BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 21 to 30

Dubanta yake har ta gama yi masa bayani da kwatance da komai dan ya gane da kyau, ajiyar zuciya ya sauke a ransa ya ayanna na godewa Allah ai da basu zabe kin ba da sun saka ni a ukunna,

A fili kuwa ya ce” wa ya fada maki baki ba alkhairi bane?

Agaishat ta ce” da alkhairin ne, da mahaifina bai kyamace ni ba da alkhairin ne da nima ana yi min dinkuna irin na yan uwana, da alkhairin ne da jama.ar gari sun mutunta ni a matsayina da dan adam mai daraja a cikin halitun Allah, da alkhairin ne da na yi saurayi koda mahaukaci ne a *Gida*, 

Katseta ya yi da fadin” aman sai na ga kina da ilimin adini sosai, ya aka yi kika kasa imani da haka?

*Agaishat , malamata, wa ya halici fari da baki,?*

Agaishat dake dubansa ta sada kanta a hankali, kafin ta ce” Allah ne,

Shin da ya halici baki ya kawo wata ayya a alkur.ani mai girma, a hadissai ko wani litafin na adinin fake nunin bakar fatar nan da ya halita ya haliceta ne dan wani laifi? Ko mai wani laifi?

A hankali ta kuma fadin” aa, ban karanci haka ba,

Mu.azam dake dubanta ya ce” Bilal, bawan Allah, wacece kalar fatarsa? Ya darajarsa take?

Dago da idannuwanta ta yi ta ce” baba tsofo ya ce shi ne ya fara kiran sallah , ya ce mutun ne mai daraja, makusancin fiyayen halita,

Mu.azam ya gyada mata kai kafin yake ciro wayarsa ya samo hoton ka.aba ya ce” zo ki ga ka.aba a hoto Agaishat, zo ki gani…

A hankali ta matsa tana kallo, kalar bakin ya tafi da imaninta, abin ya yi mata kyau a ido, a hankali ta kai yatsarta ta dan shafa hoton, 

A hankali ya ce” ba wani bawan da ya fi daraja, ya fi kusanci fa ubangijinsa sai mai yi masa biyaya, mai tsoron shi, mai kiyaye dokokinsa, a cikin nan kin ji an ce *Farar fata ta fi bak’a?*

Agaishat da take jin wani yamyamyam a jikinta na dadi ta girgiza kanta,

Mu.azam ya ce” makafi ne ko kwakwaluwar su bata ja? Ya aka yi basu yiwa abin kaunata wawa ba? 

Da sauri ta kallo shi,

Kansa ya dan sada ya ce” kina da tsararen kyau, fitinanan kyau, baki da tsayi Agaishat…baki da kiba har can, yannayin jikin ki ya tafi da yannayin tsayin ki, 

Bakin ki ba mai tabo bane bare shaida, gaba daya ya tafi iri daya ne baki mai haske mai nutsuwa, agaishat, fuskar ki yar doguwa ce mai dauke da dara daran idannuwan da a kowani yannayi kike su kadai sun ishi mutun, Agaishat Allah ya tsara ki da hanci mai tsayi mai yan kofofi wanda ya yi das da dan madaidaicin bakin ki, 

Rashin hayanniyar ki ya hadu ya kara kawata halitar ki, ke da ba dan kar na kauce hanya ba da na fada maki sauran tsaruwar ki,

Dan dakatawa ya yi gannin yanda ta zuba masa ido, sai a lokacin ya tuna ya saki baki sai zuba yake mata,

Dan kimtsa kansa ya yi a hankali ya ce” Agaishat arrrakam (Agaishat ina son ki),

Wata irin faduwa gabanta ya yi, da wani irin firgici ta akle shi, tsoro, mamaki, surprise, murna suka hade suka saka jikinta ya dan fara rawa, So na? Ji ta yi wani nauyinsa ya diri mata,da sauri ta sada kanta kasa, kafin take mikewa da wani irin sauri ta jua inda Mu.azam ya mike yana kiran sunnanta daidai Wardugu ya yi kokarin kawar da kansa dan kar su ganshi bayan ya jima wajen,

Ganninsa ta yi yana ta faman taba labulen ayya wanda ke gyare tsaf a wajen aman kamar wanda yake gyara shi, 

Kanta ta shiga sosawa kafin take dan rabar gefensa ta shige ta taka matatakalar da gudu gudu ta nufi dakin ta,

Da ido ya bita, da wani irin kallo, a hankali ya lumshe idannuwansa ya juya ya fice a dakin ya nufi wajen mu.azam da ya koma ya zauna ya dan dafe kansa da hannunsa cike da tsoron kar a je ta ki karbar sa, 

Gaban wardugu ya ji na wani irin gudu wanda har ya ji wata yar zufa ta karyo masa, 

A dan hanzarce ya karasa wajen amininsa yana mai cike da zulumin yannayinsa, a nitse ya kai hannunsa ya ce” Mu.azam?

Agaishat na shiga dakinta ta karasa da sauri wajen madubi, lufayar jikinta ta warware ta tsurawa kanta ido, du abinda ya fada take son gani sai dai ita bata wani gannin kyanta, , …..

A hankali ta kai zaune ta cuje abinda ta daure gashinta da shi wanda hakan ya baiwa gashin damar zubowa baki dayansa ya yi lumbuk a jikinta, hannayenta ta cusa ta fashe da wani kuka mai zafi, a hankali, muryarta na rawa ta ce” Anna, ina kike? Anna wai yana so na? Ashe nima mutun ce Anna? Anna wai ina da kyau, wai nima mai daraja ce, Anna nima na yi saurayi………..tana kukan kuma ta shiga dariya a hankali ta furta” Mu.azam, nawa????????????????????????????????????????????

        I.m sowi fans , jiki da jinni ne ????‍♀

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        3️⃣5️⃣

A hankali Wardugu ya kai hannunsa ya taba Mu.azam, murya a sanyaye ya ce” Mu.azam?

Da sauri ya dago da kansa daga yannayin da ya afka, ya kali Wardugu da kyau kafin yake sakar masa murmushi,

Wardugu ya ce” me me ke damun ka?

Mu.azam dake dubansa ya dan sada kai, ya kuma dagowa yana dubansa ya ce” jinta nake a raina har jikina Wardugu, sai dai ban san ba ko zata aminta ta aure ni a dan kankanin lokaci kafin mai yiwuwa ta yiwu da ni?

Wardugu ya ji gabansa ya fadi, Allah yana ganni idan da abinda ke tayar masa da hankali a yanzu bai fi rashin lafiar Mu.Azam ba, lamarin na girgiza shi in ya tuna, yakan tsinci kansa ba karfi bare laka a jikinsa idan ya tuna, …….

Duk da ya fahimci wa yake nufi aman sai ya kashe ido guda yana kallon Mu.azam ya ce” kai, soyaya ka afka daga zuwa garin mu? Fada mini wacece mai sa.ar samun abokina ?

Mu.azam ya lumshe idannuwansa ya ce” Wardugu, na kan ji wani iri idan muna hira da kai a yanzu, domin du ka canza min kan da, a da idan muna hira tamkar yaki muke, ka warto ni na tsokaneka mu yi ta shirirta har sai an shiga tsakanin mu, aman a yanzu du abinda zan maka sai na ga ka wani yi shiru ka kyale ni ko kuwa ka wani lalaba ni, malan matarka ne ni? Ko dan bani da lafia? Ni irin yanda muke da ya fi birge ni, sai ka wani dawo ladabi? 

Wardugu dake kallonsa ya ji zuciyarsa ta mugun karye, hakan ya saka wata zufa ta karyo masa, a yanzu da suke zaune a haka ba mamakin shi wardugun shi ne gawar fari, aman kuma rashin lafiar Mu.azam da ta bayana kanta ne ake kiran kisan mumuke, domin dai ta hana kowa walwala tsakanin mutane ukun nan, Mu.azan din, docternsa, sai Wardugu da ya sani shima, 

Wardugu ya saka hannunsa ya share gumin da yake , ya miko hannunsa kusan na Mu.azam ya ce” wa kake so? Ko yar gidan waye, ko wa take takama da shi nan duniya sai ta aure ka, kuma dole ta so ka! 

Mu.azam ya kwace hannunsa yana dubansa da yannayin tausayi, ya san waye Wardugu farin sani, wannan yannayin da yake ciki yayi imanin da ace zai samu kuka da ya koka tun karfinsa ko zai samu sauki,

Goshinsa ya dafe yana dubansa, ya ce” ka daina damuwa da lafiata Wardugu,

Wardugu ya katse shi da fadin” idan muka gwada aikin nan fa?

Mu.azam ya ce” bayan ka tirsasa ni shan lemun tsami cikin ruwa masu zafi, kana tirsasani cin tafarnuwa, kuma zaka bijiro da maganar aikin da na guduwa ? Wardugu aikin nan fa mai yiwuwa shigar da za.a yi da ni a fitar maku da gawata,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button