne, karo sukaci a tsakkiyar corridor ɗin bedrooms ɗin nata, sai kawai ta zabura ta sake fasa wata ƙarar.
Da ɗan lalube ya samu ya riƙota a cikin duhun ya manneta da jikinsa da lalubo kunenta yana faɗin, “K! Calm down ni ne fa”. Yanda yay maganar cikin raɗa ya saka tsigar jikinta tashi baki ɗaya, ta sake ƙanƙamesa da sakar masa wani shagwaɓaɓɓen kuka.... Baice mata komai ba, sai dai yana shafa bayanta a hankali hawayen na sauka a ƙirjinsa duk da bata kai har can sama ba saboda rashin tsahonta, dan shi sai da ya ɗan ranƙwafo sosai ya samu rungumeta da ƙyau. Maido wuta da akai ne ya sakata haɗiye sauran kukan ta shiga sakin ajiyar zuciya, sai kuma kamar wadda aka cikara ta zabura ta janye jikinta... Bai hanata ba ya saketa, suna haɗa ido tai saurin juya masa baya tana tura baki gaba. Bayanta ya ɗan tsurama ido, sai kuma ya zagayeta ya wuce bedroom ɗin nata. Da mamaki ta wara idanunta da basu gani da ƙyau tana binsa da kallo dan batama san inda glass ɗin nata ya faɗa ba, “Wannfa ai shine ƙarfin rai mai sata da sallama” ta faɗa ƙasa-ƙasa tana harar ƙofar. (Ƙarfin hali ɓarawo da sallama bahaushiyar malaysia????????).
Bin bayansa tai dan taga mi zaiyi mata a ɗakin. A bakin gado ta samesa zaune da wayarta a hanunsa. (Ƙarfin hali....) ta raya a ranta da nufar glass ɗinta dake yashe a ƙasa ta ɗauka ta saka. Dai-dainan ya ɗago ya dubeta ya kauda kai. “Babu abinci a gidan ne?”.
Bata fahimci tambayar tasa ba, dan haka ta gagara cewa komai, sake ɗagowa yay ya dubeta yana ajiye wayar tata. “Baki jini bane?”.
“Ni ban san zakaci ba shiyyasa naba maigadi, naga da safe da aka kawo baka ci ba, na rana daya rage ne na bashi na kumace kar Mom ta aiko na dare”.
“Kin bani na safen ne da kikaga ban ciba” ya faɗa cikin kafeta da ido, kallo ɗaya tai masa ta maida nata ta rissinar dan wani irin girma da kwarjini ya ƙara mata. Sai taji gaba ɗaya tsiwar tata bazata yuwu ba. Shima ɗauke nasa idanun yay a kanta batare da ya damu da rashin amsawar tata ba ya ƙara jeho mata wata tambayar. “K mi kika ci?”.
Ƙasa-ƙasa tamkar mai tsoron a jita tace, “Zansha yogurt”.
Maida kallonsa yay ga yogurt ɗin da dubulan data ajiye a bedside drawer, dama ruwa ta tuna bata ɗakkoba ta shirya komawa ɗakkowa aka ɗauke wuta. Jin baice komaiba ta saci kallonsa, “Kaima na kawo maka?”. Ta faɗa ganin har yanzu idonsa akan dubulan ɗin.
Miƙewa yay batare da yace komai ba, sai da ya ɗanzo gab da ita sannan. Idanunsa a kanta kansa tsaye yace, “Ki kawo, ki kuma haɗo da ruwa”.
Raka bayan nasa tai da hararar gefen ido, cikin kwaikwayon maganarsa da umarnin nasa ta maimaita abinda yace tana ciccijewa kamar dai yanda yayi. Sai kuma ta taɓe baki ta matsa wajen hijjabin sallarta ta ɗauka ta saka sannan ta fito duk tunaninta yana a falonta yana jira. Sai dai koda ta fito wayam, babu shi babu alamarsa. Cikin mamaki tace, “Wai miye nufinsa? Nakai masa can sashensa ko mi? Hu'umm”. Mi kuma ta tuna oho mata sai ta murgiɗa baki ta nufi kitchen ɗin nata.....
Tun shugarsa sashen Anam tana laɓe tana leƙe ta wimdonta da kallon agogo, ganin ya wuce mintunan datai tsammani zuciyarta ta sosu, ƙwafa tayi cikin takaici da son danne abinda ke ranta tana cusama kanta huɗubar su Aunty Malika, koda ya fito jitai kamar taje ta kamasa da duka amma babu damar hakan, barin wajen window ɗin tai ta shiga bedroom, ƙara gyagygyara jikinta tai da ƙara turare ta ƙara kwallinta da jambaki sannan ta fito hanunta riƙe da wayarta ta yano siririn mayafi batare da tunanin basu kaɗai bane ita da shi. Cikin yauƙi da yanga ta nufi sashen nasa tana murmushin data aro ta yafa ma kanta.....
A dai-dai lokacin Anam da batasan akwai zama ba ta shiga falon nasa bayan tayi sallama da knocking ya bata izinin shiga. Zaune yake a saman 1sitter ya miƙe ƙafafunsa duka biyu saman centre table da lap-top akan cinyarsa yana aiki. Ɗan ɗagowa yay ya dubeta da amsa sallamarta ya maida kansa ya cigaba da aikinsa. Ta ɗanyi mamakin jin falon na kamshi yanzu kuma a gyare tsaf ba kamar ɗazun da safe data shigo ba, sai dai ba huruminta bane hakan sai kawai ta ajiye a saman centre table ɗin gefen ƙafarsa kaɗan. A niyyarta data ajiye ta juya ta fita, sai dai tana ajiyewar kafin ta ɗago Fadwa ta shigo da sallama...........✍
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????