BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 21 to 30

Ban san ya aka yi, ta ina aka yi suke kawance da wannan mai sunna Alhinayettt wace ni hakanan nake gannin karya ne ba wani kawance may yiwuwa soyaya suke ba halin aurenta domin aurensa bai wani jima ba,

Ana haka ya amincewa yarinya daya soyayarsa, yarinyar da ta yi kundubala da sauran yan matan,

Soyaya suke ta hauka irin soyayar yayan zamani, ni ba zan shaidi yarona ba ba kuma zan ce yana aikata masha.a ba, aman a lokacin da yake kwana a gidan nan har kwana ta sha yi a wajensa dan kuwa sai da na rufe idannuwana na ci masa mutunci sannan na daina kamata a dakinsa,

Waye shi da zai rantse min ba abinda ya shiga tsakaninsu? Namiji ne, ita kuwa mace, sun kadaice a wajen da ba kowa sai su sai Allah, ai hankalina ba zai dauka ba! 

Ire iren abubuwan da sukai ta faruwa kennan da yarinyar da ta gama kwana gidan mu, mamaki nake da tsoro, Wardugu ina ya zubar da kunya irin ta batube? Gaba daya wannan karatu da ya yi ya saka du ya zama wani kiritace wani tsayaye! Sam ya zubar da al.adu da dabi.un tubawa idan na yi magana sai yace ai ba wani adini bane, shi gaskiya ya girma a birni ba zai ci gaba da rayuwa irin na daji ba, ! ALLAH ya shirya,

Ana haka ya tafi karo karatu inda suka hadu da mu.azam suka kula zumunci mai ma.ana, a can ya hadu da matar da yake aure yanzu wace a lokacin ba irin azabar da bata sha ba domin shi soyayarsa tana kan *AISATA* , 

Aisata? Agaishat ta tambayi Ayya,

Ayya ta ce” kwarai Aisata dai wace ubansa ya aura,

Agaishat ta ce” aa, Ayya na shiga rudani,

Ayya ta ce” bara na warware maki,….

Haka kawai mun ci gaba da fahimtar juna alhamdulilah har wardugu ya dawo daga tafia,

Nan ya zo da maganar a tura wajen yarinya a tambayo aurenta,

Tashin farko ya dira cewar ba da yawuna ba, kuma in har ni na haife shi ba za.a yi haka da ni ba, domin yarinya bata da da.a , zan so matar da zai aura ta fari ta kasance mutuniyar kirki ko dan fadar adini ku zabawa yayanku iyaye na gari,

Nan fa aka shiga tashin hankali, yarinya ta zo har gida ta tsire ni, nan ta yi ikirarin cewa” AYYA kike ko wa? Kin dai ganni, kin ga yanda nake, nice farar mace , kwakwa! Dole na shigo gidanki ko a sarakuwarki ko a kishiyar ki! 

Abin ya bani mamaki, zuciya ta kama ni na tunkareta kafin take ankara na damketa, ina faman ihun sai na nuna mata ruwa ba sa.an kwondo bane malalaciyar banza da wofi sai ga Marahut ya shigo da sauri

Kwaceta ya yi daga hannuna kafin yake fadin” ke Zannaba, baki da hankali ne? Kike ikirarin yarinya bata da tarbiya ke kina iya rantsewa waye malamin waye dalibin tsakaninta da dan naki? Ki shiga tatayinki ki daina abu tamkar wata yarinya karama!

Agaishat , a wannan rana, a gaban wannan yarinya Marahut ya wulakanta ni, ya yi min tas abinda bai taba shiga tsakaninmu ba, 

Ke dai kwana biyu tamkar kura ta lafa, domin Wardugu da ya ga na nace sai kawai ya basar ya yi biris ya shiga wata sabgar gaban nasa inda ya fara kula Walyn,

Ba.a wani jima sosai ba, domin ba .a yi wata hudu tsakani ba Marahut ya zo da maganar zai yi aure,

Agaishat ban wani nuna halinmu na matan tubawa ba, na ja ajina na yi masa fatan alkhairi, na shiga rokon Allah da ya rufa min asiri kar a je dan haihuwana ya tsaya ne wani abin zai tunkaro ni,

Sannu sannu sai abubuwa ya fara bilo mani, halayen Marahut suka shiga canzawa, 

Ya fara cika dare sosai a waje kafin ya shigo, ya dawo ya fara kin cin abincina sai yace baya jin yinwa tamkar wani inji,

A hankali ya kaurace min,

Na sha zuwa na duka nace da shi” menene damuwar? Wani abin na yi ne? Dan Allah ka yi hakuri , har ka manta alkawarin fa ka yi min? Marahut kace nice lumfashin ka, ka yi hakuri ka dawo min kamar da, ni ban wani hanaka aure ba, aman kar ka tayar min da hankali,

Marahut sai kawai ya yi min murmushi ya mike ya fice,

Du abin nan Wardugu bai san ubansa zai kara aure ba sai wani lokaci ya ji a gari, a lokacin ya garzayo gida da sanyin safiya ya tambayi uban, ashe auren ma a ranar sauran kwana biyu ni banma sani ba,

A wannan ranar na ga tashin hankali, na ga rikici, domin Wardugu idannuwansa sun rufe hakama na ubansa, ke sai da na fita a guje na kira direbobi da masu gadi da yaren gida du suka shigo suka yi kokarin shiga tsakannin uban da dan dan kuwa Wardugu ya rike wuka hannunsa yana ta balaki!

Agaishat, wannan bai isa ba sai da aka shigo da amarya Aisata, aisata yar buzaye, aisata yarinya kyakyawa, 

A ranar wardugu ya yi dan karamin hauka, ya ja iska ya zo kusan babansa ya ce” aban Wardugu ka sake ta, ka rufa mani asiri ka saketa , kar ka yarda wani abin ya shiga tsakaninka da ita, Aba, wannan bata da tarbiya, bata da haramun! Abanna ya zaka kawo macen da ta gama talatarmin da kanta a irin yannayin da ta fado duniya ni danka a matsayin matarka? Haba Abana, me mukai maka da zafi haka? 

Marahut ya dube shi ya ce” ita ba mutun bace? Kun haihu da ita ne? Na yi niya ina sonta na aureta da kudinka ne? Ka bini a sannu Wardugu, ni na haifeka kar uwarka ta zigaka ka kauce hanya! 

A lokacin ni tuni na fara gannin jiri, ni Marahut? Na sha dukan kirji nace ni mijina dan goyo ne, ba zai wulakanta ni ba, sai gashi haka ta faru, ni ba aurensa ya dame ni ba, tau da gobe ai sai Allah Allah wacece ni da zan ce ba za.ai min kishiya ba? Damuwana irin auren da ya yi, ya yi shi dan ya nuna min iyakata? Dan ya wulakanta ni? Ko wani abin ke tsakaninsa da yaronsa mai zafi haka?

A lokacin Wardugu ya fara wani irin numfashi, idannuwansa suka shiga canza launi zuwa ja, suka cicika da kwallah, ina gannin hakan na tisa shi gaba da kyar na samu muka shiga motarsa na ja muka nufi gidansa,

Muna zuwa muka tarar da Wakyn ta zo nemansa, a nan ya sauke haushin kanta domin sai da ya bala mata hannu du ya kusan canza mata halita baiwar Allah da kyar aka kwaceta,

Kin ji marabina da gidan Marahut domin akai ruwa aka yi iska Wardugu ya hau, ya gindaya rantse rantse, ya juye, nima fushi, mamaki, tsoron lamarin maza ya saka na yi watsi da shi na rungumi yarona wanda na san a duniyarnan ni ce duniyarsa ,…..

Ayya ta karasa tana dan shafa kan Agaishat,

Agaishat ta dago fuska shabe shabe da hawaye,, tana duban Ayya , ta sani bata da damar da zata iya tofa wani abin a wannan lamari domij ta yi imanin ba komai Ayya ta fada mata ba, tabas ta boye wani abin ko dan karancin shekarunta,

Sai dai wannan lamari ya tuna mata mahaifiyarta, Anna baiwar Allah, yoh ita haka rayuwarta ta kare fa, kuma bata da wani mai dauketa ya matsata daga wajen da ake cuzguna mata, ita bata san bama marainiya ce ko yar dangi, bata san daga ina ta fito ba, ba abinda ta sani,

A hankali ta mayar da kanta saman cinyar Ayya , daidai lokacin da Wardugu ya shigo dakin da salama,

Daga inda take kwoncen nan take kare masa kallo, tabas wardugu ko bashi da ko sisi sai mace ta yi haukansa, ko bashi da hali zai mitsa zuciyar mata, dan farin batube mai zamani,

Idannuwanta ta lumshe a hankali wani hawayen ya kuma zubowa daga gurbin su ta mike a hankali bayan ta share hawayen ta kai dubanta wajensa , kanshin turarensa ya cika mata hanci, 

A hankali ta ce” ina yini,

Gaisuwar da tunda suka daukota daga timiya shi dai bai taba jin ra yi masa ita ba, tsumamun idannuwansa ya zuba mata ba tare da ya amsata ba, yana kallonta har ta fice a dakin dan basu waje su tatauna ta nufi wajen Mu.azam dan gannin ko ya ci abinci?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button