BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 76

   “Please yaya k…..”

Hannu ya ɗaga masa alamar kar yace komai. “Ka gafarceni Yaya, ka bani to na tuƙaka”. Bai sauraresa ba ya tada motar ya fice dasu da gudu. Duk magiyar da Khaleel ke masa bai nuna yaji ko daya ba har suka iso gidansa cikin ƙanƙanin lokaci. Tun a gate mai gadi ya sanar masa Fadwa ta fita ai tare da wata mata. Reverse yayi, nanma Khaleel nata roƙonsa amma ya sharesa. Kai tsaye gidansu Fadwan ya nufa, dan baiyi tunanin taje gidan bikin ba. Sai dai anan ɗin ma dai maigadi ya sanar musu bataje ba, sai dai sunga hajiya ta fita zuwa gidan biki. Khaleel da yasan ba saurarenaa zaiyiba yace, “Bara mu bincika ko tana can gidanmu din”. Bai tankaba nan ma. Khaleel kuma bai fasa kiranba. Cikin sa’a ya samu Amrah, ita ya tambaya ko Fadwa na gidan ta sanar masa eh tazo gashi ma ana rigima tsakanin Gwaggo Halima da wasu dangin Mommy. Amma ga su Abba sun dawo gida yanzun nan….

   Gudun da yay a yanzu yamafi na farko, dan cikin ƙanƙanin lokaci suka iso nan gidansu, sai dai sun sami rigima ta ɓarke sosai tsakanin Mommy da danginta, da kuma Gwaggo Halima. Har Fadwa ta mari aunty Sakina saboda itama tace zata mari Gwaggo Halima. Gida ya cakuɗe harda dambe, Mommy na faɗin Shareff yazo sai ya saki Fadwa a yau, Gwaggo Halima na iƙirarin itama sai Daddy ya saki Mommy a yau. Ran Daddy yakai ƙololuwar ɓaci a yau shi da Mahaifin Fadwa daya biyosu gidan domin yima su Mommy murnar an ɗaura aure. Hajiya Luba mahaifiyar Bibah itace ta fara ganin Shareff. Ta nufesa tana kuka bayan ta gwargwaɗa ma Mommy cewar ga Shareff nan. Isowar Mommy inda Shareff ɗin yake tana rantsuwar in bai saki Fadwa ba zata tsine masa Daddy ya dakatar da ita, sai dai kafin ya faɗi abinda yay niyar faɗa Abie ya dakatar da shi. 

   “Please yaya karka ce komai dan ALLAH, inaga ya kamata a zauna dasu ko yaya asan dalilin wannan tashin hankali. Ba’a gyara ɓarna da ɓarna na roƙeka”.

   Da ƙyar Daddy ya saurari Abie a wannan gaɓar, Gwaggo da dama haka takeso tai murmushi, sai kuma tai saurin nufosu tana matsar ƙwalla. “Ni wannan fitina ta wannan yara ta isheni Muhammadu, gaskiya an shiga tsakanin Nafi da Halima dan da dai ba haka sukeba. Yara kansu haɗe kamar uwa ɗaya uba ɗaya ta haifesu amma yanzu komai ya canja…..”

   “Kinga Gwaggo kiyi haƙuri komai zai daidaita insha ALLAHU, inaga ku mu shiga can tunda nan da mutane.”

    Gwaggo ce da kanta ta tattara su Gwaggo Halima zuwa gidan Abie, shi kuma Abie ya saka su Shareff da gaba ɗaya yama rasa abinyi gaba. Sai da kowa ya hallara har mahaifin Fadwa da su Baba Ibrahim dana duk wani mai faɗa aji a falon kasancewar duk dangi na gidan, maza sun taso a wajen ɗaurin aure, matan kuma duk suna a cikin gida. Ran baba Ibrahim a ɓace ya dinga zagin su Mommy a yau dan shikam halinsu ya fara kaishi maƙoshi. Fitina daga wannan sai wannan kamar sune kaɗai mata a cikin family ɗin.

     Hayaniya na neman ɓarkewa ya daka musu tsawa, amma sukaƙi saurarensa. Daddy da dama a wuya yake kai tsaye ya buga musu tsawar da tafi ta baba Ibrahim. “Tabbas a wannan gaɓar na gaji da halinki Nafisa. Kije na sakeki saki ɗaya”. (biyu kenan????????).

   Lokaci ɗaya falon yay tsitt tamkar ruwa ya cinye kowa. Gwaggo da tafi kowa firgita dan ita Gwaggo Halima take burin ganin an saka ta waro idanu, “A’a Muhammadu bakai gaskiya ba, yo ai ba Nafi ta cancanci saki ba Halima ce, ko kuwa dan ita ƴar uwarkace shiyyasa. To wlhy yanda ka saki Nafi kaima Sadiqu sai ka saki Halima in har na isa da kai matsayin ƙanwar uwarka”.

    Hajiya Luba ta fashe da kuka. “Gaskiyafa Gwaggo, Halima ita ta cancanci saki kodan baƙin halinta ita da ƴarta…..”

   Saukar mari Hajiya luba taji a kuncinta tauu, kafin ta dawo hayyacinta Gwaggo Halima ta sake sauke mata wani. “Babbar magana kenan”. Cewar Gwaggo tana miƙewa. “Halima shine zaki mareta dan ta faɗi gaskiya, to idan Mustapha da Sadiqu sun sakeku ba dan an saki Nafi ai dole su sakeku dan zubarda ciki da Fadwa taima Mustapha………..✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button