BAK’A CE Page 21 to 30

Wardugu ya ce” kuma tana iya yiwuwa a fitar mana da kai ras ka sami lafia,
Mu.azam ya ce” mafi akasari idan Allah ya yi an sami lafiar ma kwakwaluwa na tabuwa, ko a samu shafewar tunani, cikin kaso dari bai fi 2/100 suke mikewa garas ba Wardugu, na fi son idan ta Allahn ce zata kasance da ni nan kusa ya kasance ina kusa da mutanen da nake so suke so na,
Wardugu ya kura masa ido, kallon cikin ido, ya ce” ba zan iya ba, zuciyata mai mugun rauni ce a kanka, ina jin rashin karfi a abinda ya shafe ka, baka yi min adalci ba idan har ka yi min haka, !
Ya mike ya dauki kys dinsa, ya dora hanayensa saman table din yana dubansa ya ce” baka isa ka min haka ba, ba zan taba barinka ka yi min haka ba! Zan nemi karin bayani ……
Juyawa ya yi ya fice inda yake jin kansa na mugun sara masa,
Mu.azam ya girgiza kansa bayan ya bi shi da kallo, a hankali ya furta” ban so ka ji ba, sai dai rigumarka ta saka ka tankalo abinda zai hana maka nutsuwa!, ya hana maka jin dadi!
Tukin garari ya yi wanda ikon Allah kawai ya kai shi gidansa lafia,
Yana zuwa ya sauka daga motar ya rufe ya nufi bangarensa kansa duke yana mai jin yanda yake sara masa,
Har zai bude ya shiga, sai ya fasa ya dubi bangaren Walyn,
A hankali ya juya akalar tafiar tasa ya nufi bangarenta yana wata irin tafia wace da ka gani zaka fahimci da karfi ne ake yinta ba dan ana jin dadinta ba,
Wardugu na shiga ya zarce falonta baba inda kamshin turaren da aka turara ya yi masa salama.
A hankali ya shige yana hangenta kwonce saman doguwar kujerar falon nata tana danna waya ranta da yannayin bace, sannan da maganin zazabi mai tafasa a gefe da alama dai ita ta sha bata jin jikinta,
Da sauri sauri ya karasa gareta yana mai cire rigar tasa ta sama ko zai ji dan sanyi sanyi ya karasa wajen Walyn da ta zabura ta mike tana dubansa da wani irin yannayi mai fasara abu uku, na farko ganninsa a bangarenta, na biyu yannayinsa ya firgitata, na uku mugun haushinsa da take ji domin yanzun ma a cikin grup dinsu na manyan mata ne ake tatauna maganar har wata na ikirarin ita walahi a duniya ba wanda ya yi mata irin wardugu halayensa na kasheta da dadi, idan ta kali hotonsa takan jita a wata duniya, tunani take wannan mutumen ya kasance hazarsa a gabanta kadai ya isheta, duda an kwabeta cewar da matarsa a gidan fa , kamar an zungureta ne an tirata domin a lokacin ne ma ta ce” Wardugu ai mijin mace hudu ne wanda Allah ya halita masa ba wani shege ba, duniya kuwa idan takamarka sauko wani a can ya kwana,
Tana wannan tunanin wardugu ya karaso jikinta, batai tunani ba ta ji ya rungumeta da karfi wanda sai da ta ji kamar numfashinta zai tsaya dan ya kanainayeta ya hana ta motsi,
A hankali ta rungume shin itama, ta shiga sauke ajiyar zuciya tana shakar turaran jikinsa wanda koda ya yi zufa bata hadewa da turaran ta bayar da wari wari, turaran ke cin karfinta bama zaka gane ba sai dai idan mafi kusanci da shi ta ji gishiri gishiri a jikinsa a irin wannan yannayi ????,
Gajiya ta yi da tsayuwar domin daman ba wani karfin jikinta take ji ba,
A hankali ya bita saman kujerar domin shi a wannan lokacin bashi da bukatar komai sai na ya jima a jikinta , ta rungume shi, yana so ne kawai ya ji shi a jikinta ba komai ba,
Haushi Walyn ta ji, aa me wardugu ya dauketa ne? Jiya ya gama wulakantata, ya fanshi jikinta, ya tashi ya yi tafiyarsa, ta je saloon ta kwashi rashin mutunci dan shi, ta zo gida mata na wawarsa shi oga! Yanzu ya kuma dawo mata da bukatar sa? (Domin a tunanin ta , bukatuwa ce ta dawo da shi a irin wannan lokacin ),
A hankali ta zame jikinta tana dubansa yanda ya yake ringeshe jikin kujerar idannuwansa du a lumshe,
Baki ta dan yatsina, a fili ta ce” ka san yau a saloon wata karuwa ke ikirarin sai ka aureta?
Daga yanda yake kwonce yake dubanta, a hankali ya ce” ki zo gare ni Walyn…..
Ya mika mata hannunsa,
Kafadarta ta make irin na yangar nan na mata ta ci gaba da fadin” ka saurare ni mana, ina maka hira ka wani basar,
A hankali ya kai hannunsa wajen goshinsa kafin yake mata alama da ta ci gaba, domin ya lura kwata kwata matar tasa bata lura da yannayinsa ba, bata da niyar fara sauraronsa, zata tiso abinda ke damun nata wato *kishi da isa*,
Zamanta ta gyara tana mai dubanda da kyau ta ce” ni kuwa na bata amsar cewa , Wardugu mijin mace daya ne, ba zai kula wace ta san mutuncin kanta bama bare ita karamar yar bariki, Wardugu nawa ne ni kadai!
A hankali, ba tare da wani damuwa ba ya ce” *wa ya yi miki wannan albishir?*,
Da sauri ta dubo shi, da yannayin mamaki ta ce” me kake nufi?
Dagowa ya yi yana dubanta ya ce” *Auten zobe muka yi da ke?*,
Walyn ta kara zabura da mamaki ta ce” kana nufin sai ka kula wata macen?
Wardugu ya buda idannuwansa da kyau, ya ce” *To waye ni?* , an fada maki ni ba mutun bane? ,
Yanzu sai ka ci amanata Wardugu? Sai ka dubi wata macen da sunan so?
Kallon kar ki raina min wayo ya yo mata sannan ya ce” tunda hirar kike so mu yi bari ki ji, da farko dai ni mutun ne dan Adam wanda nake tara ba goma ba wanda nake cike da laifuka , nake dauke da zuciya mugun nama, wanda na kwonta da sannin Allah ya halasta min auren hudu na jera, nake da sannin ina da wajen saka su, ina da abinda zan ciyar da su, na tufatar da su, sannan ….ya yi murmushi ya ci gaba da fadin” na sauke hakinsu saman lit (bed) ba tare da gajiyawa ba! Ke kin san wa kike aure shi ya sa kike kishi! To a haka da nake, akoy wa.inda ban yi masu ba, sam bana gabansu, bana cikin tsarin da zan samu koda gaisuwarsu ne! Walyn, ana aure dan soyaya, da tausayi, dan sha.awa, dan arziki, ba zan maki karya ba, ba zan yi maki rantsuwar ni na isa na kauce kaina daga kan *mace yar dagwas dagwas mai dorinar dukan maza ba* , ciki kuwa koda yar barikin ce da kike fadi mai yiwuwa na zama silar shiryuwarta!
Gaba daya har Walyn ta fara fita a hayacinta , ta hayayako ta ce” me na gaza da shi Wardugu da kake kiran min sunnan wata a gabana?, *Kyau, fari, tsafta, girki, iya tarairayarka,* wane na gaza a cikin nan?
Haushi ya kara kama shi, itace ke ikirarin iya tarairayarsa bayan yanzu ya shigo mata a wani yannayi maimakun ta dubi halin da yake ciki ta zauna a kusa da shi aa, sai ma ta tsankalo kabarun banza da wofi, kai da Walyn a wajen aikinsa take kai koda ficewa take ta hanyar da an kwashi yan kalo da ita da matan dake kai masa ziyara, wai kuma ta yi ikirarin ita ta san kanta ita mai kyau me memememe, *Isarta* ta hanata ta duka masa yanda ya dace, takamarta da halitarta sun hanata gane ainahin biyayar aure, sai idan baki ya bude ta shiga zubo masa abubuwa mararsa tsari, dan haka da yannayin haushin nan ya mike yana daukan rigarsa ya ce” *Kin san dadin miya ke sakawa a yi kari!*
Wai wai wai wai , shin fans zaku kuwa iya zama da mai hali irin na wardugu????♀????♀????♀,
Su waye wardugu ke ikirarin ko arzikin gaisuwa baya samu daga wajen su? Me ke damun wardugu?
Me ke damun kwakwaluwar Wakyn? Ta hada kyau, fari, tsafta, kanshi, girki, bata isa ta daki kirjin mijinta na ita kadai bane?????
Mu.azam, zai kai labari kuwa?
Agaishat Ayya, Anna, Ba, Marahut, ya labarin su ne?????????????
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*