BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 21 to 30

(????????????‍♀️????????????????????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️)

Rakiyar Aghali aeroport tamkar za.a raka shi tafiar da ba zai dawo ba, 

Idan ma ya yi salama da iyayensa kuma yin salama suke ,

Har aka fara harama kiraye kirayen suna wanda hakan ya saka shi komawa wajen mahaifiyarsa ya dan duka kansa ya ce” Allah ya ja zamanin sarauniyar garin Agadez, sai Allah ya dawo da ni.

Dago da habarsa ta yi tana dubansa ta ce” Allah ya kai ka lafia yarimana, ka gaisar min da aminiyata domin ban lamunci ka sauka hotel ba bayan gata a gari,

Murmushi ya yi mata yana daga mata kansa , kafin ya juya wajen matarsa ya sakarwa yarinyarsa kiss a goshi da kunci, itama matar ya yi mata kiss a goshinta a hankali ya ce” *Tarhanine* (masoyiya)

Dago da kanta ta yi ta dube shi, da dara daran idannuwanta ta yi masa salama kafin take juyawa ta nufi dankareroyar rangrover din su

           Sauka lafia Yarima Aghali .

Yai tunda ta farka a barci ta ahige bayi ta yo wankanta ta fito ta kimtsa jikinta domin ta farka da al.adarta wace ta zo mata tsakiyar dare,

Bayan ta gama ta kuma rufa ta turara turaren wutar da ya zame mata jiki karfi da yaji Ayya ta koyar da ita saka turaran wuta a jikinta da kowani lokaci, barema idan ta fito a wanka sai ta turaru kafin ta bushe,

Sai da ta gama turaruwa ta dawo ta ciro doguwar rigar atampa , jar atampa ce mai adon baki baki a jikinta, An yi mata dinkin mai turmi , saman ya dan rike daidai kirjinta ya yi mata das sai ya bude kasan , ,

A hankali ta zauna saman yar kujerar gaban madubin ta caje gashinta wanda Ayya tace yau za.a kitsa shi, domin ana kitsawa yana warwarewa ne Ayya kuwa tace sai an yi kitso mace ce dole ta yi kitso,

A ranta ta ayanna , ina yake? Ya ya kwana? Har yanzu yana kan bakansa? (Domin rabonta da Mu.azam tun guduwar da ta yi jiya,) yanzu har karfe goma ya gita na safe, tana jin lokacin da Ayya ta shigo take fadin zasu je su dauko Aghali dan aminiyarta , sannan ta ji lokacin da mai aiki ta shigo tana fadin Wardugu ya zo Ayya bata nan, aman ina ita barci ya ci kargfinta domin idan tana al.ada takan yi wani barci mai nauyi ne,

A hankali ta saki murmushi ta kuma furta “Mu.azam nawa ,

Ji ta yi an turo kofarta dan haka ta mike tana duban kofar,

Shigowa ya yi da salama a bakinsa, da sauri ta kai dubanta saman bed dinta, Allah ya so ta abin shinfidar ya rufe pant dinta da ta ciro ta zabi wanda zai riketa da kyau ta saka, bata rigaya ta mayar da sauran ba, 

A hankali ta mayar da dubanta wajensa, kafin murya a sanyaye ta ce” i….i.ina kwana , 

Yauma bai amsata ba, sai kallo da yake binta da shi na mamakin yaushe ta iya saka kaya haka? Yana gannin yan aikin gidansa har kulun su shigarsu tamkar an tsamo su daga rafi, domin Walyn nata daukan yan aiki yan birni sai yan kauye, baya taba gannin sun waye su kulun tamkar mahaukata, shi ya sa koda wasa ya hana su taba wani abin a bangarensa, hakan ya sa ta samo masa namiji mai aikace aikacen bangarensa wanda ta yi ta rantsuwar ba dan daudu bane, shi kuwa dan daudu ne idan ya shigo gidan ne yake namiji! 

A hankali ta karasa ta dauki dan kwalin atampar ta daure gashin kanta da kyar , wanda yake lumbuk gaban goshinta, ta koma gaban madubin ta zauna abinta ta shiga daure gashin kanta, 

Wani irin mamaki ne zai kashe wardugu dake tsaye yana biye da ita da kallo, kai! Ya fada a ransa, ya shigo ne dan ya tambayeta kys din dakin Ayya dan ya san ita zata barwa, sai dai mamakinsa, ya hadu da macen da bata nuna tsoronsa, kakahin ta birge shi, shishigi a gare shi ba, ita bata nuna tana tsoronsa ba , ita bata nuna bata tsoronsa ba, ita dai ta gaishe shi, gaisuwar da ya tsana wai wani *Ina kwana*, sai kace wani sa.anta! 

Yana nan tsaye har ta gama daurin dan kwalin da ya boye baki daya gashin kanta, ta dauki turaren ruwa ta kuma fesawa a jikinta mai sanyin kanshi wanda Ayya ta sayi kwali guda irinsa sunnansa princesse , 

Kwali ta dadage ta saka sannan ta shafa dan man lebe kadan, ,

Mikewa ta yi ta juyo facing dinsa tana dubansa yana dubanta, a hankali ta shiga takawa tana nufo shi, wanda du takunta daya sai ya ji gabansa ya dadage ya fadi , da sauri ya kawar da dubansa a kanta daidai nan ya jiyo muryar Ayya,

Tamkar an hankada shi haka ya fito daga dakinta wanda har ya waiwaya da sauri yana duban kofar, hankali ya furta” innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, abinda Wardugu ya furta kennan kafin yake tura dakin Mu.azam dake kasa kadan da dakunnan su Ayya ya shige ya rufo ya nufi gaban madubi da sauri,

Duban kansa ya tsaya yi, kaki ne a jikinsa, sosai yannayinsa na ban tsoro ya bayana a jikinsa, sai dai kaki din wandon ne kawai sai bakar rigar da ya saka, a fili ya furta” ko dai makauniya ce? 

           ????????????????????????

Ba laifi yau kun yi comment, dan haka ga kari????????????????????????

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        3️⃣8️⃣

Murmushi ya yi bayan ya tabatarwa kansa da yarinyar ba makauniya bace tana gani sosai, 

To aman ayar tambayar shi ne me ya sa bata tsoronsa? Ko ta tsaya ta shagalta a kallon sa kamar yanda du yawancin mata da mata ke yi? Bale ita da ga irin wajen da ta fito wato kauye zai kasance shi ya zama abin kallo a wajenta, sai dai abin mamaki tamkar ba.a yi halitarsa a gabanta ba,

Kansa ya girgiza a fili ya furta” Ayya kwashe kwashe, idan kuma aljana kika kwaso mana ba sai ki huta ba????.

Sai da ya gama abubuwansa sannan ya juya ya fice ya tafi falo domin yana jin hayaniyar samarin biyu da muryar Annarsa.

Agaishat tsam ta yi bayan fitarsa ta sauke ajiyar zuciya, murmushi ya kubuce mata a fili ta furta” idan Mu.azam nawa zai aure ni, cikin abokan ango da zasu zo daukana a rakumi (???????????? ke malama a birni kike????), harda wannan mai kama da mutanen cikin alon nuno mutane (tv), 

Dariya ta yi tana dafe goshinta ta ce” kai aman katoto ne, kuma wai dan Ayya ne????‍♀, ko ta yaya ta goya shi? 

Kys din Ayya ta dauko ta juyo zata fita, ta ja ta tsaya ta dubi wajen da Wardugu ya tsaya ya zuba mata ido, nuna wajen ta yi da hannunta ta ce” kai katoto, ka daina irin kallon nan, baba sofo yace ba kyau irin kallon nan da kake! 

Yatsina fuskarta ta yi , ambaton sunnan baba sofo da ta yi ya sace mata lakar jiki, a hankali ta shiga takawa da zancen zucin ko ya yake? Ya Annarta? Ya yan uwanta? Ko da wasa bata tuna yannayin mahaifinta, sai ta tuna da baba tsofo sau dari bata kawo sunnan Ba a layin zuciyarta ba, tsananin tsoronsa da ya dasa mata ya saka har a zuciyarta idan ta yi kamar ta tuna shi sai ta gargadi kanta cewar ki kula Agaishat kiyayarsa gare ki madaukakiya ce.

Agaishat na saukowa, kanshin turaranta ya fara karasowa, kafin a hankali ta idasa fitowa fallon,

Da murmushi Ayya ke kallon ta, domin ta ji dadin irin yanda yar tata ta koyi saka kaya da wuri haka, 

Mu.azam da ya dago daga hirar da yake yiwa Wardugu ya zuba mata mayatatun idannuwansa , zuciyarsa na luguden kida yana dubanta da wani yannayi mai nuni da ” kin azabtar da ni, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button