BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 21 to 30

Ayya ce ta lakato shi tana yi masa murmushi tana saisaita kanta ta ce” dan gidan Ayya, sannu da dawowa,

Wardugu ya juyo da sauri yana dubanta, ya yi murmushi ya ce” Ayyana, ina yini?

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        3️⃣4️⃣

Amsawa ta yi tana dubansa da madaukakiyar kulawa kafin take mikewa ta kama hannunsa, 

Shima biye yake da ita suka fito daga dakin Agaishat suka nufi dakinta,

Walyn ce zaune a saloon mai suna Tawaye saloon, fitacen saloon ne na manya wanda sai ka isa kake saka kafarka,

Akifunta ake gyara mata bayan an yanyanke su an wanke su sosai aka dauko na kanti zako zako din nan aka shiga dora mata,

Kawarta dake gefenta tana karanta magazine, itama ana gyara atach din da za.a yanyara mata kitso ……..

Wata mata da ta tsare Walyn da kallo tunda ta shigo ce ta yatsina fuska, a ranta ta yi murmushi tana ayyana ba laifi , matar tasa bata da laifi,

Kadan ta dan muzguta ta dubi cousint dinta dan daudu wanda suka zo gyaran gashin tare da shi ta ce” ina son aikin General a rayuwana, ina son yanda yake cin uwar kananun yan iska! 

Kallota ya , ya wani yi far da idannuwansa, ya yatsina fuska tamkar mace ya ce” ke kawa, ya iya tata rashin mutunci ne fa, mutumen nan kin san da matar tsohonsa ce ya rufe? Uhum ke ni ko a lahira bama fatan mu hade da General Wardugu domin bashi da mutunci, ya iya aiki da doka, ke matarsa fa ta yarda ta kai dare a waje sai ta kwana a cel! 

Daman inda take so a tabo mata kennan dan haka ta maida hankalinta sosai ta kali dan daudun nan ta ce” kawaliya matar naci ta taba daraja ne?

Walyn dake kalonsu tana kada kafarta, ta kai dubanta wajen mai saloon din, ta maida wajen kawarta da ta yi kasake itama tana jiran gannin me zata yi? sai sauran matan dake wajen da yan tsirakun ya daudun dake wajen suna suba nasu sha.anin…..

Walyn ta saki murmushi mai ciwo, ta daga idannuwanta cike da isa da takama ta ce” Wardugu kennan, mijin mace daya, jarimina mai ban tsoro, Warduguna zazafa ne, kawata kin san Wardugu baya bin kadangarun bariki? Ke na yi imanin da Wardugu na bin mata zai je ya zabo zuga zuga ne, wa.inda idan ya zaga zai dire chek ba wai ya dane karamar yar bariki ya kasa iyanta harda kason shekara sanadiyar rabuwa da mace ba! 

Dan daudun nan ne ya sheke da dariya yana duban matar da suka zo tare, wace ta ji abin tamkar saukar guduma domin mijinta ne ya jewa wata yar bariki ya ki biya sannan ya yi mata duka hakan ya sa harda su kaso, wani tukukin bakin ciki ne ya taso mata, bata tsamaci jin haka ba , abin ya dake ta,

Kallonta ta yi da yannayin bacin rai ta ce” ke Walyn kike ko wa? Kin san ko wacece ni?

Walyn ta fizge hannunta daga hannun mai saka mata farcen ta ce” ke ce katuwar yar barki marar aji! Sai me kuma?

Mikewa ta yi itama ta ce” ke din ba yar barikin bace? Ke naki a boye kike yi ko ji kike ba.a sani ba? Meye bambancinki da yar bariki? Ke kawai bakya yi dan kudi ne aman menene bakya yin? Ko dan kina rufe takunki ne baki san wa.inda kuke labewar da falasawa ba? Ki jika ki ajiye Wardugu General ya fi karfin zama da mace daya wace na sani ne bakima goge a kai shi wata duniyar ba! Zaki ga aikin gogagiyar yar bariki domin Wardugu katuwar kadara ne wanda malakarsa sai tsayaye ba isa ce zata kai ki ba mu je zuwa!……

Walyn ta yi murmushin rainin hankali kafin take bufe jakarta, 

Yan jika goma goma ta fitar dami guda ta bale yar takardar dake zagaye da su wace itama sai kyali take, ta dauki bakin gilas dinta ta jefa katuwar wayarta a jaka ta juyo sosai wajen matar da sauran mutanen saloon din ta daga kudin nan ta sake su a iska wanda hakan ya saka du suka shiga wawusoso harda mai saloon din da yarenta kiwa na nema har wasu suka shiga dambacewa , aman banda wace ake kira da kankana! 

Walyn ta bi kawayen da kankana ta zo da su da ido ta ga suma sai wawa suke harda yan daudun,

Yatsina fuskarta ta yi ta ce” abokin mai kanwa ba ya rasa burbudi, Wardugu ya daure min a niger tunda ya sakar min yayan banki, na kwana lafia koda Wardugu ya shiga tsakiyar yan bariki ba zata motsa ba domin kyankyaminku yake!

Ta kara taku har gabanta ta zaro idannuwanta ta ce” ki sauke girman kai ki duka ki kwashi kudi…..su kike kwadayi! 

Iska ta ja ta kaiwa Walyn duka warda itama ta damketa suka shiga dukan junnansu,

Sai da suka lilisa junnan su sannan mutanen wajen suka shiga tsakanin su kowace na haki,

Walyn ce ta warce jakarta ta yi gaba inda kawar tata ta biyota da gudu tana kiran ta tsayata, aman ina cikinta take ji yana wani irin hautsina mata, bata san me ke damunta haka ba yanzu, ya kasance tana yawan jin abubuwa a tatare da ita, 

Wardugu ya jima wajen Ayya, inda suka tatauna sosai sannan ta saka shi a gaba kan sai ya ci abinci,

Agaishat na fitowa ta nemi Mu.azam, sai dai bata ganshi ba hakan ya saka ta fice ta nufi wajen runfar Ayya mai wani ni.imtacen sanyi tana neman Mu.azam,

Nan kuwa ta same shi, ya kurawa waje daya ido, ya zurfafa sosai a tunani wanda yannayin fuskarsa ta nuna ba tunanin dadi yake yi ba,

A hankali ta karasa ta kuma maimaita salamar da ta yi ta yi masa tun daga dan nesa da shi,

A dan tsorace ya kalota kafin yake daidaita yannayin fuskar sa ya amsata yana mai kokarin gyara mata kujerar dake kusa da shi,

A hankali ta ja ta zauna tana dubansa, yannayinta ya nuna itama ta shiga damuwar da yake ciki, 

A hankali ta ce” me ke damunka ya Mu.azam?

Daman ita yake kallo, dan haka ya bi bakinta da kallo yanda ta fadi maganar a hankali sannan a cicire domin dai tana faman koyon yarensa ne,

A nitse ta janye idannuwanta daga cikin nasa, domin kallo nr yake mata tamkar zai fada idannuwan nata take ji,

A hankali ya ce” Agaishat, 

Ta dago tana dubansa, inda a take ta ji gabanta ya fadi da yannayinsa,

Mu.azam ya ce” kin san soyaya? 

Agaishat ta zaro idannuwanta tana dubansa, tama rasa me zata ce da shi,

Mu.azam ya ce” kin taba yin saurayi wanda kika ji kina so?

Agaishat ta saki murmushi mai kama da na sakalci, domin ita abin har ga Allah dariya ma ya bata, A hankali ta maimaita kalmomin” *So, Soyaya, Saurayi?*

Mu.azam ya dan kankance idannuwansa ya ce” yeah,

Agaishat ta dube shi, duba na ido da ido kafin take fadin” *Ban san shi ba*! 

Da mamaki yake kallon ta, bata san shi ba tace fa? Aman daga ina Agaishat ta fito haka? Ko dai masu son nata ne basu yi mata ba?

Yin wannan tunanin ya saka gabansa ya fadi, a ransa ya ayanna ya salam, kar dai a je nima ban yi mata ba,?

Muryarsa sanyaye ya ce” du a maneman soyayar ki ba wanda kika taba jin kina so?

Agaishat dake dubansa itama, bata dago ina ya nufa ba, domin dai ita ba.a taba kamanta za.a ce ana sonta ba, dan haka ta bashi hankalin ta sosai ta ce” ba wanda ya taba fada min ya ake so din ne,

Dariya ya shiga yi kasa kasa yanai mata wani duba kafin yake fadin” ba fa zolayana nace ki yi ba Madame,

Bata san kalmar madame ba, aman ta gane yana nufin wasa take yi masa, dan haka ta ce” ban taba yin saurayi ba, ko an zo zaben yan mata a gidan mu ba.a taba zabena ba, Ba yace dan na cika baki da muni, ni ba alkhairi bace dan baki ba alkhairi bane, hakan ya sa ba mai zabena bare a biya sadakina, har kanwata an zaba sai dai kafin auren ta rasu ita,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button