AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 55-56

??55and56??

Auren soyayya sukayi, baya tunanin ameelah zata iya cin amanarsa, (hmm baisan kuwa tagama ba )… cikin motarsa yakoma, yadafe kansa, yana tunin irin fadan da yayiwa ameelah, sai yaji duk tausayinta yakamashi,

Yafi kusan minti goma cikin motar yana tunani duk jikinsa yayi sanyi, 

Sannan yakunna motar yadawo gida domin jiyakeyi kansa namasa ciwo, dakinsa ya wuce baiko gayawa ameelah yadawoba,

Gado yasamu yayi kwanciyarsa, 
 ***     ***

Sai bayan la’asar lis ameelah tafarka, jikinta duk yayi tsami saboda dukan datasha,

A kasale tatashi tanufi bandaki, tahada ruwan zafi tayi wanka,
Jikinta yadan saki, tarage jin zafin bulalar, bata fito daga toilet dinba saida tayi alwala,

Tana fitowa tayi sallah azahar da la’asar, domin bacci tayi bata samu damar yin sallar azahar ba,
(Wa’iya zu billah, yan uwa mudaina wasa da sallah, sallah itace hisabinmu nafarko a ranar gobe kiyama, Dan Allah yan uwa mukiyaye)

Bayan ameelah tagama sallah, tatashi ta nade sallaya, ta ajiyeta saman gado sannan tanufi gurin mek up dinta,
Motsi taji a falo, murmushi tayi domin tasan bakowa bane sai hilal, fushi yake da ita shine bai shigo dakintaba,

Kwalliya ta chaba, wacca bata taba yiwa hilal irintaba,

Bayan tagama ta kalli kanta ta mirror taga tayi kyau tai murmushi sannan tatashi, tanufi gurin shirinta,

Wasu kananu kaya naga tadauko, tana kokarin sakawa, ( nan mukabar dakin muka fito waje, bayan minti biyar na leka dakin, ido na kafawa ameelah, wani irin kyau datayi)

A hankali ameelah tafara zagaya dakin, kamar mai kowon tafiya,
Tabbas tasan kwalliyar datayi danta janyo ra’ayin hilal ne zuwa gareta,

Cike da kinsa da karairaya tafito waje,

A falo tasami hilal yana kallon wani indian fim, RAJKUMAR…

Tundaga nesa hilal yaji kamshin turarenta, ya juyo suka hada ido, yagagara dauke idonsa,

??NOTE??
Muna bawa Masoyan littafinnan namu AMANAR AURE, haquri zaku d’an jimu shru na kwana biyu! Da kuma masoyan HAFSATUL KIRAM, kuyimin uzuri insha Allah dana dawo zan qarasa muku! Muna godia da ‘Kaunar littafanmu da kuke!??????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button