BAK’A CE Page 21 to 30

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3️⃣6️⃣
Rigarsa ya rataya a kafadarsa, ya juya da niyar barin mata bangarenta domin bai ga dalilin fa zai saka a caza masa kwakwaluwa a waje, ya zo wajenta dan samun nutsuwar zucuya itama ta caza masa, yana bauwa Walyn damarta ta mace, na ta yi korafi a kan abinda bai mata ba, ya sha duba korafinta ya nuna mata ya tuba a aikantance ta hanyar daina abinda ta kawo masa korafin a kai, sai dai abubuwa na damunsa na irin yanda ita ba abinda ya sha kanta da damuwa da damuwarsa, bata wani damu da yannayin da zata ganshi ba indai da abin fada zata rufe ido ta fada da gatsali,
Murmushi ya yi yana girgiza kai bayan ya kare mata kallo du ta fice a hayacinta daga wannan yar maganar? To idan Allah ya kadarto min kara aure yaya zamu kwashe da Walyn?
Rai bace tana kokarin fashewa ta kuka ta ce” Wardugu, idan ka yarda, idan ka saki, ka yi saken kula wata mace sai dai a kwashi gawarwakin mu baki daya! Wardugu kamar yanda Batuben namiji zai iya suka da wuka dan an kali matarsa toh zan iya suka da wuka dan an rabe ka!
Tsayawa ya yi yana dubanta, iya gaskiyarta ta fada domin a tsaye take tana dubansa ido cikin ido, jikinsa ya ji ya dan yi sanyi, karasawa ya yi kusa da ita , ya dan sasauta murya aman a cunkushe ya ce” Walyn, bakya aiki da adini ne ke? Kin san da sunnar ma.aiki ce? Me ya sa zaki daukarwa kanki zafi haka? A haka Walyn ban ma nuna zan yin ba idan zan yi fa?
Idannuwanta ta dago dan sakawa cikin nasa domin ya darata tsayi, ta ce” na tsinci kaina a zazafar kaunarka, haka na wayi gari na ganni zundum , na shanye wulakanci kala kala dominka, kai da kanka ka sha wulakanta ni mai girma, karaya uku ka min a gabai na, du na shanye! Kai a tunaninka ba zan shanye azabar kawar da du wata tsagerar da ta tunkaroka ba? Wardugu, mahaukaciya ce ni a kanka! Sakara ce da a yaren ka! , kamar yanda ka sumar da saurayin da ya yaba maka ni, ni kuwa ka yi min marin da na yi ta ihu sai da kyar jina ya dawo dan na yi kwaliyar da aka yaba ni, haka zan iya rike makigwaron du wata yar iskar da ta yabe ka!
Kansa kawai yake dan girgizawa yana dubanta, Walyn, walyn Wardugu…ya saki murmushi ya juya,
Haushi ya kara rike mata zuciya ta daga murya ta ce” ciki kuwa harda wannan tsohuwar kilakin da ta ki aure take binka gida ma.aikata, anguwa! *Alhinayett*, ciki harda ita,
Dawowa ya yi ya tsura mata ido, kafin yake fadin” ki daina zagin Alhinayett domin mai son ki ce, tana yaki kan ki, tana yi min fada kan ki,
Karuwancin kennan! Karuwancin kennan Wardugu! Ta shiga jikinka har ka ji in ba ka kasance da ita ba , ba zaka ji nutsuwa ba!
Wardugu ya zauna saman kujerar dakin ya ce” Walyn, Alhinayett ba yar bariki bace, mutun ce mai daraja, mutunci ne tsakanina da ita, ke kin san da soyaya ne da tuni na auri abina na kilace, jimawarta ba aure kuwa Allah ne bai kawo lokaci ba, aman an kusa saka aurenta, ki daina magangannu irin haka Walyn , ke macece, ko a kan ki ba haihuwa zaki yi watarana, ba.a so mutun ya cika izgili,
Kai ta kawar ta ce” wardugu, gaskiya ne baka so? Alhinayett ai kowa ya san kilakin ka ce!
Wardugu ya mike a karo na uku kennan, ya karasa kusan Walyn yana mai binta da kallo, hannunta ya damko ya bude yana dubawa, ya riko fuskarta ya daga idannuwanta yana dubawa, ya gwale bakinta ya saka yatsunsa ya ciro harsanta yana dubawa, ya saki ya kama rigar dake jikinta ya dage sosai har biyu suka bayanna, nan ya tsura masu ido yanai masu kallon kurullah,
Cikata ya yi , ya dan taka ya tako kafin yake nunota da yatsarsa manuniya, muryarsa ya saki baki daya ya ce” Ba karuwa bace! Aminiyata ce, du wanda ya zagar min ita zan bata ransa! Kika kuma kiranta da karuwa na rantse da girman mahalicina sai na aureta koda kuwa ta tsane ni , koda mutuwa zata yi dan kina na kawota na kwana da ita saman gadon ki! Ke da ba dan ina hangen kamar mai shigar ciki ba yau da na nuna maki tsagwaron rashin mutunci! Ya ina taro ki kina raina min hankali? Walyn ni in ban kara aure ba ni ba dan babana bane!, ni ba jinin tubawa bane! Walyn dole ki zauna da kishiya in baki kona mu ba ke ba yar babanki ba ce!
Fuuuuuu ya juya ya fice yana jin kamar ya koma ya yi kwalo da ita, sai dai yana tsoron kar a je ciki ne da ita, ta ja ya yi mata lahani bayan adu.arsa kennan shima allah ya azurta shi da haihuwa, yar bakin ciki kawai take jan sa masifa salon ya biye mata idan cikin ne su barar su shiga uku!
Haka ya koma bangarensa ya zube a falon sa ya yi ruf da ciki ya dora hannayen sa saman kansa yana yamutsawa yana tunanukan rayuwa,, walyn ba wayo , haka ya ayyana a ransa kafin ya kuma fadin….ta saka sai na kara zama da wata macen? Walyn shirme shirme????♀,
*Timiya*
Amai take kwararawa har kamar ta shide, inda *Ba* ke tsaye ya dan duka dan tsayinsa, da rawaninsa yana dubanta,
Gefe guda kuwa su Anna ne da yayanta yauma Gaishat ta kawo mata ziyara da dan cikinta da ya tasa kafan wanda sarki ke mugun zumudi kansa tkar shi ne dansa ma fari,
Suna kasan bishiyar gidan suna zaman su suna yar hirar su , domin yanzu da safiya ta yi Mariama ke fitowa ta gyara wajen ta shinfida tabarmar kabar da Anna ta siyo daga garin agadez ta dauki du abinda zasu bukata su koma can su yini abinsu , nan suke sallah su ci abinci, ta dauki na baba tsofo ta kai masa domin Gaishat na tsaye kan abinda zasu ci, sarki baya wasa da ta nuna tana da bukata ake kwasa a kai mata itama ta kwasa ta kaiwa mahaifiyarta, inda ta saka sarki ya yiwa *Ba* gargadin kar ya kuma kwashe masu abincin su,
Bakinsa yake motsawa ya juya ya karewa Anna kallo da yarenta su uku sun zagayeta, ya juyo wajen amarya dake maida lumfashin kadangare bayan ta gama sheka amanta,
Tabar sansaninsa ce yake gumtsa a bakinsa,
Bakin ya bude ya totofar da yawu, domin du mai shan tabar sansani ya kasance yana tofe tofen yawu, ya juyo wajen amarya ya ce” sannu *Uwar mai uba biyu*,
Kallon kasan ido ta yi masa kafin ta kada kai,
Juya kansa ya yi wajen Anna ya ce” duniya, anai min kallon ina yiwa yarana aure suna tafia birni, ke gashi kin dauki yar santal ki badata yawon kilaki!
Da sauri Anna ta kallo shi, gabanta ya fadi,
Kura mata ido ya yi ya ce” karya na yi? Ke yanzu zaki daki kirjin yarinya na hannun kirki? To ni dai in tana aiko wani abin ake boyewa ana ci Allah ya isa! Dan ko dan ciyar da ita da na yi ya isa a yaga mini wani abin ba a rufe ni da baibai hannu ba!
Gaba dayansu dubansa suke,
Ya tako da fararan kafafuwansa da sukai fari fat na kasar garin ya dubi Gaishat ya ce” ke kuwa fa? Haka zaki saka mini ko? Kin samu na aura maki sarki , ya nada ki sarauniya aman ni kika saka kafa ki ka shure ni sai wannan tsohuwar matar kike baiwa abinki ko? Ai dukan ku Allah na kallon ku! Ko hakin ciyar da ku da na yi zai bi ku,
Ya kara tofar da yawu yana duban Mariama dake bin sa da wani mugun kalli itama da sansanninta a bakinta kamar na sauran yan uwanta da Anna, ya ce” ke kuwa ke ce gagarara ko? Mai tarda ni wajen majalisa ki tirke ni gaban abokaina, ke mai karfi wace ta fi kowa iya rashin kunya, a gaban yan uba kika yi ikirarin zaki ga ubanda zai maki aure ko? Ba laifi, ba laifi Mariama, in sun zo sai mu basu gidan su saya su tafi mu kuwa mu koma zaman titi ,