BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 45

Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

45

………Saukar hanunsa a wani sashe na jikinta ya sakata dawowa hayyacinta babu shiri, ta damƙe hanunsa da fisgar kanta baya tana sauke numfashi da sauri-sauri kamar yanda shima yake sauke nasan. Kunya tsoro da firgici suka zagaye zuciyarta a lokaci guda. Jin abin take gin-girin-gin tamkar a mafarki, bargo taja da sauri ta naɗe jikinta da juya masa baya amma sai ji tai ya riƙota, maidota yay jikinsa har yanzu yana kokawa da numfashinsa da bai gama daidaita ba. So take tace wani abu tsoro ya hanata, sai jujjuya masa kai take alamar ya barta.
       “Ni ba’a juyamin baya yayin kwanciya”.
   Ya faɗa cikin kunnenta da sake matseta a cikin jikinsa yanda bazata iya ko motsi mai ƙyau ba. Bata da zaɓin daya wuce yin shiru, dan tasan babu wani yunƙurinta da zaiyi tasiri tunda ruwa ba sa’an kwando bane. Sai dai kuma bata samu nutsuwar yin barci ba har sai da taji shi yayi..

        Rashin kwanciya da wuri baisa ta gagara tashi alokacin da sanyin asuba ya busa cikin ƙofofin fatar jikinta ya kaima jininta saƙo ba. Ta buɗe idanu a hankali tare da ƙoƙarin yin miƙa da tabbacin ta mance inda take. Rashin gani da ƙyau sakamakon duhun ɗakin ya taimakawa zuciyarta harbawa da ƙarfi irin na razana. Da sauri ta sauke hanunta kan abinda ƙwaƙwalwarta ta bata tabbacin mutum ne. Firgicin lokaci guda ya hanata damar tunawa balle yin nazari tai zaburar data farkar da shi daddaɗan barcin daya riskesa fiye dana farkon dare….
        Cikin zafin nama ya maidata jikinsa ya matse tare da kai ɗayan hanunsa ga makunnar fitila ya kunna. Tabbas badan hakan da yay ba babu abinda zai hanata wantsalawa ƙasa sakamakon gab suke da gefen gado ashe.
    “Relax!” 
  Ya faɗa cikin sarƙewar muryar wanda ya farka a barci, domin samar da nutsuwa daga mutsu-mutsun data cigaba dayi har yana iya jin yanda zuciyarta ke harbawa da sauri-sauri akan ƙirjinsa. Babu alamar zata nutsu ɗin, dan jin muryar tasa ma da alama sake hargitsata yay a dalilin ganewa da tuna komai mai alaƙa da inda take. Sarai ya fahimci yanzu ba tsoron bane, borin kunyane kawai tattare da ita, dan duk ƙoƙarin da yake na son tama buɗe ido ta dubesa hakan ya gagara, sai faman san zame jikinta take da nashi da kuma ƙoƙarin hana ƙirjinta sauka kan nasa ta hanyar tokare tsakaninsu da hannayenta. Dariya sosai ta bashi, amma sai ya gimtse baiyiba ya matsa kaɗan daga gareta. Damar data samu kenan ta wantsala gefe faɗuwar dai daya gudar mata tun farko sai gata tayita, zafin daya ratsata ya sata sakin ƴar ƙara. Yanzun kam bai iya daurewa ba sai da ya murmusa, batare da yace mata komai ba ya tashi yay shigewarsa bayi har lokacin da murmushin akan fuskar tasa.
        Sai da ta gama ƴan matse-matsen hawayenta sannan tai wuf ta miƙe jin kamar alanar zai fito, key ɗin da idonta ya gani a gadon ta ɗauka ta nufi ƙofa da sauri hijjab ɗinta a hannu da galashinta da shima ALLAH ya bata sa’ar gani. Fitowarsa dai-dai da ficewarta a ɗakin…..

       Bayan idar da salla tagumi ta zabga ranta fal takaicin abin kunyar daya faru a ɗakin Yaya MM daren jiya, ta rintse idanunta dake cikin glass tana cije lips kamar ta tariyo komai ta goge a rayuwa da zuciyarta ko zata samu sukuni. Tamkar tana a gabansa ta murguɗa baki da miƙewa, tana naɗe sallayar tana mita cikin yaren malay. “Idan kaga ma na sake kallon hanyar sashen can naka ba riƙeni na kwana ba kace har abada bazan fitoba ma mana, ko kunya bayaji yana mazurai da zare ido amma zuciyarsa saninta sai ALLAH. Toni an faɗa masa waccan shashashar matar tasa ce dake hauka akansa, mtsoww! Tana wani fiffika ita mai miji kamar ance ana son mijin natane balle ra’ayin zama da shi. Aikin ɓurr miye abin so jikin wannan mutumin mai baƙin hali, sai dai ita ɗin dan dama duk jirgi ɗaya ya kwaso su mtsoww!!”. Haka ta dinga mitar har takai kwance kan gado, kasancewar barci ne taf da idon nata cikin ƙanƙanin lokaci yay awan gaba da ita tsiwa fal bakinta daya tashi sama kamar zai taɓo p.o.p.

         ★★★

     Kamar su, itama dai makarar tata bai hanata tashi yin salla akan lokaci ba, koda ta idar kuma kasa komawa tai ta kwanta kamar yanda tai niyyar yi, sai ta ɓige da kiran wayar aunty Malika dan a yanzu sune ke bata dukkan ƙwarin gwiwar da bata samunta a gun kowa hatta mahaifiyarta data san suma suna a cikin tasu damuwarne game da wannan auren ƙaddara ko biyayyar daya sami mijinta da rana tsaka. Cikin muryar barci suka gaisa da aunty Malika…
      “Fadwa badai kin saka shashanci a zuciyarki kin gagara barci ba? Yanzu saboda abunda baida amfani kika zaɓi hana idanunki barci bayan mun gama miki da matsalar?”.
    “Aunty naso mantawa da komai tamkar yanda kuka faɗa sai dai na kasa. Wlhy na tsaneta shima a yau naji na tsanesa. Tare fa suka kwana a sashensa da ita”. Ta ƙare maganar da rushewa da kuka. Aunty Malika taja tsaki tana tashi zaune. “Lallai Fadwa ke shashasha ce gaskiya, yo duk da nasan cewar baki girmi yarinyar nan ba sai dai kuyi sa’anni kuma ita ɗin girman turaice ai banyi tunanin samunki haka muguwar lusara ba. Har mi akai wai akai wannan tsefatar yarinyar da kaɗan tafi wada tsaho. Fadwa kefa girman Nigeria ce, Nigeria ɗin ma Arewa, arewar ma kano kuma matsayin ƙabilar hausawa. Tunda kika taso a gidanku bayan mahaifiyarki kin sameta tare da wata matarne kafin ta fita tabar gidan, kinga kenan kinsan minene kishiya, kin san ilimin zama da ita tunkan ki buɗe ido kiga wata da sunan kishiyarki. Idan har kika cigaba da zubar da mutuncinki wajen zaman yin kuka ko bari Mijinki yaga lagonki to lallai k baki cika jinin zuri’armu ba…..”
     Cikin tarar numfashin aunty Malikan tace, “Aunty wlhy nayi dukkanin ƙoƙarina, ban aikata wani abu saɓanin wanda kukace nayi ba”.
         Ajiyar zuciya aunty Malika ta sauke. “Haka nake sonki ƴa tagari, ki zama jaruma kuma jajirtacciya a gidanta bawai lusara ba. Kamar yanda na faɗa miki yanzu ba’a bin boka ba’a bin malam akan kishi, kissa da kisisina da magungunan mata sune takubban ƴaƙar kishiya musamman irin taki da babu abinda ta sani sai kauɗi da buɗewar ido a cikin masu jajayen kunne. Kafin duniya ta goge mata idanu ta hango abinda kikema sakaci ki jajirce ki ƙwaci mijinki da wannan damar inba hakaba dare zaiyi miki, dare mai duhun tsiya da tafin hanunki ma sai kin gagara gani balle hanyar ceton ranki. Dan haka yanzu ki tashi ki haɗa breakfast mai rai da lafiya irin wanda baki taɓa masaba, kije ki shirya musu a sashen nasa kamar yanda ya buƙata”.
      Hawayenta ta share, duk da sam wannan shawarar batai mata daɗi ba amma zata jure, dan ita shaidace taga alfanun danne zuciya a jiya, badan ta shanye komai ta maidashi ba komai ba Shareff bazai ko dubeta ba akan abunda ta dinga masa tun daga fara rikicin auren nan. Amma gaskiyar su aunty Malika namiji tamkar yaro yake, duk kunnasan da kai da zarar ka lulluɓesa da kwalba sai kaifinsa ya zama mara tasiri ya koma haska maka zuciya da hasken wutar daka kunna masan. Da layin barci da dauriya ta shirya breakfast mai sauƙi kuma mai daɗi tamkar ba Fadwa mai babbake abinciba. Maimakon ɗauka takai sai ta fara shiga wanka, tsaf ta shirya cikin doguwar rigar lass ta caɓa ado tamkar ita ɗince amaryar, ta baje jikinta da kalolin turarren da tasan yafi so da ƙauna sannan ta fice ɗauke da basket ɗin data haɗa komai cikin yauƙinta da iya taku…
         Fitowarsa da ga bedroom yayi dai-dai da shigowarta. Sanye yake shima cikin ƙananun kaya masu taushi da rashin nauyi yanata bulbula ƙamshi. Ta sakar masa murmushi da faɗin, “Good morning Soulmate”.
      Idanunsa ya lumshe da jinjina mata kansa, laɓɓansa shima da ɗan murmushin. “Morning dear! how are you?”.
      “Alhmdullh” ta faɗa tana kauda kumburarrun idanunta da yakema kallon tuhuma, tasan shi mutum ne mai saurin fahimta, amma zatai duk yanda zatai domin hanasa hakan a wannan karon. Hanunsa ɗaya dake cikin aljihun wandonsa ya zare dai-dai yana ƙarasowa gareta, ya amsa basket ɗin. Batai musun bashi ba. Cikin zolaya da cigaba da kafeta da idanunsa dake tsumata ya kashe mata ido ɗaya.
      “Ai da nasan haka zan dinga samun gatan nan a wajenki dana jima da ƙara aure gaskiya”.
   Har cikin ƙwaƙwalwar kai maganar nan ta soketa. Harta kasa ɓoyewa fuskarta ta canja, amma sai tai ƙoƙarin saita kanta ta hanyar maida abun wasa ta hararesa da juya baya kamar tayi fushin wasa. Basket ɗin ya ajiye ya rungumota ta baya yana ɗaura habarsa akan kafaɗarta da murmushi bisa fuskarsa. “Juyawa Shareff ɗinki baya yana nufin lalacewarsa matata. Amma da gaske wannan aure yamun ranar zama ɗan gatan Fadwa”.
         Ita shaidace bai iya ƙaryaba, ko tace baya ɓoye-ɓoye. Duk abinda ya fito a bakinsa koda mai ɗaci ne shine iya gaskiyar dake zuciyarsa. Ta sani tayi kuskure a baya na gazawar bashi kulawa, duk da taci matuƙar burin hakan a garesa kafin aure……
   Jan hanunta da yay ya katse mata tunani, ya zaunar da ita a kujera yana faɗin, “Kinga jirani anan ina zuwa”. Kafin ta samu damar tuhumarsa harya fice. Ta bisa da kallo zuciyarta na ƙuna har hawaye na ciko idanun nata. Duk da gargaɗinta da zuciya keyi haka ta miƙe ta nufi bedroom ɗinsa wai ko zata samu sauƙin ranta idan bataga alamar abinda take tsoro ba…..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button