TAKUN SAKA 50

*_Chapter Fifty (End)_*…………ALLAH kuwa ya amsa addu’ar tasa. Dan a daren data koma gida kusan ƙarfe uku ta farka da matsananciyar naƙuda da dama kusan sati kenan tanata cinta a tsaye tadaiyi shiru ne kawai dan karya hanata halartar bikin su Amira. A rikice ya miƙe ya kira baba Saude. Wadda tana zuwa ta fahimci haihuwarma ta taho.
Duk yanda yaso su tafi asibiti hakan bai yuwuba. Dan kuwa dai abin yazo inji mai tsoron wanka. Ansha fama da gwagwagwa kafin ALLAH ya sauki autar Ummi lafiya gab da kiran sallar asubahi. Ta santalo ɗanta namiji mai kama da Ubansa sak. Lokaci da Master ya ɗauki yaron sai ga hawaye na rige-rigen sakkowa kan fuskarsa dan hakan ya tuna masa da randa Mamynsa ta haifi Habib. Ya rungume yaron wata irin ƙaunarsa na rsatsa jini da ɓargonsa. Sai da aka kammala gyara Hibbah tsaf bayan sallar asuba sannan ya shiga ya ganta. Su Habib ma sai lokacin suka sani.
Wayyo zo kaga murna da ihu. Yaro kuwa gaba ɗaya suka hau rububin ɗaukarsa Hibbah na kallonsu tana dariya da hawaye ita da Master, dan Alhmdllhi batajin wani damuwa a jikinta. Amma duk da haka sai da suka fita asibiti taga likita. Kasancewar babu wata damuwa suka dawo gida da wuri. Inda suka iske matan su Yaya Muhammad dasu Ameera amare cike da gidan. Dan tuni su Idris sun baza batun haihuwar. Hotunan yaro kuwa nata yawo a wayoyin ƴan uwa da abokan arziƙi.
Master yama yaro huɗuba da *ALIYU HAYDAR, ZAKI GADANGA ƘUSANR YAƘI*. Sosai Hibbah taji daɗi, duk da dai tasan shima sunan mahaifinsa kenan. Ammar kuwa ai cayay shi akaima takwara babu wasu su daddy.
Tsaye Baba Saude take akan Hibbah hakan yasa Ummi sam bata damu da batun a maidota gida ba tunda biki zasu shiga. Kwana biyu da haihuwa aka dire tarin kayan barka daga su Yaya Abubakar na ban mamaki. Dan har sai da Master yace sunyi yawa ai. Amma suka nuna masa zama su ƙaro kuwa.
Dole ya tsuke bakinsa yay godiya hakama Hibbah.
★★★
Duk da ɗanyen jego dake a jikin Hibbah haka aka tsunduma hidimar biki, sai dai ita kam babu damar yawan shigi da fici. idan kuwa ta kama dole zaka ganta cikin dogon Hijjab kamar yanda Baba Saude ta tilasta mata sakawa.
Randa take cika kwanaki shida da haihuwa aka ɗaura gagarumin auren ƙannen Master guda bakwai a babban masallacin juma. Taron aure ne daya samu halartar mutane manya dama jama’ar gari talakawa irinmu yaku bayi. Dan kuwa kowa burinsa nuna halacci ga Master. Zo kaga bakunan anguna uwa gonakin auduga. Sunyi shar dasu abin sha’awa da birgewa.
Washe gari aka haɗa bikin suna da karasun biki, inda kowa ke nuna bajintarsa. Amaryar jego Hibbah tayi ƙyau harta gaji ita da jariri Hydhar, wanda gaba ɗaya kamaninsa ke rikiɗewa zuwa Habib abin zam-mamaki.
Iya jigatuwa kowa ya jigatu, anci ansha ankuma raƙashe an ƙwalle yanda ya kamata. Dan kuwa Ammar ma dai yace shimafa auren nan yakeso nanda wata guda kacal, dan maganar gaskiya bazai bari su Habib su ajiye ƴan dugwi-dugwi ba shi yana sake da baki ga Hibbah da ɗa.
Zuwa dare aka kawo amare ɗakunansu, kowa ya kama gabansa akabar su Hibbah da sauran aiki.
____________________
Kamar yanda Ammar ya ambata shima kam ALLAH ya amsa masa. Dan bayan bikin su Khalid da wata guda cif aka ɗaura nasa auren da amaryarsa. Hibbah kuwa ta samu nayi. ta tasashi gaba da sheri kala-kala ta rama duk bashin da yaci akanta tsaf.
Bayan bikin Ammar da kwanaki tara suka wuce Umrah ita da Master ɗinta da Hydhar. Dan Master yace yana buƙatar hutu kasancewar tayi arba’in. Sai da suka fara zuwa ƙasar dubai suka more rayuwarsu na tsahon sati biyu kafin suka wuce saudia domin gabatar da umrah. Daga saudia Canada suka nufa wajen Abdull dake shirin tattaro iyalansa ya dawo gida shima.
Zokaga murna wajen ƴaƴan Abdull din da matarsa duk da kuwa a waya suka san juna da Hibbah. Hydhar kam ya zama ɗan gata dan koyaushe yana nane da yaran. Da wannan damar su Hibbah da Oganta Master suka sake ɓarje guminsu da gajiya a ƙasar canada.
satinsu biyu cif a canada suka ruguntsumo da iyalan Abdull suka dawo gida. Inda suka iske rasuwar hajiya mama.
*_AKWANA A TASHI_*
_A KWANA_ a tashi babu wahala wajen UBANGIJI, dan kuwa cikin ƙanƙanin lokaci rana ta zama dare, dare ya zama kwana, kwanaki sun koma sati, sati sun zama wata. Watanni sun rikiɗe shekara. Kafin cikar wasu buruka shekaru sunta ninkuwa a cikin rayuwar su Hibbah.
Alhmdllhi zuwa yanzu yaranta uku, hakama su Yaya Muhammad yara uku-uku suke da, dan haihuwar ta cigaba da tafiya musu ne kamar yanda suka fara. Family ya haɗu cif ga Ummi abin birgewa. Hakama ga Master burinsa ya cika. Dan suma su Habib yaransu bibbiyu yanzu suda Ammar. Family biyu sun dunƙule waje guda sun koma zuri’a ɗaya.
Yau data kasance Friday sauri-sauri Hibbah ke ƙoƙarin kammala ayyukan gidan kafin sojojin gidan su dawo makaranta. Dan Hydhar da yaransu Habib na farko duk an sakasu, sai ɗiyarta ta biyu mai sunan Mamyn su Master suna kiranta mimi. sai na ƙarshen da shima rarrafe yake ko ina mai sunan Master ɗin. Wato Isma’il, suna kiransa Ansar.
Kasancewar duk juma’a a tare suke haɗuwa da matan su Zaidu suyi girki mai yawa da ake fita da shi sadaka shiyyasa komai bataiba a sashen nata daya danganci abinci. Sai ɗan fruit salad data shiryama Master da fura damammiya da taji kayan haɗi.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta saka ƙamshi ta faɗa wanka, dan Ansar na wajen Sharifat data zama budurwa. Dan ayanzu hakama a wajenta take ta bar hannun baba saude dake fama da ƙafa zuwa na tsufa. Rigimar da yaketa tsilala mata ce tasa Sharifat ɗaukarsa suka tafi can compound inda matan su Adam ke girki. Dan dama ba barinta sukeyi tayi ba ita, sai dai ta duba abinda baiyiba.
Suna tsananin bata girma kamar yanda suka samu mazajensu na mata itada Masternsu. Ita kuma ta tsare mutuncinta bata bada wata ƙofar da raini zai shiga tsakaninta da wani a cikinsu ba. Yaransu duk ta haɗe da nata tana kulawa da basu tarbiyya kamar yanda suma sukeyi. Koyaya taga saɓanin zai shiga tsakaninsu zatai iya ƙoƙarin ta taga ta gyara komai cikin hikima…….
Da sauri ta buɗe idanunta saboda jin an buɗe ƙofar toilet ɗin. Ta sharce ruwan dake sauka mata a fuska tana kallonsa dan dama tasan sai shi ɗin. Harara ya sakar mata yana kwance towel ɗin jikinsa ya shigo wajen wankan da dungure mata kanta. “Yarinya kinsan dai kin saɓa doka ko? To wankanki baiyiba sai kin koma farko”.
Fuska ta ɗan ɓata da turo hanunsa dake ƙoƙarin ɗora mata soson daya haɗama kumfa. “Ban yarda da wayon nan naka ba Daddyn Hydhar. Ai yanzu muka gama waya amma baka sanarmin kana hanyar shigowa gida ba”.
“Kinma isa”. Ya faɗa da dungure mata kai ya turata jikinsa yana goga mata sosan. Son ƙwace jikinta ta cigaba dayi amma ya hana. Daga haka suka koma kokawarsu ta masoya suna dariya. Har dai takai an koma asalin soyayyar datafi ta kokawar wanka. Cikin nishaɗi da farin ciki suka kammala wankan nasu dana abinda ya biyo baya suka fito yana tsokanarta da fitinanniya.
Dariya tayi da yarfa masa ruwan hanunta. Cikin ɗaga gira tace, “Kai kuma Master na fitinannun miye sunanka?”.