BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 77

Chapter 77
77

……..Kaɗan ya rage zuciyar Fadwa yin tsale ta fito, jikinta na rawa tace, “Wlhy ƙaryane, munafukar tsohuwa da bazataga MANZON ALLAH ba”.

  Saukar mari taji lafiyayye daga Mahaifinta. Gwaggo ta jinjina kanta cike da jin daɗi, “Nagode Sadiqu. Ba laifinta bane uwace bata moraba. Yo dama yaushe Halima taga wata tarbiyya balle ta bata. Ai bakai dace da mata ba wlhy”.

  Cikin matuƙar mamaki su Daddy suke kallo da sauraran Gwaggo da alamu suka nuna akwai suɓutar baki a kalamanta. Gwaggo Halima zatai magana Alhaji Sadiq ya dakatar da ita. “Wlhy kikace tak sai kinyi nadama Halima…”

   “Barta tace in ma tanada abin cewar mana. Dan kuwa inada ƙwaƙwaran hujjar ita ta zubar da cikinta da kanta, saboda karya hanata waɗan nan raye-rayeda sukeyi na zamani a wannan abubuwan da kuke kira yanar gizo-gizo ko uwar mima. K Luba kiramin Bibah ta shigo da likitan da ta saka yaymata aikin. Amma kafin sannan fara latso min ita a wayarki su gani”.

   Cikin rawar ɓutiya Hajiya Luba ta latso Fadwa a tiktok ta miƙama Baba Ibrahim dake a tsakkiyar Daddy da Abie, sai Baban Fadwa a gefen Daddy, Abba kuma na gefen Abie. Wani video ne na rashin mutunci da aka ɗauka a ranar kamun Fadwa. Ana gobe ɗaurin aurenta da Shareff kenan. Kayan barcine jikinta riga fingila iyakarta cinyarta amma ta kusa gwiwa, sai gashinta dake a buɗe tama warwaresa akan kafada. A yanda taketa komanta kai tsaye da farko na rawar wata wakar turanci zaka san bata san ana dauka ba. Sai a kusan ƙarshe-karshe take kare jikinta da filo data ɗauka tana masifar miyasa zatai mata video, sai dai anyi cutting sunan wadda ta ambata na mata video ɗin. Bayan shi akwai wasu daban-daban na rashin mutunci, abindama zai baka mamaki kamar an tsinto iya wanda tayi abin ALLAH wadai ɗinne kawai an ɗora a shafin. Hatta wayarsu ta ranar daurin aure da Shareff duk akwai a wajen, duk wani faɗa datai da wani a tiktok ko rawar banza cikin shigar wofi duk sune aka tato aka ɗaura. Harda ma wanda bata kai tiktok ɗin ba

    Komai ya ƙara tsayama Shareff cak, bama shi kaɗaiba hatta sauran jama’ar falon gaba ɗaya. Kafin wani ya samu damar tofa tasa sai ga Bibah da likitan daya zubdama Fadwa ciki. Harga ALLAH tayi matuƙar firgita. Zuciyarta ta dinga tsitstsinkewa lokacin da Gwaggo ke faɗa masa ya faɗi miye alaƙarsa da Fadwa. Kansa tsaye babu fargabar komai saboda an toshe bakinsa da kuɗi ya fara bayani tiryan-tiryan tun zuwan su Fadwa da ƙawayenta Sima da Amal. Baice akwai Bibah da Siyyah ba. Sai yanzu ne Fadwa ta samu damar fashewa da kuka.

   “Wlhy wlhy ba haka akaiba. Bibah kiji tsoron ALLAH, dan kina son auren mijina basai kin ƙullamin sharri ba…..”

   “Sharri kuma. Idan sharri nake miki aiga wayarki a hanunki a amsa a duba agani”.

  Duk da Fadwa tasan duk waɗancan videos ɗin tayisu amma ta goge mafi yawa a ciki saita bada wayar tata, saboda sanin masu dama-damar ne kawai a shafin nata na yanzun. Baba Ibrahim ne ya amshi wayar, sai dai koda aka duba babu wani accaunt akai sai irin wanda Bibah ta nuna.

     “To’ai babu banbanci tsakanin wannan da wanda ke anan ciki”.

  Ba karamin ruɗewa Fadwa tai ba. Harta fisgi wayar a hanun Baba Ibrahim batare da tasan tayi ba. Koda ta duba itama sai taci karo da abinda suke maganarne kawai babuma accaunt ɗinta data sani akan wayarta kwata-kwata. Mamaki da tsoro suka risketa. Takai dubanta ga Bibah sai ta samu tana murmushi, hakan ya bata tabbacin itace tai komai. Wata irin wawuyar mikewa tai ta shaƙi Bibah, nan take kokawa ta kacame Bibah ta fara kakarin mutuwa. Da ƙyar Maheer ya rabasu shi da su Aunty Bintu.

    “Shareff idan baka saki Fadwa ba wlhy wlhy wlhy har abada babu ni babu kai. Yanzu nan ka saketa, dan baka taɓa rayuwa da wadda ta zubar maka ciki ba dan son zuciyarta, sannan ballagaza.”

   Shareff da gaba ɗaya brain da Heartbeat ɗinsa sun tsaya cak daga aiki, ya dago yana kallon Mommy.” “Ba kallona nace kayiba saketa nace, idan kuma bazaka saketaba to wlhy zan……”

   “Haba Nafisa kinada hankali kuwa, ki tsaya abi komai a sannu mana”.

  “Yaya daina wani maganar a sannu, ai tunda Ubansa ya sakeni wlhy shima sai ya saki Fadwa. Dan na tabbatar abinda na aikata bai kama kafar abinda taiba. Itafa ciki ta zubar masa”. Kafin ma Baba Ibrahim yace wani Shareff da dake cikin matsanancin fushi ya furta “Na saketa saki biyu”.

   Tamkar saukar aradu Fadwa taji saukar wannan kalma. Tai baya ta zube ƙasa, ihu take son yi amma ta kasa yi tsabar yanda falon ke juya mata tana ganib bibbiyu, da sauri ta rarrafa gaban Shareff.

   “Soulmate dan girman ALLAH ka saurareni, wlhy ba…..”

  Wani irin hankaɗata yay tai baya ta zube har kanta na buguwa da kujera sai da Abba ya tareta. “Wlhy idan kika sake koda matsoni zan iya shaƙeki ki mutu, ballagaza. ALLAH ya isa ban yafe miki zubarmin da ciki ba, na tsaneki, na tsaneki, bana buƙatar sake ganin mummunar fuskarki a rayuwata har abada. Idan har zaki iya salwantar da ƙyautar da ALLAH ya bamu, abinda ke amsa suna gudan jininki to zaki iya halakani nima, na tabbata zaki iya kasheni saboda cikar burinki. Kin wulaƙanta aure na, kin nunama duniya ke ɗin baki da tarbiya, har wasu banzaye najin wani abu akanki saboda kin nuna musu ke ballagaza ce. Anya Fadwa kinada ilimin addini kuwa? Anya kin san darajar kanki kuwa? Anya kina tuna zaki mutu kuwa?, na godema ALLAH ma da ban haihu da ke ba, dan bana fatan ƴaƴana su taso su kalleki matsayin mahaifiya balle har halayenki su zama naso ga tasu rayuwar. ALLAH ya wadaran mace irinki mai tara ƙawaye da bata da ra’ayin kanta sai nasu, kije ƙawayen naki su cigaba da baki rayuwar da kike buƙata, kije, kije bana son ganinki wlhy”. Idanunsa har tara ƙwalla suke na tsananin ɓacin rai, Shareff nada kishi matuƙa akan duk abinda yakeji ya killace matsayin nashi. Yanzu haka yanajin kamar zuciyarsa zata tsage, babu abinda ke masa amsa kuwwa sai zantukan samarin ɗazun a kanta. Wata muguwar shaƙa ya kai mata jijiyoyin kansa na matuƙar tashi. “Fadwa na tsaneki, bazan yafe miki ba…..” da ƙyar su Abie suka ƙwace Fadwa a hanunsa, sai numfashi take fiddawa da ƙyar na wahala ga Gwaggo Halima na ihu da kururuwar kuka zai kashe mata yarinya. Kansa ya kife a jikin Abie dake kusa da shi, yana mai ƙoƙarin danne hawayensa. Abie ya shiga shafa kan nasa cikin lallashi tausayinsa na ratsashi. Ba Abie kaɗai ba kowama yaji tausayin Shareff ɗin dan abune mai matuƙar ciwo ga duk namijin daya san ciwon kasa. Su kansu sunajin raɗaɗi a zukatansu matsayin iyaye, mahaifinta kam ma ai ya kasa ko motsi dan gaba ɗaya ya tattara laifin a kansa shima, zuciyarsa suka take matuƙa a ƙirjinsa………..”

   “Tabbs da ace kayi haƙuri saki bashi bane mafita Yaya MM”.

  Kusan gaba ɗaya suka waiwaya a inda sautin maganar ta fito. Anaam ce sanye da hijjab har ƙasa. a kallo ɗaya zaka fahimci a barci ta tashi ma. Kuma yanayinta yana nuni da batajin daɗi….

   “Ke kuma a wa, kajimin ƴar iskar yarinya. To ko ubanki Usman da uwarku basu isaba balle ke haihuwar yau”.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button