BABU SO HAUSA NOVELNOVELS

BABU SO CHAPTER 2

Tuni yana kudancin ƙasar sai ya gadama yake waiwayen kano tun daga karatu, su kansu ƴan uwan ba’a komai suke sakashi a lissafinsu ba. Rasuwar ma baizo ba sai bayan kwana bakwai duk da mahaifiyarsu ce. Kamar yanda ƴan uwansa suka gabatar masa iyalansu shima haka ya gabatar da tasa matar a garesu. Ƙyaƙyƙyawar bafulatana mai tarin ilimin zamani dana addini. Ga tarbiyya da mutunta mutane.


     Babu laifin zaune babu na tsaye Mommy ta tsinci kanta da tsanar Humairah wanda babu makawa kishine kawai da hassada ke cin ranta, dan kuwa ko ba’a faɗaba Humairah ta fisu komai na rayuwa. Kasa biye ƙiyayyarta tai ta dinga nunata ga Humairah datai kamarma bata fahimta ba, dan mace ce data iya zama da mutane matuƙa, sai dai koda wasa taƙi bada fuskar da Mommy ɗin zata kawo mata raini.


     Rasuwar Mama yasaka baƙin halin Gwaggo fitowa muraran gasu Muhammad. Dan kuwa sun fahimci Gwaggo itace ke tunzura mahaifiyarsu aikata wasu abubuwan ashe. Duk da tana nuna itace uwa a garesu kamar da can, a yanzu hakan baya hana ta nuna musu bata haifesu ba ko wani abu makamancin haka. Sannan a kullum burinta taga babu zaman lafiya tsakaninsu da ƴan uwansu biyu kacal da ALLAH ya basu, kai hatta lalacewar Umar sun fahimci Gwaggo nada kamasho dan kuwa dai shi da Muhammad sune ƴan ɗakinta, a yanzu kuma Shareff ma a hanunta yake yaron gaba ɗaya ya tashi a taɓare ga rashin kunya da rashin mutunci. A kullum cikin jibgar ƴaƴan anguwa yake da musu ƙwacen abu idan ya gani gashi baya son karatu sam.
      Abubakar da yaran gidan suke kira da Abbah ne ya fara nusar da Yayan nasa Muhammad da suke kira Daddy abinda ke shirin faruwa, yana tsoron su sake samun bara gurbi bayan Umar a zuri’arsu. Sannan koba komai Shareff shine babba a ƴaƴansu lalacewarsa na nufin rugujewar sauran ƙanensa.

Sosai Daddy ya fahimci Abbah, suka zauna shawarar matakin da zasu ɗauka akan yaronsu duk da gida ɗaya suke da Gwaggon sashenta daban itama inda suke zaune da Mama kafin rasuwarta. Suna a wannan halin Usman yazo Nigeria domin fara ginin wani fili daya saya, a ganinsa ya ƙyautu ya mallaki muhalli a ƙasar haihuwarsa. Zuwansa ya musu daɗi, dan basu ɓoye masa komai game da halin da Shareff ke neman shiga ba a hanun Gwaggo.

Ya jimanta al’amarin tare da sanar musu subar komai a hanunsa shi zai ɗauke Shareff ɗin ya koma hanunsa insha ALLAH. Ba karamin farin ciki sukai ba, tare da ƙara ɗinkewa kamar komai bai faruba a baya. Ginin da yazo da niyyaryi a nesa da su sai suka hana hakan, suka tilastashi zuwa ya gina filin da suka rage masa tare da ƙara masa dana cikin gidansu kasancewar gidan nasu ƙatone sosai kowace mace ma da part ɗinta, ga kuma na Umar ma da babu kowa a ciki tunda yaki zama. Dan da farko ma na Umar ɗin sukace ya ɗauka yaƙi.
     Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara ginin daya tada hankalin Gwaggo da Mommy, babu kunya suka tada rigimar basu yarda ba. Su su Daddy ma abin har mamaki ya dinga basu, dan sun rasa dalilin Gwaggo na son nisantasu da ƴan uwansu. Basubi takanta ba, dan a lokacinma ne suka nuna mata bore, a wajen Halima kawai ta samu goyon baya dan ita dama sai a hankalice. Wannan rigima bata kwantaba kuma maganar komawar Shareff hanun Usman ta sake tasowa.

Nanma dai ansha ƙaramin yaƙi dan Mommy haukane kawai bataiba ɗanta zai koma hanun maƙiyanta. Tsiya ta dinga zazzagama Usman harda masa gorin haihuwa. Shi dai bai kulata ba kamar yanda bai kula Gwaggo da Halima ba. Iyakaci ma idan suna abun nasu sai dai yayi murmushi. A gefe kuma bai fasa shiryama Shareff tafiya ba.
         A lokacin da zasu wuce dole sai sace Shareff akai daga gidan batare da sanin Mommy da Gwaggo ba, dama ita Halima tana gidan aurentane zuwa takeyi, itama dai yaranta uku ne a yanzu tana auren ɗan wan gwaggon dan ita ta haɗa….

        Humairah da Mimi sunyi farin cikin ganin Shareff, sai dai kuma sam babu cikkakkiyar tarbiyya ga yaron. Dan ba ƙaramin wahala da azabarsa suka sha ba duk da kwata-kwata shekararsa tara ne a duniya lokacin. Haka Ruƙayya taita juriyar ganin ta sauya tarbiyyarsa ita da Usman.

Basubi takan zagi da walakancin da Mommy ke kira a waya ta musu ba akan su dawo mata da ɗanta idan sunji haushi su haifa nasu. Gorinta na musu ciwo, amma sukaita dannewa tunda sun san domin ALLAH zasuyi ai da ɗan uwansu. Tunda dai sun san bazatazo ta ƙwacesa ba.


       A hankali komai ya fara daidaita, Shareff ya fara nutsuwa da son karatu, ga kulawa yana samu da soyayya ga iyayen ruƙonsa. Shaƙuwa kuma mai nagarta ta gama shiga tsakaninsu. Bashi da kamar Abie da Mamie yanzu a duniya sai aunty Mimi da akoda yaushe yakanje gidanta kodan yaronta data haifa Su’ad. Shareff nada shekara biyar a wajensu ALLAH ya bama Mamie ciki.

Zokaga murna da farin ciki wajensu, yayinda Mommy ta shiga baƙin ciki dan taso ace sun ƙare rayuwarsu ne babu haihuwa. Kuma har yanzu tana kan caccakarsu akan su maido mata ɗanta. Sudai basa kulata, dan ko ƙasar zasuzo basa zuwa da shi ma.


       Mamie tasha rainon ciki har ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo ƴarta mace. Mommy da Gwaggo sun ɗanji sassauci dan a ganinsu darajar mace bata kai ta namiji ba. Dan haka suka shiga shigi da fici gidan malamai kai harma da bokaye akan wai a tsaida haihuwar Humairah. Humm abin dariya, dama basu wahal da kansu ba dan iya abinda ALLAH ya rubuto a ƙaddarar bawa shi kaɗaine rabon dazai samu ai dama.

Ita dai batama san sunai ba, dan kuwa da ALLAH ta dogara. Su Daddy ne kawai sukaje Malaysia ganin gudan jinin ɗan uwansu, duk da Gwaggo taso binsu ganin ƙwaf sukaƙi. Yarinya taci sunan Juwairiyya, mahaifiyar su Abie kenan amma suna mata alkunya da Anam (Blessings of GOD).

         Rainon Anam ya dawo kamar a hanun Shareff ne. Bashi da damuwa a yanzu sai ta Anam, daya dawo makaranta tana hanunsa, bacci ne kawai ke rabasu shima sai Mamie tayi jan ido. A haka aka yayeta ta buɗa ido da sanin Shareff matsayin Yayanta kawai. Dan kuwa duk wani gata da kulawarta tamkar ta koma hanunsa ne. Dan hatta wanka da abubuwan da uwa zatayi duk shike mata.

A koda yaushe tana maƙale da shi kamar cingam. Hatta da Abie wani lokacin ƙiwa take masa sai shareef. Lokacin da take cika shekara shidda a duniya a lokacin Shareff ya kammala secondary school ɗinsa. Abie yay masa shirin wucewa jami’a a ƙasar Indonesia. Ya shiga damuwar rabuwa da ƴar ƙanwarsa, dan kuka sosai ya dingayi duk da lokacin yanada shekaru sha takwas a duniya dan ya zama ɗan saurayi abinsa.

Haka dai babu yanda ya iya ya tattara ya tafi badan yaso ba. Yasha matuƙar wahalar kewar Anam a ƙasar Indonesia, dan da ƙyar ya haƙura ya maida hankali ga karatunsa kodan faranta ran Mamie da Abie ɗinsa. Fara karatun Shareff a ƙasar Indonesia ya ƙara bama Gwaggo da Mommy ƙwarin gwiwar cigaba da shiga da fita domin ganin hankalinsa ya dawo garesu, su kuma nisantashi dasu Mamie.

Zuwa lokacin gidan nasu ya ƙara haɓaka da ƴaƴa. ALLAH kuwa ya amsa musu, dan kuwa dai a hankali rayuwar Shareff da hankalinsa suka fara dawowa Nigeria, ko hutu ya samu da yaje Malaysia dake kusa da shi gara ya wuto Nigeria. Takai yakan ma jima bai je inda su Abie suke ba. Sai dai abinka ga ikon UBANGIJI har lokacin soyayyar bayin ALLAHn nan na’a ransa babu abinda ya canja.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button