BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 21 to 30

Wardugu dake gefensa yana sauraron sa, jin ya yi shiru ya saka shi duba wajen nasa, nan ya bi abinda ya tsurawa ido, ya kai dubansa wajen Aghali da yana tsakar waya da mamansa yana shaida mata ya sauka lafia, aman ya tsaya mamakin wai yarinyar da Ayya ta dauko ce haka? 

Da sauri Wardugu ya mayar da dubansa wajen Mu.azam, shima zuba masa idon ya yi yanai masa kallo mai cike da ma.anoni, 

Salama ta yi , kafin ta zarce wajen Ayya , inda a takaice ta ce” ina kwana………. (wannan na cikin abubuwan da Ayya ta koya mata, cewar ta ringa kiyaye sakin baki, kai ko gaisar da bako zatai ta takaita , in dai ta yi salama cikakiya halas!)

Tana zuwa ta zauna inda Ayya ta nuna mata,

Hannunta Ayya ta kama tana duba faratunnanta , domin ta umarce ta da sakawa yatsutsanta jan lale,

Ta kuwa saka , ya kama yai mata das a hannun , 

Ayya ta saki hannun ta lakaci kuncinta, kafin ta yi kiran Hanne, kan ta kawowa yarinyarta abin kari,

Kai Wardugu ya girgiza, ya mike yana daukan wayarsa ya kai dubansa wajen samarin dan ya ankarar da su , da haushi haushi ya ce” ni zan tafi,

Da sauri Aghali ya mike yana fadin” zamu tafi dai oga,

Wardugu ya ce” a mashin fa nake Aghali,

Aghali ya dafe kansa, ya kai duban sa wajen Mu.azam ya ce” docter tashi mu je ka kai ni ,

Mu.azam ya dubo su, irin yanda Wardugu ya yi kicin kicin da fuska ya san ko sun bi shi walahi zai bace masu ne, dan haka ya ce” ni sai na karya,

Idan kana so ka karye! Wardugu ya fada ya juya yana fadin” premiere dame (First lady, wato Ayyarsa), sai na dawo ,

Ayya ta amsa shi da” ka dawo lafia *War*,

Haka ya fice a gidan cike da takaicin girman kan yarinyar, domin shi kawai ya ajiye haka a matsayin girman kai, wai su *Ashak* ko? Ba buzuwa ba dai, su waye ma su buzayen nan da suka raina mutane har suke yiwa mutane Ashak? 

Sosai ya kunsa a lamarin Agaishat ya bashi mamaki, wanda hakan ya saka ya dauki aniyar nazartarta a tsanake, shi zai koya mata ladabi da biyaya a haukace! (Toh fa),

Kuka take na tashin hankali tun da ta shiga bayin da kamar minti biyar, da gudu ta fito ta mikowa mamanta abinda ta yi gwajin fitsarin nata dan gannin ko ciki ne da ita? Domin tunda Wardugu ya yi maganar komai nata ya tsaya ya daina aiki,

Da yannayin farin ciki uwar ke dubanta, ta ce” kukan murna kike ko na me Walyn??

Da madaukakin tashin hankali ta ce” ba zan haihu yanzu ba, bana son cikin nan walahi sai an zubar da shi, bana so! 

Da mamaki uwar ta mike tana dubanta, kafin take nunota da yatsa ta ce” ke ke ke, da hankalin ki kuwa? 

Walyn ta dan tsagaita kukanta ta dubi uwar, kafin take kara barkewa da wani kukan ta ce” ba zan yarda na dauki ciki da Wardugu a wannan lokacin ba, a bai tabatar ina da ciki bama ya yi min rantsuwar sai ya yi mini kishiya ina da ya gane ina dauke da ciki? 

La haula wala kuwata ila bilah, maman Walyn ta fada, ke bashi da hankali? Yaushe ma aka yi auren da har ya fara yi maki maganar zai maki kishiya? Me kikai masa da zafi? Ki bakya barinsa zuwa wajen ki yanda ya dace?, fada mani me ki kai masa da zafi haka?

Nan walyn ta warwarewa mahaifiyarta yanda suka yi da Wardugu,

Haushi kamar uwar zata dake ta ta ce” yaushe zaki gane mahaukaci ki ke aure ki iya takun ki da iya zama da shi?

Da sauri Walyn ta ce” Ma, Wardugu ba mahaukaci bane !

Uwar ta yatsina fuska tana dubanta ta ce” toh dan uban ki ba mahaukacin bane, aman wannan cikin ko aman jini kike sai kin haife shi kin sama mana magaji, ke ko me zaki yi sai kin kawo shi duniya, bara ma ki ga na fada masa, ai shi kina tsoron sa tamkar ran ki! banza sakarya marar tunani!…..

Rigima ta kirki suka kwasa kafin da kyar ta samu ta zaunar da ita ta ce” Walyn , kina bani kunya a rayuwa, wani lokacin har kokonto nake ko dai an canza min ke a asibiti ne? Ina yi bakin kokarina dan gannin kin yi fice a gidan ki aman a kulun sai da hadu da abin takaici abin mamakin da zai saka ni jin kunya,

Matar Batube, ta kasance tamkar abinda ya malaka kwalin kwal a duniya, wanda tamkar numfashinsa ne, yana ririta ta, yana kulawa da lamarin ta kafin na kowa, na sani ci sha sutura kilacewa, kayan burga ba wanda baki da, matsalar daya ne baki isa ki saka mijin ki ko ki hana shi ba! Menene dalilin haka? Na kasa ganewa, na kasa ganewa walyn,

Walyn dake zaune du ta hade jikinta, a ranta kuwa ayannawa take ko da jaraba sai ta zubar da wani tsinanan ciki, a haka ma tana cas cas dinta yanai mata maganar kishiya, ina da ta haife? Bama zai yiwu ba, idan ta haifi guda ai ta kama hanya, kofa ta budu, sauran zasu zo ko fa balaki ne, kennan shikenan kishiya ta tabata a gare ta ? Duda tana tsoron lamarin wardugu, ya yi aure haka ba tare da ya cika al.ada ba ba damunsa zai yi ba, tsohuwar uwarsa kuwa ba tirsasa shi zatai ba!

       Mrning alll

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        3️⃣9️⃣

*baki ba zai iya misalta maku irin yanda zuciya ke cike da farin cikin karanta ku Bak’a fans, Allah ya bar kauna baki daya*

Ya Allah, kar ka kai labarin mutuwarmu zuwa kunnen da baki ba zai fadi alkhairi kan gawarmu ba ????????????????????????????????????

Haka Walyn ta wuni wajen mahaifiyarta , inda uwar ke kwatanta mata yanda zata yi ta ci ribar zama da wardugu, ita kuwa tana tsara yanda zata rabu da ciki! 

Tana komawa gidanta ta zauna falo, ko kayan bata iya cirewa ba tsabar tana cikin tashin hankali, fatar jikinta kuwa du ta yi ja abinka da jan mutun,

Tv ta kunna ta kamo tashar labaru, 

An yi sa.a kuwa ana watso labarun su Aisata kan an yi bincike har an fara cafko masu shigo da kwayar, inda alkali zai yanke masu hukunci, , nan aka hasko sunnanta baro baro hade da sunnan mahaifin wardugu, aka fadi cewar ta bada hadin kai wajen kamo wasu masu harkar dan haka zata samu sasauci kan hukuncin da aka yanke mata,

Tsaki ta ja ta kashe tv din ta mike nan ta shiga baci domin ji take tamkar idannuwanta na dauke da yaji ne dan tsabar nauyin da su kai mata.

Wardugu na tsaka da aikinsa aka shigo aka shaida masa Marahut na son ganninsa, a shigo da shi ko kuwa?

Wardugu ya dafe goshinsa, a ransa ya ayanna me ke damun Elhaj Marahut ne da zai mayar min da office wajen zuwa haka?

Umarnin a shigo da shi ya bayar , ya ci gaba da aiyukansa yana hada takardun wasu yan gudun hijira ne da aka kamo , ya duduba da kyau ya ga du yawanci yan libia italia da dai sauran su, yana son mika su hannun likitoci a duba lafiarsu kafin su yi masu takardun tafia su juya garuruwan su!

Shigowa Marahut ya yi ya zo ya zauna saman kujerar zaman mutun daya yana duban Wardugu,

Kai shima yana alfahari da namijin yaron nasa, suna mugun kama aman ko a zamanin da yana saurayo bai kai Wardugu tsayi da yannayin karfi da cikowa irin nasa haka ba,

Murmushi ya yi masa ya miko masa hannu ya ce” Asalamu alaika Wardugu

Dago da kansa ya yi , a nitse ya miko masa hannun shima ya amsa da” amine wa.alaika salam *Elhaj Marahut*.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button