BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 76

Chapter: 76

……….Sun iso gidan biki inda yake tanƙam da jama’a. Dan maza nata shirin wucewa massallaci saboda an haɗe ɗaurin auren waje guda har na Khaleel domin sauƙaƙawa mutane. Cikin takama da isa Gwaggo Halima da Fadwa suka shigo cikin gidan, anan fa kallo ya koma sama dan ko makaho ya shafa yasan naira ta zauna. Kai tsaye sashen Mom suka nufa dan ko kallon sashen Mommy a yanzu Gwaggo Halima batayi a gidan balle Gwaggo. Mom da babu ruwanta dama tai musu tarba ta mutuntawa duk da kuwa tunda aka tsira bikin sai yau kowa yaga idon Gwaggo Halima a gidan. Tadai aikoma Abba da Daddy Da mom gudun mawa. Shi kansa Khaleel mota ta danƙara masa duk dan cusama Mommy haushi. Tuni ƴar rahoton Gwaggo taje ta sanar mata isowar su Fadwan. Tai murmushi mai alamomi da yawa tana mai miƙewa, cikin toilet ɗinta ta shiga, duk da kuwa ta hana kowa shiga mata bedroom dama. Amma duk da haka bata yarda ta tsaya iya bedroom tai wayarba. Daga can aka ɗaga, fuskarta ƙawace da murmushi cikin bada umarni kuma tace, “Ki tabbatar da an ɗaura aure ki tura masa, dan ina son maimakon su iso gida da labarin farin cikin an gama ɗaurin aure lafiya, labarin ya canja”. Batako jira amsa ba ta kashe wayar gaba ɗaya.

    Cike da farin cikin sake aurar da yaransu lafiya su Daddy suka bar gida, tare da tawagar sauran ƴaƴansu su Shareff da ango Khaleel da tarin abokansa da ƴan uwa da abokan arziƙi. An fara yin sallar juma’a, sannan aka ɗaura auren Khaleel matsayinsa na babba, sai na Aysha da nata angon. Nan fa bakin kowa ya washe anata gaisuwa musamman su babban Yaya Shareff da Maheer. Anguna kam ai ba’a magana. Bakunansu har kunne ko gonar audiga albarka. Daga massallaci aka kwashi tawaga zuwa hall ɗin da aka shirya walimar cin abinci ta iya mazan kawai kamar yanda su Daddyn kanyi a duk aurarrakin ƴaƴansu.

   Ana tsaka da cin abinci saƙo ya shigo masa. Shi dama ba abincin yakema ci ba, yana charting ne da Anaam ta WhatsApp. Baibi takan saƙon ba ya fita da nufin rufe datan sai Anaam ta sake turo massege, ya koma da nufin buɗewa ya gani hanunsa ya buɗe wancan a mistake. Ganin videos da yawa ya bashi mamaki, sai yay tunanin shiga ɗaya a ciki yaga minene. Gabansa yay wani irin faɗuwa sakamakon cin karo da Fadwa, best ce sanye jikinta fara da dogon wando, kanta babu ɗan kwali, da sauri ya fito, mikewa yay zai bar hall ɗin dan bai kamata ya gani a gaban wani ba. Ya fito sai ya samu wasu a abokan Khaleel tsaye su kusan huɗu tsaye, da alama suma sun fitone susha iska. Suka gaisheshi ya amsa musu da fara’a, harya gota su sai ya tsinkayi muryar wani a cikinsu na faɗin,

   “Tabb bala’i, Mubeen da’alama yau zamusha kallo a tiktok. Gasu Sufi nan sun taɓo mutuniyarka Fady Babie”.

  Wanda aka kira Mubeen yaja tsaki, “Shegiyar yarinyar nan ai su Sufi ɗinne dai-dai da ita. Ƙawartace jiya taima Ɗan soja wani Comment ɗin rainin wayo shine fa yay mata tatas ya kuma ce yanada video ɗinta da taje ɗakin wani guy, idan bata kama kantaba ana gab da cin kasuwarta a tiktok, shine ita mai bakin akku Fadwan ta maida murtani jiya da dare, ai shagalin nan ne yasa bakama luraba, tun jiya aka fara faɗan har suna zasu ɗakkoma su M soja ƴan sanda, shine shi Sufi ɗin ya shiga faɗan”.

   “Oh dama haka akai, taɓɗi jan. Ai dama ina fatan naga wanda zai kawo ƙarshen ƴan iskan yaran nan, musamman Fadwa ɗin nan ta cika ɗaukar kanta wata tsiya. Ƴar iska tayi auren ma kamar batai ba”.

   “Ai bazaka ganeba yarinyarce ta haɗu, wlhy da farko ban yarda bahausa bace ƴar arewa. Irin zuƙaƙan matan nan ai dole suyi girman kai dan ALLAH ya basu. Idan fa tai shigar ƙanan kaya kamar wata balarabiya”.

   Dariya mai maganar farkon yayi, “Shege ka ƙyasa kenan, to tana dai da aure, akwai wani room mate ɗina, ya rantsemin idan yaga yarinyar nan har hankalinsa tashi yake, har saida takai sai ya dinga wassafata a ransa ya buƙatarsa ta biya yake samun nutsuwa”.

   A tare suka kwashe da dariya. ”Kai wlhy bashi kaɗaiba. Akwai lokacin datai wani shegen shiga tabi waƙar mara mutuncin nan ranar jinai inama-inama, bara kaga video ɗin ALLAH yasa bata gogesa ba.”

   Jiyay kamar jiri na ɗibarsa. Amma kun san halin ƴan mazan sai ya dake ya nufi samarin domin tabbatar da Fadwa ɗinsa ko wata. A hankali ya iso ta bayansu batare da sun fargaba. Wanda aka kira Mubeen na nuna musu video da yake faɗa. Ba ƙaramin tsinkewa zuciyarsa ta shigayi ba, dan ko’a magagin barci aka nuna masa video ɗin zai shaida wacece a cikinsa. Da baya-baya ya dinga tafiya har ALLAH ya bashi ikon jingina da motar dake kusa da shi, dai-dai nan Khaleel ya fito da babban abokinsa. Cikin salo irin na abokai yake ƙundumoma abokan nasa zagin mi sukeyi anan. Ganin basuma ko jisa ba ya karaso inda suke.

   A firgice yace, “What!!?”.

Yana mai fisge wayar. Shi kansa zuciyarsa ce ta shiga tsitstsinkewa, idanunsa sun gaza cigaba da kallon videon dan koba komai matar Yayansa ce. Yayan nasa kuma mai tsananin kima da mutunci a idonsa….

  “Kai lafiya kuwa?”.

Mubeen ya faɗa yana fisge wayarsa. Dariya sauran suka kwashe dashi. Anas yace, “Ka sani ko shima ya shiga tarko ne. To ka rufa mana asiri an jima zamu kaika ga taka wannan dai kwalelenk….”

  Ai Khaleel baima san ya kaima Anas ɗin mari ba. Su duka suka zabura da waro idanu. Khaleel ya nunasa a zafafe. “Ka iya bakinka Anas, kasan ɗin ita wacece a wajena? To matar yayana ce, idan ƙazamin bakinka ya sake faɗar wata magana mara daɗi zan fasashi”.

   Sun tsorata ƙwarai da gaske da rikicewar tasa. Mubeen ya dubi Khaleel ɗin a karo na farko cin son yin tunani. “Khaleel dan ALLAH kwantar da hankalinka. Wlhy sai yanzu dakai maganar matar yayanka wani abu ya ɗan dawo min a zuciya. Tabbas sanda ta ɗaura wani hoto nata tunanin a ina nasan mutumin, hakama da take daurasa matsayin mijinta na jima ina son hasasowa amma sai na kasa. Saboda sau ɗaya na taɓa ganin Yayan naka shima ba wani mun jima bane. Da gaske wannan shashashar yarinyar ce matar Yayanka? Kasan kuwa wacece Fadwa a tiktok? A ɓangaren shaiɗanun tiktok da a kullum ake ALLAH wadai da su da ganin sakacin duk wani na kusa da su wlhy Fady na sahun farko, dan ita a karan kanta mata uwar shaiɗanuce mai zaman kanta. Amma domin tabbatarwa maza ka shiga shafin nata ka duba zakafi yarda dani dai”.

   Gaba ɗaya Khaleel yayi mutuwar tsaye, dan kuwa tun fara maganar Mubeen idanunsa suka hango masa Shareff dake tsaye alamar komai da suke yana jinsu. Shi a karan kansa Khaleel ɗin baya tiktok, bawai dan yana kallon tiktok ɗin baida amfani bane, a’a, a komai na rayuwa akwai mutanen banza a waje akwai na kirki. Shi bai taɓa ƙalubalantar tiktok ba ko yima jama’ar dake mu’amulantarsa kuɗin goro. Ya tabbata idan aka shiga tiktok za’aci karo da abubuwa masu amfani kamar yanda za’a samu na banza marasa amfani. Kawai dai shima bamai ra’ayin yawan biye-biyen shafuka bane kowanne iri. idan ma ya kama sai yabi abinda ya kaisa kawai yake zuwa yayi saboda aikinsa na cimasa kaso mafi yawa na lokacinsa. Da sauri yabar inda su Mubeen suke ya nufi Shareff daya shiga mota da alamar barin wajen zaiyi. Buɗewa yay ya shiga gefensa.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button