BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 1 to 10

Juyawa ya yi da sauri yana mamakin Kaf yayansa idan ya yi magana a da jiki na bari suke aikata abinda yake so aman kwanakin nan yana haduwa da hari kala kala da wajaje daban daban a cikin yayansa bale Mariama yarinyar na da zuciya  ……..

      Labari bak’a ce labari ne kirkirare bisa lamarin da ba kirkirare ba, labarin yana tafiya ne bisa gaskiyar lamarin abinda ke faruwa , tabas na shiga kuma sai na fada……ku mu je zuwa a labarim bak’a ce in sha Allah

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na            *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        8⃣

Yana fita Bak’a ta cire daurin dake kanta ta daure hannun mamansu da fan kwalin du suka zauna jigum jigum suna kallon Fatimata

A hankali ta dora kanta kan cinyar mamansu da take jin zuciyarta na yi mata nauyi sosai ta ce” a ranar da aka dora ni saman Amale (Rakumi) daga ni sai mata hudun da suka zo a matsayin fagin mijin da aka aura mini muka tafi

Mun shiga garin agadez daga nan muka dauki hanya muke tafia tamkar ba zamu tsaya ba

Sai da muka je Damagaran daga nan muke mike muka dauki hanyar kano

Muna zuwa kanno muka kwana guda muka dauki motar asuba suwa Abuja

Tafiyarmu tamkar ba zata kare ba, tsakanina da su ido ne su basa jin yarena nima bana jin nasu ya kasance muna tafiyar kurame ne sai dai abinda na lura da shi tamkar masu jin haushina domin ko abinci zasu bani sai dai su wulo mini su fadi wata kalma sannan su yi mini nuni da in ci

Ba mu mu isa garin nan ba sai da safe domin da mukai dare muka tsaya muka waye a wani garin kafin mu karasa

Gida ne tafkeke, ya tsaru, ya hadu iya haduwa

Muna zuwa kowace ta yi tafiyarta aka barni a wani tankamemen falo ina zaune ni guda

Ban jima sosai ba na fara gannin wasu mata masu kyau suma kowace ta sha kwaliya sai baza kamshi take sun fifito sun layu saman kujera gefe da gefena hakan ya saka na takure waje guda 

Ba.a jima ba wanda aka aura min da sunan mijina ya fito ashe yana cikin dakin du zaman nan da na yi ya zo ya zauna saman kujerar dake kallon tamu ya dora kafa daya kan daya

Walahi Anna mutumin sam ba annuri a tare da shi, mumuna ne, garjejen kato ne fuskarsa ba anuri ba fara.a ba haske ko kadan a nan ya kuna taba domin ba sigari bace taba ce ya kuna ya shiga ja wace nan take wajen ya garwaye da warin kwaya

Wasu maza ne suka fara shigowa, suka zauna suma inda suke hangen mu da kyau abin mamaki matan nan sai su ringa mukewa daya bayan daya su jujuya gaban mutanen  nan  wasu har su dakan masu duwawu su mamatsa a gabanmu a gaban kowa shi kuwa yana hakimce idan mace ta yi maka sai su hau ciniki cikin jarshen turanci a dauki mace a tafi da ita kwana wato Bariki

Nan wani yace wannan fa? Wato ni domin sun ga sabuwa ce a wajen

Da sauri na mike domin nunoni ya yi kafin yake yin maganar, koda ban ji me yace ba idannuwana sun nuna mini abubuwan da suka faru na ga komai na gane komai

Magana ya yi masu wace ban san me yake nufi ba suka gama kasuwancinsu ya cashi kudinsa sosai kafin suke tafiya

Sai da ya gama shaye shayensa ya taso kusa da ni sosai da muryar mashayi ya ce” ke fa sai na yi maki filafila dan kuwa an caje ni kudi kafin a bani ke kuma dan iskanci aka kawo ki daga ke sai wannan bakin kayan 

Tashi ki tube

Da mamaki nake kallon shi, in tube, wai ina ne nan? Me hakan ke nufi? Matan nan su waye? In tube haka kai tsaye ai ko matarka ce ni koda mun saba da sannin juna fitsara ne gatsal ka kale ni ka ce mini tube

Mikewa na yi da yarena na rufe ido na shiga zazaga fitsara ina son sannin inda ya nufa 

Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya kafin take kara sakin wani kukan mai karfi ta ce” Anna matan nan da suka fita bayan ya amshi kudaden karuwanci da zasu fita su kwana da karti ashe gaba dayan su suna zaune a matsayin matansa mace har bakwai ni ta takwas cikinsu ba daya ta yarwa sannan ba daya da ta san hanyar gidansu

A wannan ranar da katsa ya dake ni kafin yake zuwarmini da wata irin sufa yayi anfani da ni ba imani yana gamawa ya wawatsa kafafuwana ya goge gaba daya najasar nan ya shafe a fuskarsa harda jini jinin nan ya side hannayen nasa ya fice

Anna a wannan ranar.kafin gari ya waye sau tara yana zuwar mini

Mariama ce ta dauko kwan fitilar sosai ta haska wajen kafafuwan Fatimata, ruwa ne ke yawo wanda ya saka Mariama cewa” Anna ruwan nan kuma na menene?

Fatimata ta ce” fitsarina ne ba ruwa ba, haka fitsari ke zubar mini bama na sannin yana binna

Anna ta fashe da wani irin kuka kafin ta ture kan Fatimata ta mike ta yi dakin yaren da sauri hannayenta duka biyu saman kanta, *YoYo, YoYon fitsari Fatimata ke yi*!

A wannan rana yanda suka ga rana haka suka ga dare inda suka cure gaba dayansu waje guda ba mai yiwa yar uwarta magana sai dai suna bin juna da ido , nan Mariama ta mike ta dauko wata leda baka baba ta shinfida ta dauko zani ta shinfida ta kallo yan uwanta ta ce” ke fatimata taso ki kwonta saman nan, ke Agaishat(Bak’a) tafi wajen Anna, kuma ku taso mu kwonta dare na tafiya kar safiya ta yi mana a nan

A hankali ta samu ta lalaba ta hau, suma du suka samu waje suka kwonkwonta ba dan zasu samu yin bacin ba, sun dai yi zuru ne domin Fatimata bata gama basu labarin irin ukubar da ta sha ba aka ga fitsari na binta hakan kuwa ya tayarwa da Annar hankali bata ma tsaya ta ji sauran zancen ba

Anna ce duke kanta kasa ta kai sujada tana ta sheka kuka ta ce” ALLAH ka san wacece ni, kai ka halice ni, ya Allah ina cikin jarabawarka tun daga yannayin aurena har zuwa yau, na rasa me ke daure da ni da wannan mutumin ainahi Allahna idan ba a cikin sallah ba bana iya tuna wacece ni, menene tarihina, ina da yan uwa ko haka nake ni daya? Bana son a yi min maganar ko wa ya kawo min zancen zan nuna bacin raina ne, Allah yayana, ka bayannar sauran, wa.inda basu da lafia ya Allah ka basu lafia, wa.inda yake niyar aurarwa dan samun abin duniya Idan da alkhairi a cikin auren ka tabatarda, idan kuwa ba alkhairi bane Allah kai ka yi shi ka hana, ka hana ya Allah Allah sannan ka yaye min duhun dake cinkushe min ganina

Ta jima tana kai kukanta wajen Allah kafin take mikewa ta yi tahiya ta salamce ta dora adu.a tana ta yawaita istigfari domin ba abinda ke saurin yaye kunci irinta 

Da safe tana tashi ta dauki sansani (tabar buzaye) a cikin nata ta matsa a bakinta ta yane jikinta ta buga safiya ta fice a gidan

Zugum suke ba mai yiwa dan uwansa magana har wajen karfe tara Anna bata dawo ba, Aba daman tun cikin daren nan ya fice basu san ina ya kwana ba sannan bai dawo ba, sun zubawa sarautar Allah ido ne kawai

A hankali Bak’a ta kali gorin tsofo, ta mayar ta kule a harshen zaninta a ranta take ayanna bawan Allah ko a wani hali yake? Ko an dauko masa ruwa? Tabas yana cikin damuwar rashin ganninta yau har za.a kwana biyu, sai dai ba zata iya fita ta bar gidansu a wannan halin ba, a hankali ta rike goron ta ce” sofo ina nan lafiata klau, ka ga na saya maka goro ma kar ka damu ina nan tafe wajenka 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button