BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 79

79*

……….Yanda Fadwa ke jigatuwa a gidansu haka Mommy ke jigatuwa a gidan Baba Ibrahim, dan kuwa matansa babu kanwar lasa a ciki. Basa raga mata koda da wasa. Abinci kuwa iya abinda suka bata shine zataci, bata isa cewa tak ba Baba Ibrahim zai silleta tass. Kaf ƴaƴanta an hanasu raɓarta har su Shareff kuwa. Itama duk ta fige ta ruɗe da damuwa mai tsanani, ga rashin aure, ga rashin ƴaƴa, ga dukiyar ɗan da take taƙama dashi ashe ta maƙiyintace. Kai ina itako zata saka kanta taji sanyi wannan rayuwa haka.

       Gwaggo Halima kam ai zamu iya cewa ta susuce a wannan gaɓar. Dan kuwa maganar auren mijin nata ya risketa dan abune da aketa faman watsasa a gidajen talabijin da rediyoyi. Bikine ake shiryawa na hamshaƙai biyu masu daidaiton ƙwarya tabi ƙwarya. Ga rashin ƴayanta tare da ita, dan kuwa itama dai su Abba sun ƙwace wayoyinta, sun kuma kafa mata sharadin inhar tana buƙatar zama da su sai ta nutsu, inba hakaba zata bar musu gida, dan yanda sukayi haƙuri da ita a baya a yanzu kam bazasuyi ba.

     Kwanan su Sima takwas a police station aka shiga kotu, dan duk magiya da roƙo da iyayensu ke ma Shareff ya rantse sai sunyi shari’a. Kasancewar laifinsu a bayyane yake ba’awani wahalar da shari’a ba a zama biyu kacal aka yanke musu hukuncin zama gidan yari na watanni goma shaɗa. Tare da tara mai tsoka. Kafin kace mi media ta ɗauka, babu abinda ke trending kamar labarinsu. Manyan yaran da akeji dasu a tiktok da istagram dama mafi yawan kafafen yanar ta gizo sunsha ɗauri a dalilin shugabarsu. Ga labarin mutuwar auren Fadwa ya zama kamar wani abin izgili a bakunan wanda suke jin haushinta. Sai dai wasu hakan ya sanyaya musu jiki matuka. Dan inhar haka zata kasance ga Fadwa suma ɗin basu tsiraba kenan tunda duk iri aiki guda sukeyi, wasu ma nasu yafi nata muni matuƙa. A take wasu suka fara goge wasu videos na rashin tarbiyya dake a shafukansu, wanda kuwa ke kai musu ji suke yanzu aka fara wasan ma. (Ya rabbi ka shirya mana zuriya damu baki ɗaya????????????)

Kwanan Anaam goma sha biyar a gidan Shareff ya dauka matarsa suka koma gidansu, dan ta ɗanji daɗin jikinta. Sai dai an sama mata mai aiki tare kuma da Aysha suka koma can dan itama tana cikin kunci da damuwa abin tausayi, dan ma Anaam ɗin na tsaye a kanta wajen ganin ta sakama ranta salama da daukar komai matsayin jarabawa.. Komawarsu gidansu da sati guda su Abie suka koma, dan Abie yayi iya koƙarinsa na ganin komai ya daidaita amma hakan yaci tura, ya zube kuɗi masu tsoka na kula da Gwaggo a asibiti ya tattara iyalansa da su Aunty Mimi suka koma Malaysia, inda suka bar Anaam na faman kuka sai da Shareff yayta lallashi…

★★★

     Zuwa yanzu abubuwa da yawa sun ɗan lafa ba kamar da ba, Anaam da Shareff sun buɗe sabon babin soyayya mai tsayawa a rai, mantawa suke da kowa da komai suna kallon kansu tamkar su kaɗaine a faɗin duniyar kawai. Tun Aysha da mai aiki najin kunya har da suka saba da gani. Dan kuwa dai tare da Shareff ake rainon cikin Anaam ɗin. Tana da sauƙin laulayi, abinda kawai bata so hayaniya. Inhar waje ya cika hayaniya yanzu zata jangwaɓe babu lafiya. Hakan yasa babu inda take zuwa sai bayan sati uku zuwa huɗu ya kaita can gidansu ta yini. Gaba ɗaya ya tattara lamarin Fadwa ya ajiye a gefe. Ko tunawa da ita ma baya sonyi balle jin sunanta. A dalilin ta yay ma tiktok tsana mai tsanani, dan zuciyarsa na ayyana masa duk wanda ke a wajen mutumin banza ne irinta. (Sai da Shareff da sauran ƴan uwa ba haka bane. A yanda muke kallon tiktok ba hakan bane. Shima dai dandaline tamkar kowane dandali na media. akwai na ƙwarai akwai bara gurbi. Kawai dai a komai bara gurbi sun fi saurin yin shura a idon al’ummarmu ne da yaɗuwa. Kuma ita yanar gizo tamkar kasuwa take, abinda kai niyyar shiga ka saya shine zaka nema kuma ka samu. Dan haka tiktok akwai mutanen kirki a cikinsa masu yaɗa abubuwan alkairi saɓanin tunaninmu na musu kuɗin goro. Fatanmu matan aure irinsu Fadwa da suka tsunduma rayuwarsu a waɗannan hanyoyu ALLAH ya shiryesu. Hakama ƴammatanmu da basuyi aurenba ALLAH ya shiryesu ya basu mazaje na gari, hakama zawarawa da samarinmu baki ɗaya).

     Watanni kusan huɗu da faruwar komai aka sake ɗaura auren Aysha da Dr Jamal, sai dai su Abie basu zoba sun dai saka albarka. Hakama Daddy ya haramtawa dangin Mommy zuwa bikin har ita kanta Mommy din. Tako ci kuka mai zafafa zuciya, har tanajin inama bata biyema Gwaggo ba da ayanzu haka tana nan an dawo da ita gida. Sai dai kasancewar babu inda zata zauna a gidan baba Ibrahim aka haɗasu ɗaki ɗaya da Mommy. Ko kallonta Mommy batayi, balle ta taimaketa koda da bada magani ne. Kullum cikin mata ALLAH ya isa takeyi. Kaf dangi an rasa mai jinyarta, dan kuwa dai ƙafarta da gaske ta ruɓe, a yanzu hakama ana shirin gundile har cinyar data ragene saboda imfection ya shiga.
       
     Zuwa yanzu cikin Anaam watanni bakwai ne ciff, hakama matar Maheer an gamu, dan shima dai ya kwantar da hankalinsa zuwa yanzu ya rungumi matarsa. Matar Khaleel ma dai nada cikinta ɗan wattani uku. Haka amaren suka cigaba da rainon ciki musamman Anaam dake a gaɓar gangara. Shareff dai na shan shagwaɓa matuƙa. Dan kuwa kun san mutuniyar taku da raki. Ga kuma cikin daya fara tsufa yana yawan sakata a saurin fushi, hatta da mai aikinta taka tsantsan takeyi. kullum cikin rigimar ita a Malaysia zata haihu take. Su Abie da Shareff nata lallashinta, acewarsu suma sun kusa dawowa Nigeria. Haka dai akaita rarrafawa har ALLAH yasa aka shiga watan haihuwa da ƙyar. Dole fa badan yaso ba Anaam ɗin ta koma gaban Mom ta cikagaba da kula da ita ana jiran naƙuda. Shareff ma sai ya haɗa kayansa ya koma can gidan shima. Dan kuwa dai nan ɗin ya masa daɗi shi kaɗai, yana matuƙar jin kewar ƴar darun tasa.
      A daren wani alhamis ta farka da naƙuda mai tsanani, babu shiri suka nufi asibiti a daren. Sai dai fa tun ana jiran haihuwa har al’amarin yaci tura aka yanke shawarar za’a mata cs kamar yanda Dr Bilkisu ta basu shawara, dan ta tabbatar musu jikin Anaam baida ƙwari za’a iya zamun matsala gaskiya. Dole Daddy ne ya saka hannu da Shareff kwata-kwata baya a hayyacinsa. Yana can maƙale da Anaam tana kuka yana rungume da ita. Anyi-anyi ya bar ɗakin haihuwar amma yaƙi, dan shi gani yake daya gusa zai iya rasata.
    Alhamdulillahi zuwa ƙarfe ɗayan rana aka samu nasarar zaro mata ƴar babynta mai kama da ita kamar tayi kaki ta ajiye. Kowa na murnar ɗaukar Baby shi baban baby hankalinsa nakan uwar baby. Dan bai samu nutsuwar ganin ƴar tasa ba sai da aka miƙa Anaam ɗakin hutawa, ya tabbatar ta ambaci sunansa cikin mayen barci sannan ya samu nutsuwa. Cikin ƙanƙanin lokaci hoton babby ya zagaye dangi har ƴan malaysia, zo kaga murna wajen Abie da Mamie tamkar zuyi tsuntsuwa su ganzu a 9ja kawai. Dangi tako ina shigowa suke asibitin, harda dangin Mommy waɗanda ma ba’ai zaton gani ba.
        Shareff dai na nane da natarsa harta farka, ya rungumeta yana mai sanya mata albarka da tarin godiya. Bata da ƙarfin rungumarsa. Amma tana maijin daɗin addu’oin da yaketa zuba mata da albarka. Ya sumbaci lips ɗinta suna mai kallon juna da murmushi. Ƴar babyn ya ɗakko saitin fuskarta yana nuna mata, ta kai hanunta saman kan yarinyar a hankali ta shafa, tare da sumbatar goshinta hawaye na silalo mata. Ita Anaam itace da baby a hannu mallakinta, ita kaɗai iyayenta suka haifa babu wa babu ƙani, yau sai gata da gudan jininta kuma. A hankali ta furta “I love you Yaya MM”. Cak ya tsaya daga sumbatar babyn da yakeyi, ya tsura mata idanunsa da ke nuna tsantsar rauni da jin kalmar a bazata. Tunda suke tare bata taɓa furta masa ba. Kai duk soyayyar da yake ambata yana mata bata taɓa nuna ta damu ba balle ta karɓa masa. Tana dai ƙyautata masa da kuma shagala a tare da shi a duk sanda shi yake jadada tasa soyayyar a gareta harta bada gudunmawar maida murtani….
      “Dan ALLAH ki maimaita Noorie, danna tabbatar ba mafarki nake ba”.
    “Ba mafarki kake ba Yaya MM. kanwarka na tsananin ƙaunarka, kamar yanda ka rayu da sonta haka itama ta girma da soyayyarka, sai dai wani nauyayan dalilai sun matuƙar ɓoye hakan a zahiri. Kai kaɗai zuciyata ta taɓa so Yaya Al-Mustapha, bayan kai kuma bazan taɓa son wani ba, ina fatan na zame maka mata har a gidan aljanna. ALLAH yasa mu mutu tare…”
     Ta ƙare maganar hawaye na ziraro mata. Hanunsa dana baby da batasan sunaiba tanata baircinta ya haɗa waje guda ya share mata hawaye. sannan ya rungumeta yana mai jera mata tari-tarin kwandunan godiya marasa adadi, tare da sake jadada mata ɗunbin ƙaunarta dake ratsa jininsa da ɓarko a kowanne bugawar cikar sautin sakan na agogo, “Na gode da waɗan nan kalami masu tsada tsadar tsada. Kece mace ɗaya tilo dana fara so, bazan taɓa iya jera sonki dana wata ba har abada.”
       A hankali Fadwa dake tsaye bakin ƙofa taja hanun ƙanwarta suka koma da baya. Dama Daddynsu ne yazo da su suyi barka su kuma duba Anaam ɗin. Shi yana can tare da su Daddy a waje akace su su shigo, shine tai gamo da wannan al’amari. Kuka take rurus zuciyarta na mata raɗaɗi da zafi, tasan ko iya haka aka tsaya Anaam tayi winning a kanta. Shareff kuma ya mata nisa, nisan irin wanda sama kema ƙasa. Duk wanda ya ganta dole ya tausaya mata, dan tana a cikin tsananin ciwo na so da har ya haifar mata da ciwo a zuciya. Tana tsananin son Shareff har bata san iyaka ba. A ƙarshe wannan rana sai a asibiti ta kwana magashiyyan.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button