BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 82

gazawarsu koka aibanta waɗan nan yaran, akwai ƙaddara amma wasu lokutan akwai sakaci sosai na iyaye. Karka matsawa ɗanka, kar kuma ka sakesa da yawa. Dan matsi na saka lalacewa tunda zai koma a tafin

hanun neman sharar ƙawaye ko abokai ne, sannan saki gaba ɗaya ma kuskurene, zai koma a tafin hanunun tarbiyyar ƙawaye ko abokai. A wannan zamanin iyaye sun kashi kaso uku ne zuwa huɗu koma nace biyar ko fiye da haka, masu raunin talauci da komai yaron yayi dan an sakar masa komai ne. (Kamar

dai su Sima da Amaal) kaso na biyu rashin wayewar kan sanin mi yaran ke aikatawa ma ko ilimin sanin illar wayoyin ko yanar gizo. Kaso na uku ƴan boko wayayyu da komai akai su a wajensu ba komai bane zamanine. Kaso na huɗu masu tsananin tsaurarawa har ƴayan suna fakar ido suna aikata abinda sukema tsaurin. Kaso na biyar ƴan fifita aiki ko kasuwanci fiye da saka ido akan al’amuran ƴaƴansu komai na hanu

n ƴan aiki kosu yaran a karan kansu. Iyaye mata suna ƙoƙari matuƙa, duk da a wani ɓangaren akwai sakacinsu, sai dai kuma laifin iyaye maza yafi rinjaye. Da yawa ƴaƴa suna matuƙar shakkar iyayensu maza fiye da matan, sannan a wani fanin iyaye mata nada rauni akan ƴaƴa, dan haka idan kana son ingantuwar tarbiyyar ɗanka yanda ya kamata dolene a matsayinka na uba kaima ka tsaya tsayin daka wajen taimakawa uwa mace ku gyara kuma ku tsawatar, sannan ku haɗa da addu’a. A wani fanin Gwaggo halima tayi matuƙar ƙoƙari wajen tarbiyyar su Fadwa, domin kuwa bata barsu kara zube ba akan wasu fanonin, hakan zaisa mai karatu ya fahimci itafa uwa uwace koyaya take tana buƙatar ganin ɗanta a ƙyaƙyƙyawar

nasara bawai faɗuwa ba. Su Fadwa na tsoron mahaifinsu, amma maida hankalinsa a kan hidimarsa da siyasarsa yasa bai maida hankali wajen sanin dukkan motsinsu ba, shi dai kawai idan ya samo ya basu sunci sun sha sun samu komai basu da matsala ya gama nashi. Ba mahaifin Fadwa kawai bane a irin wannan halin, mazanmu na yanzu musamman yarena hausa dana sani wannan shine babban rauninsu akan ƴaƴansu gaskiya. Namiji ya fita tun safe sai dare ko yamma zai dawo miki, komai ya sakar miki akan tarbiyyar yara, masu ƙoƙarin ciki sune ke ɗan zama da yaran weekend, wanima da sun raɓesa zai korasu shi an takura masa yana son ya huta, ko wani ya ɓato masa rai a waje ya shigo gidan yayta tambotsai. Komai sai uwa dai, tayaya uwa zata iya da komai? musamman akan yaran yanzu da sai dai addu’a. Abu

mafi girma shine maida nauyin gidajenmu a hanun ƴaƴanmu musamman ga iyayenmu talakawa. Taya zakice yarinya budurwa baliga ko bazawara itace zata nema kuɗi ta ɗauka nauyin rayuwar gida? Ko namijine a wannan zamanin dole ka kasance cikin taka tsantsan balle mace, anji neman nakai nada daɗi, amma komi ƴarka zatai tayi a gaban idonka, bisa control naka kona yayunta domin ceto rayuwarta daga faɗawa wata ƙazamar rayuwa. Tabbas wasu iyayen basu san ƴaƴansu na abubuwan nan a media ba, saboda su basu da wayewar kan sanin mima wayoyin suka ƙunsa ko yanar gizo, wasu kuma masu wayewar hakan basu cika zama masu bin ƙwaƙwƙwafin yaran nasu ba. A ganina hakan duk kuskure ne, akwai abinda baida ƙyau ka cika masa bin ƙwaƙwƙwafi kam, akwai kuma wanda saida bin ƙwaƙwƙwafin komai zai tafi dai-dai. Karmu hana yaranmu wayoyi, kar kuma mu barsu da su su zame musu komai. Idan baku da wayewar kai akan waya samu wasu da zasu dinga bibiyar yarinyarki a kowane shafi nata/nashi suna kawo miki rahoto, idan kunada ilimin bibiya a kowanne dare wayar yaranki musamman mata ko matasan samari masu tasowa dan nasan na manyan gwasaken zaiyi wuya ta kwana a hanunki, dan dare shine mafi girman fili dake basu damar aikata komai a yanar gizo. Sannan ki dage da addu’a da yawaita nasiha mai tsoratarwa ga yaran akan irin waɗan nan abubuwan. Mu kammu iyaye mata da muke shiga a irin waɗan nan abubuwan dan ALLAH muyima kammu faɗa mana, kina tunanin zakiyi ƴaƴanki su kasa koyi dake? Shifa hali naso yakeyi, Fadwa ta fara tiktok tun bata da aure, amma saboda ya zame mata jiki har taje gidan aure tanayi a duk yanda taso. Wlhy wlhy maza da yawa na faɗawa a tarkon sha’awa a kalle-kallen videos na yanar gizo da mata ke yaɗawa a duk shigar da suka gadama. Karku manta wanifa abu kaɗan ke tada masa hankali, shiyyasa zinace-zinace sukai yawa yanzu muka rasa gane daga inane, ada yarinya saita ɓalle daga gida ta shiga duniya ake kiranta karuwa, wlhy yanzu a gabanki za’a maida miki yarinya karuwa ko matarka ko ƙanwarka ko yayarka????, dan wasu matan a dalilin abinda sukeyi wasu mazan ke hillatarsu harsu bata musu rayuwa. Duk yanda mace take tana son a yaba mata, shiyyasa maza mayaudara ke saurin samun galaba akan ɗiya mace saboda su duk hanyar yabo da gwarzantawa sukebi, suna kuma samun abinda suke so su watsar dake su koma gefe suna zagin iyayenki dake kanki matsayin mara tarbiyya. To hakane ke faruwa a duniyar tiktok dama sauran kafafen sada zumunta, waɗan nan masu zugaki a Comments kin haɗu, kin isa, kin kai, wlhy ba ƙaunarki suke ba, dan daza’ace ɗaya daga ciki ya fito ya aureki sai kin nemesu kin rasa sun gudu. Maza dake kawo matansu ana video su wai soyayya ban taɓa ganin waɗanda basu san ciwon kansuba irinsu wlhy, matarka ta aure sirrinka itace kuma abin ado a shafin sada zumunta?, anya wannan soyayya ce kuwa ta gaskiya? Muji tsoron ALLAH, mu dunga tunawa da mutuwa, mu dinga tunawa akwai kwanciyar kabari, akwai hisabi, dubinki sunyi amma basuci ribaba, tayaya ke kike tunanin zaki ribantu?, bazaku gane illar abinda kukeyiba sai kinje gidan aure namiji na miki kallon zargi ko yana bin irin hanyar daya ganoki wajen gani wasu matan duk da yana dake a gidansa. Ki dauka abu mai amfani ki yaɗa sai kici riba, amma mummuna zakiyi bayani idan baki tubaba. Dan Fadwa a novel ta fito shiyyasa wani a cikin hukuncunta yazo a bayyane, amma ke a zahiri kike ALLAH shine zai hukuntaki idan baki tuba kin koma garesaba, ba kuma kisan ta hanyar dazai hukuntakin ba ma. ALLAH ka shiryemu badan halinmu ba.????????????

Shima Daddy koda ya amsa maganar dai ɗaya ce akan zuminci da tarbiyyar ƴaƴanmu. Mu daina sakarma abokai ko ƙawaye ƴaƴayenmu hakan kuskurene. Dan zai zama kina tufƙa wasu na warware miki, yanzu lalacewa basai a zahirin rayuwa ba. Daga budurwa har bazawara da saurayi ko magidanci ko matar aure inhar suna biyema ƙawaye ko abokai zama samu rayuwarsa tana tangal-tangal, dan zai koma ne baida ra’ayin kansa sai nasu, hakan kuma babban kuskure ne………✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button