BAK’A CE Page 21 to 30

Mariama ta yatsina bakinta ta kawar da kanta,
Babar rigarsa ya kabe ya ce” kudinku yanzu na fara ci, ni da ku ba shari.a domin ni na haife ku! Dole na yi maku aure na mori kudin ku! ,
Ke kuwa, ya nuna Anna da take jan dan karamin carbinta tana shamaninta ya ce” kin ji kunya, anai maki kallon saliha sai gashi kun hada baki da tsohon can kun tura yarinya nema; ana zaton wuta a makera su Annar yara sun kunata a masaka.
Yana gama fada ya fice a gidan yana ta tofe tofensa,
Mariama ta dantsa yatsarta a bakinta tana yiwa yayarsu kallo mai kama da harara, domin ita ta yi masu kashedin kar ta kuma gannin wani ya biye masa, dan ta lura hakan na masa dadi
Gaishat ta yi murmushi tana dubansu ta ce” baku lura ya fara yin sanyi ba?
Mariama dake hararar Amaryar Ba ta ce” sanyi? A wannan tsohin najad…..
Bige bakinta da Anna ta yi ya saka ta kasa karasawa tana turo baki,
Da yannayin bacin rai ta ce” in kina irin magangannun nan hankalina tashi yake, mahaifin ki ne fa, ko me ta zama adu.a ce tsakanin ki da shi, ya zaki ringa halaya irin na wace bata da tarbiya? Bana so Mariama ,
Aman Anna, kina ganni abinda yake yi fa, ke tsoronsa kike , to ni bana tsoron sa,
Kuma bakya tsoron Allah? Gaishat ta fada tana dubanta, hakin dake tsakanin ki da shi na matsayinsa na uba Allah ba zai bar maki ba, ki bi shi, ki yi masa biyaya, ki bar shi idan shi gobensa bata dame shi ba kai nasa,
Shiru ta yi tana duban fatimata dake dan zane a kasa ta ce” wacen matar ciki ne da ita fa? Kuma kum san ba cikin Ba bane,
Anna ta kwalalo ido tana dubansu, a dan harzuke ta ce” na ga mai isata yau da yaren nan, kun yi da shi ne? Bama wannan ba sa.anku ne? Du wace ta kuma gigin muguwar magana a kan mahaifin ku a gabana zamu bata da ita! Ba ruwana ban koya maku ba, baku ga ina yi ba, kuma idan na ji tsoronsa ai ba laifi ba, shugana ne, wanda aljannata ke karkashin kafafuwansa, a haka ma ya muka kare da shi bare na yi masa gatsali? Ku daina bana so!
Ta karasa tana dan dafe kanta domin har ya sara mata maganar nan da ta yi,
Da dadaya suke bata hakuri suna masu lura da yannayinta………….
Daga inda yake ringeshe yake biya bagara a fili hannunsa a kan zuciyarsa,
Sai da ya kai karshe ya samu ya dan daga ya jingina yana duban hanya dan ya san yanzu Mariama ta zo,
Yana jin dadin lamarin mariama sai dai ita ba.a hira da ita, kimkim take masa har yanzu haushinsa take ji, bata san irin yanda shima hankalinsa ke kan Agaishat ba, adu.arsa a gareta ne, da fatan saduwar fuskokinsu kafin ya koma ga mahalicinsa,
Jama.a Wardugu na neman karin aure????, du mai son karya kafa ta shigo layi????♀????♀????♀………………. dan Allah aunty Alhinayett kar ki tura masa wannan page din wollah lalla batai kwari ba kar ya karya min kafar nima????????????
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3️⃣7️⃣
Yana nan zaunen kuwa sai gata ta shigo da salamarta ciki ciki,
Ajiye masa robar abincin ta yi bayan ta dan jefa masa wani kallo ,
Wajen ruwa ta je ta dibo masa ta zo ta tsuguna ya wanke hannunsa ta kuma cikowa ta ajiye ,
Dakin ta tatare kamar kulun shi kuwa yana cin abincin yana duban yannayinta, Mariama akoy shiru shiru sai dai yannayinta na yau kamar ranta a bace ne,
A hankali ya ce” me ke damun Mariama?
Tana gurza goron hannunta ta dan dago ta dube shi, ta ci gaba da gurzar abinta,
Can ta ce” idan ta zo hankalinta a tashe, ranta a bace, idan ta fada maka ka taba yi mata maganin damuwarta ne sofo?
Baba tsofo da ya gane Agaishat take nufi sai ya girgiza kansa a hankali , kafin ya ce” ban taba magance mata damuwarta ba Mariama, sai dai nakan saurare ta, na ji damuwarta, na yi mata nasiha a musulunce da girma, nakan ji ciwon damuwarta a raina na nuna mata ba dadi, aman kuma sai na nuna mata girman hakuri,
Shiru ta yi tana jinsa, can ta ce” wai dan na kire shi da mumunan sunna Anna ta dake min baki bayan bata taba koda shakunana ba, kana da labarin irin manya manyan munana halayansa, aman sai ta wani tare mashi?
Baba tsoho dai kallonta yake , har ta dasa aya tana hucin bacin rai, a nitse ya ce” su iyaye, sune masu madaukakiyar daraja in kika cire Allah da mazon sa a wajen dan adam, su iyaye Allah ya ce a bi su a yi masu biyaya banda hanyar sabonsa,
Shi abinda yake ba sobon Allahn bane yake?, ta fada tana duban Baba tsofo,
Baba ya gyada kansa yana dubanta ya ce” ya taba daukan y’a ya bayar ba.a daura aure ba?
Mariama ta girgiza kai,
Ya ci gaba da fadin” yana yin aurwn yayansa dan dukiya, adini bai jaramta hakan ba sai dai ta yannayin da yake yi ne,
Yana yi ne tamkar yana siyar da yayan,
Wa ke tafe da duniya da abinda ke cikinta Mariama?
Ya kuma watso mata tambaya,
Mariama ta ce” Allah,
Shin baki da labarin ya fi gannin abinda kike aikatawa? Ya fi ki jin abinda ke wakana a tare da ke?
Na sani , ta fada tana kawar da kanta,
Baba tsofo ya ce” shi zai kare ku!
Yana fadin hakan ya yi shiru tamkar ba shi ba,
Da mamaki take dubansa, bata san lokacin da ta dawo facing dinsa ba ta riko hannunsa tana dubansa ta ce” shikenan? Hukuncinsa kennan?
Baba ya yi mata murmushi ya ce ” ke kika halice shi da zaki hukunta shi?
A hankali ta sada kanta, muryarta ne ya yi rauni ta ce” ya cika cin zalinmu, bai san darajar matarsa ba wace take mahaifiya a wajen mu, mu yayansa yakan dauke mu ne ya yi kudin mu, yanzu ya tare da matar da wani ke ziyara a kan idannuwansa, shin yaya ake so dole dole sai na daraja wannan mutun?
Baba tsofo yana dubanta ya sada kansa shima, ya dago ya ce” muna tursasa ki yi masa biyaya ne dan goben ki, kar ki ga duban laifukan da kike hange nasa, idan kika taka hakinsa a kanki na matsayinsa uba a gare ki, Allah ba zai bar ki ba, ki yi masa biyaya, sai ki ga Allah ya jibanci lamuran ki Mariama,
A hankali ta cika hannun Baba tsofo ta juya ta hado goronsa ta kule sauran ta kula a harshen zannin ta,
Miko masa ta yi wanda ta gurzan ta duka gabansa tana dubansa ta ce”ya aka yi mutun mai mutunci irinka ya rayu shi kadai? Ni tunda aka haife ni kai kadai nake gani sai almajiranka wa.inda da sun fara tasawa suke tafiarsu birni neman kudi, ya aka yi baka da mata da yara?
Dubanta yake da mamakin ashe dai ta iya magana, sai dai tambaya ne da Mariama tamkar me, komai so take ta gane ya aka yi ? Ta ina aka bi aka yi? Wa ya yi? Su waye shaida? ????,
Iyayena yaki ya tafi da su,
Na tashi ni daya sai Allahna,
Na yi aure sau biyu a rayuwana, sai dai rashin haihuwa ya saka matan na guduna,
Me ke birge ka a rayuwar wannan daji kai daya kwal da ranka?
Tsareta ya yi da ido kafin ya ce” nan ne muhalin da Allah ya ara min,
Kalonsa take da wani yannayi na tsoro, a hankali ta mike tana dan duban yannayin dakin baba tsofo,
Fitowa ta yi ta hangi anguwar ba wani mutun mai gitawa bukar baba tsofo a tsakiyar rana take sannan nesa da jama.a,
A hankali ta waiwaya bayanta ta tsurawa kofar bukar ido, a ranta ta ayanna ” *Wannan mutun ne ko aljan?*