BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 77

   “Badan na isa bane na faɗa Mommy, ba kuma dan iyayena nada wani kusanci da zama masu isa a wannan Family ɗin ba. Sai dan kusan gaskiya ku daina dukan jaki kuna barin taiki (ALLAH yasa na faɗi hausar tawa dai-dai). Tabbas Fadwa bata taɓa ƙaunataba. Kamar yanda Gwaggo Halima bata taɓa ƙaunar iyayena guda uku ba. Haka kema baki taɓa ƙaunarsu ba. Kafin wata rana ina ganin laifinku matuƙa ina kuma jin zafinku mai tsanani, sai dai lokaci ya saukaƙamun hakan sakamakon fahimtar kuma a haka aka raini zukatanku. Zan faɗi gaskiyane a yanzu ma badan ku soni ni da iyayena ba, sai dan ku sani wadda ta raineku ku kanku ba ƙaunarku take ba bawai iyayena ne kawai take ƙi ɗinba. Lallai da sanin Fadwa aka zubar da cikin jikinta, sai dai kuma Gwaggo itace ta tsara komai da taimakon momyn Bibah, su Bibah ƙawayenta su huɗu suka ɗarata a hanya har komai ya faru…..”

   Wani irin harziƙowa Hajiya Luba tayi, amma sai Baba Ibrahim ya dakata mata wata irin razananniyar tsawa. Komawa tai ta zauna daɓar. Anaam tai murmushi mai ciwo da dafe karfen benen takai zaune saboda jiri da take gani. Sai da ta ɗan dafe kanta na wasu sakkani sannan ta ɗago tana ɗan murmushi. “Kuyi haƙuri.” Batare data jira cewar wani ba ta cigaba da faɗin, “Ban faɗa muku wannan maganarba sai dana riƙe hujja, kuma dama irin wannan ranar nake jira dan nasa duk yanda Maman Bibah da Bibah zasuyi da Gwaggo sai sunyi domin Yaya MM ya auri Bibah, kuma Fadwa itace kawai makaminsu da Mommy”. Ta ƙara maganar da miƙa wayarta dan bazata iya tasowa ba saboda jiri. “Gashi komai na’a cikin nan. Ku kira Amrah ma kuji dan tasan abubuwa da yawa itama”.

   Aunty Bintu ce ta amso wayar, ta kaima Baba Ibrahim. Gwaggo ta miƙe a fusace sai dai jikinta rawa yake. Amma sai Gwaggo Halima tasa ƙafa ta taɗota ta koma zaune daɓar har tana sakin ƙarar azaba data ratsa ɗuwawunta. Sosai da mamaki mai cike da ɗunbin razani suka bayyana a fuskokinsu Baba Ibrahim. Dan kuwa dai ga muryar Gwaggo gata Hajiya Luba da Bibah. Su Mommy zasu fara hayaniya Baba Ibrahim ya hanasu, cikin matuƙar razanarwa Baba Ibrahim yace Hajiya Luba ta faɗa kokuma ya ɗauka mataki a kanta. Jikinta tsuma yakeyi, musamman da taga irin mugun kallon da Shareff ke jifanta da dashi, wanda ba ita kaɗai ba, hatta Gwaggo haɗiyar yawu take da ƙyar…

    “Wlhy Yaya mu ba laifinmu bane, kawai dai Bibah ce ke tsananin son Shareff, nayi-nayi Nafi ta fahimci abinda nake buƙata na mu haɗa aurensu taƙi, sai nunawa takeyi da Fadwa za’a haɗa. Har nayi zuciya da hakan sai dai Bibah ta shiga damuwa, shine nazoma Gwaggo da batun ko akwai yanda za’ayi, amma saita nunamin itama bata san zancenba. Ban gajiba muka cigaba da binta har akai auren Fadwa da Shareff, sai lokacinne ta fara saurarena, ta kuma tabbatar min idan har muka taimaka mata cikin Fadwa ya zube zatai duk yanda zatai dan auren Shareff da Bibah ya yuwu”.

   Salati falon ya ɗauka baki ɗaya, yayinda a lokaci guda Gwaggo Halima da Mommy suka kaima Gwaggo shaƙa, da ƙyar aka ɓanɓareta a hanunsu idanunta har sun firfito waje kamar na tsohon kwarto. Nan fa sabuwar hayaniya ta kaure har wani baijin zancen wani, dan Fadwa kam tuni ta turmushe Bibah tana jibga, itama uwarta Hajiya Luba ta turmushe Fadwan. Ƙurace sosai ta tashi a falon, wadda ta saka Anaam ji kamar duniyar na juya mata. Cikin sa’a Shareff ya hangota tana jujjuya kanta. Da sauri ya miƙe yay inda take, cak ya dauketa ya koma saman da ita tana faman jujjuya masa kanta, Mamie da itama ta hangosu tai saurin bin bayansa dan ita kam ma ba komai take fahimtaba a abinda ke faruwa a falon.

   Faɗa sosai ya kaure, duk yanda su Abba sukaso kwantar da abun ya gagara, dan tun anayi a falo har aka koma tsakar gida, kafin kice mi ƴan biki sun fara tururuwar shigowa bama idonsu abinci tunda dama akwai ƙofar dake a tsakanin gidajen wadda basai kaje gate ba. Cirko-cirko mutane sukai sunajin fallasa da tonon asirin da su Mommy sukema juna, yayinda Gwaggo ke neman naɗe tabarmar kunya da hauka. Sai dai fa ganin lamarin yafi ƙarfinta dan hatta Mommy yau la’antarta take ga ƴan biki sai ta nema fita a gidan tana kuka wai su Daddy sun shirya wulaƙantata. Nanfa wasu a munafukai masu son jin ba’asi suka take mata baya, sai dai taƙi sauraren kowa, tana gab da barin layin nasu wani mai mota ya shawo kwana, duk da horn da yakeyi sam Gwaggo daketa faman sambatu da surutai batajisa ba, shi kuma ALLAH ya hanashi damar taka birki, ya kwasheta sama ya direma kasa, yana son riƙe kan motar ina saida taya ɗaya ta dirza ƙafar Gwaggo har ana iya jin karar farfashewar ƙashi. Tun ƙarar azaba ta farko data saki bata sake fahimtar ina take ba ta suma. Dan danan aka rufu kanta, har su Daddy labari yazo musu sun fito, nan fa layin ya cika dankam. Matasa zasu rufu kan mai mota da ƴan biki yazo dauka baba Ibrahim ya dakatar da su. Kamalarsa da dattakon kasancewarsa tsohon arziƙi ya sakasu bin umarni, sai dai an kama Gwaggo da babu alamar numfashi a jikinta an saka a motar mutumin aka nufi asibiti.

    Babu ko tausayi a fuskar Gwaggo Halima, sai ma faffaɗar magana take wai ai ƙarshen Gwaggo kenan. ALLAH ma ya kara sakata a masifa fiye da hakan. Mafi yawan mutane maganganun Gwaggo haliman basu ɓata ransu ba, sai dai duk da mugun halinta baban Fadwa ya kasa haƙuri shima a wajen ya yanke igiyar auren Gwaggo halima biyu. Ai sai lokacin Fadwa da Mommy suka sake tunawa da mutuwar nasu auren fa suma. Nan guri ya kara daukar zafi faɗa ya dawo sabo fil da ƴar koke-koke abin zakkunya da takaici………..✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button