GURBIN IDO

GURBIN IDO 10

10

      "Assalamu alaikum" ta furta kamar yadda yake a al'adarta duk sanda zata amsa waya,daga daya sashen muryarsa ta bayyana,cikin sanyi daya sanya annin ta shanshano wani abu daga gareshi tun kafin yace wani abu

“Barka da dare”

“Dare?,a garinku kenan” daga can sashen da yake sai daya dafe goshinsa,ba zata taba yarda ta karba yadda ya bata ba sai tayi challenging dinsa

“To barka da safiya shikenan?”

“Yanzu naji magana…..barkanmu kadai” dorawa yayi da

“Kun tashi lafiya,ya jama’ar gidan?”

“Alhamdulillah,lafiya qalau,jama’ar gida mun barsu a gida,mu mun danyo balaguro nan cikin adamawa”

“da wannan qafar anni?” Ya fada murya a kwance cikin nuna kulawa

“Eh,to ya za’ayi,duk inda Allah ya tsaga sai ka taka saika taka din kafin lokacin da takun naka zai qare”

“Hakane…..” Ya fada a taqaice

“Banji duriyar jafar ba” ta fada cikin zaquwa da son jin muryarsa,ajiyar zuciyar da taji jabir din ya sake sai da gabanta ya fadi

“Maganarshi na kira nayi miki anni” ya fada a sanyaye

“Menene kuma?” Ta tambayeshi gabanta yana faduwa

“Anni har yanzu dai…..har yanzun babu wani ci gaba anni,sai abubuwan sunyi kamar zasu gyaru sai su sake rikicewa”

“Kuma dai?” Ta fadi cikin tsantsar damuwa,kamar tana gabansa ya gyada kai

“Wallahi anni,yanzu haka tun jiya banga fuskarsa ba,nayi iya bakin qoqarina ma naga ya fito ko ruwan zafi ne ya sha idan ma bazaici abinci ba amma ko motsi yaqiyi bare ya bani alamar da zata gayamin yana raye lafiya lau”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” kalmar da taja hankalin yuuma,ta koma ta zauna daga shirin tashin da takeyi din,ta kuma kamawa daada sukakai salatin tare.

Sosai fuskar anni ta nuna alamun tashin hankali da kuma damuwa,wannan wata matsala ce data zama kusan jarrabawa cikin tata rayuwar,saidai a yadda Allah yayi mata komai a rayuwa,ya albarkaci zuri’arta,to ta dora hakan a matsayin jarrabawar da ubangiji kan yiwa kowanne bawa don ya gwada imaninsa

“Ka kira wayarsa?”

“Ya rufeta anni,yaqi bude wayar…..amma ki kwantar da hankalinki,koda bazaice komai zan sanar dashi daga bakin qofa,awa uku suka rage ya cika awa ashirin da hudu a dakin,idan har bai bude ba ya fito zan sanarma jami’an tsaro na qasar su shigo su balle qofar su dubamin shi,duk da jikina yana bani lafiya qalau yake,tunda fitilar dakinsa naga a kunne take tun jiyan kawo yau”

“Jabir…..duk yadda zakayi ka tabbata kayi ya fito haka a dakin nan,na gaji da zamanku a wannan qasar jabir,bana jin zan barku kuci gaba da zama kamar yadda kukeso”

“Kada ki damu anni”

“Ka kula dashi don Allah,duk abinda ake ciki ka shaidamin,kada ka yarda da maganar babanku kan kada a gayamin komai,ni hakan shine kwanciyar hankali na”

“In sha Allah,i will do my best anni”

       Jikinta a matuqar sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta ta ajjiyeta a gefanta,sai ta hade hannayenta waje guda

“Ya Allah…..mun tuba Allah,Allah ka kawo mana qarshen wannan matsalar,wannan damuwa Allah ka yanke mana ita gaba daya,ubangiji ka aiko mana da HASKE”

“Ameen……lafiya kuwa anni?” Yuuma ta tambayi annin cikin matuqar kulawa da kuma damuwa,saboda ta fuskanci koma wacce irin matsala ce lallai ba qarama bace a wajen annin

“Jafar ramatu,har yanzu jafar ya kasa komawa kamar kowanne irin mutum,jafar ba jahili bane….amma bansan me yasa ya kasa yarda da qaddararsa ba,gaba daya rayuwar jafar ba ita bace a yanzu,wani jafar ne na daban da dukka muke kallon an sauya mana shi,tsahon shekara uku amma komai ya kasa wucewa?”

“Jafar dai anni?” Yuuma ta tambaya tana dubanta,kai ta jinjina

“Shi…..tun daga shaheeda da amra suka rasu,bamu sake gane kan ja’afar ba,babu irin roqon Allahn da ba’ayi masa ba,ana kan yi masa ma,ba irin nasiha jan hankali da ban bakin da jafar bai samu ba,ba za’ace babu sauqi ba sam,saidai tashi danganar data zo sai tazo wani iri,duk da cewa dama miskili ne mara son magana me kuma bau dadden hali…..amma hakan baisa rayuwa ta naqasa tako ina ba,yana rayuwarsa kamar kowa,yana kuma yin dukkan wani abu daya dace da mutum kamarsa zaiyi,amma tun bayan nan jafar gaba daya ba shine tare damu ba,sai abun yayi kamar zai dai daita,sai ya sake dilmiya cikin damuwa me zurfi,na dauka zaman gidansa ke sake dagula masa lissafi……sai nasa ya tattaro ya dawo cikin gida,duk da haka babu wani canji,sai na sake tunanin kodai zaman kadaici ne?,tunda a baya shi din me aure ne?,na shiga nema masa yarinyar da zata dace dashi,ta kuma kula dashi……amma abun takaicin,wallahi ramatu yadda kikasan nayi busa a iska,baisan ma anayi ba,wannan yasa duka yaran suke kasa daurewa,saboda kowacce tana tsammanin samun kulawa da soyayya daga gareshi,to duka babu ko daya da suke samu,abinda yake sanyasu sarewa kenan,su kuma ce sun haqura……ba tare da sun duba cewa a yanzun shi din tamkar mara lafiya yake ba,zuciya da qwaqwalwarsa na buqatar magani ta hanyar mu’amalantarsa da dawowa dashi ya dawo ja’afar na asali……sannan koma meye sai ya biyo baya…..karo hudu kenan,amma dukkaninsu sun gaza daurewa zama dashi…….abinda ya bani mamaki da tsoro,yasa kuma na saare shine,wadda na nema masa a karo na shida ‘yar uwarsa ce,a yadda abun ya dauko naji dadi.matuqa,saboda ina hangen haske da kuma waraka,don yadda yarinyar ta jajirce,ashe akwai mummunar manufa a ranta,dukiyarsa take hange,Allah ya toni asirinta,na gano na kuma watsa tafiyar,tunda dama shi wanda ake dominsa baima san inayi ba” shuru anni tayi tana maida numfashi,abun yana matuqar damunta da zuciya,a yanzu duk duniya zata iya cewa bata da matsala sama da wannan.

“Iyaka nazari da hangena,babu wata hanya da zamu samu yadda mukeso sai ja’afar ya haqura yayi aure,saboda jabir bazai taba dawwama tare dashi ba,shima mutum ne,aure zaiyi,don maganar da ake yanzun,watanni kadan suka rage akai masa kudi da sa rana,yau idan jabir ya tafi,shikenan haka zamu zuba idanu muna kallon rayuwar jafar ta dulmiya ta nutse a gaban idanuwanmu?” Kai yuuma ke girgizawa,tsahon wasu mintuna shuru ya baqunci dakin,kafin yuuma ta saki ajiyar zuciya

“Maganarki gaskiya ce anni,hanya daya ce tak ta fitar da ja’afar daga yanayin da yake ciki,hanyar kuwa itace,a sama masa mace mai tsananin sonsa,so fisabillahi saboda Allah,jajirtacciya da zata iya kasancewa koda yaushe tare dashi,mai juriya da zata iya daukan dawainiyarsa…..komai nisan zangon da zasu samu dashi kafin a cimma gaci….”

“Wannan shine abunda muka kasa samu har yanzu” anni ta katsi numfashin yuuma,gyara zama yuuman tayi

“A nawa tunanin kaf cikin matan da kuke nema masan,kuna sama masa ne irin matan can wajejenku,wadanda idanunsu ke a bude,suke ganin cewa ‘yantattun mata ne su,wadanda zasu shiga gidan aure ne da dukka iko da isa irin wadda d’a namiji ke da ita,ba bautar aure zasuyi ba,zama ne na ‘yanci da cin gashin kai” shuru ne ya sake ratsa dakin,sai hayaniya daga jama’ar dake karakainarsu daga waje jifa jifa tana ratsasu.

Sosai maganar yuuma ta ratsa anni,ta kuma sanyata zama ta dinga wareta daya bayan daya tana nazarinta,lallai yuuman tayi wani dogon nazari da kuma tsinkaye,wanda ita kanta bata yishi ba tsahon lokacin da aka dauka matsalolin suna faruwa.

Kusan rarrabuwa hankalin anni yayi kashi kashi,tana sauraren kira daga khalid,tana kuma ci gaba da nazarin maganar yuuma,tare da tunanin inda zata kamo bakin zaren,ta damu da ja’afar matuqa,tana kuma shiga damuwa ainun game da lamarinsa.

Sam hankalin anni bai kwanta ba har sai data samu tabbacin lafiya lau daga bakin jabir

“Ka bani shi jabir zamuyi magana” kai jabir din ya girgiza yana duban bakin qofar dakin da yake zaune a yanzu daura da ita,kamar wanda aka bawa gadin wajen

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button