BAK’A CE Page 21 to 30

Murmushi ya kuma yi ya rike hannun na wardugu, sam baya son sakin hannun, rabonsa da rike hannun yaron har ya manta,
Da ido Wardugu ya yi masa nuni da ya cika shi mana?
Sakin hannun ya yi , a nitse ya ce” Wardugu sunana kake kamawa haka ko?
Wardugu ya dube shi, ya yi masa murmushi ya mayar da dubansa kan takardarsa,
Ka saka baki wajen alkalin nan ya sasauta mata hukuncin da ya dauka a kanta, kaso har na shekara biyar ya yi tsauri Wardugu,
Wardugu ya dago yana dubansa , ya ce” ka san ba hurumina bane, sannan bana saka hanuna a irin haka, kaima ai kana da hanyar hanata yin kason ma domin ka fi ni fada a ji a wajen su,
Wardugu sunana zai bace Wardugu, sannan hakinta a kaina yake! Marahut ya fada yana dubansa da yannayin iya gaskiyarsa kennan
Wardugu ya ce” ni nawa sunnan sai na kai na dulmiya ko? Ah koda yake daman sunana a bace yake a bakin al.umar da suka aikata laifi, sai ya yi ta baci jar a bakin wa.inda basu taka dokar bama?
Marahut ya dafe goshinsa, ransa ya fara baci ya ce” har sai yaushe zaka daina mugun fushin nan a kaina? Ni fa na haife ka! Baka tsoron goben ka? Kai idan naka suka ki yi maka biyaya fa? Wardugu ba laifina bane abinda ya faru a baya ,
Wardugu ya dube shi ido cikin ido ya ce” wannan tsohuwar magana ce Marahut, kana iya tafia ba zan saka bakina a maganar iyalinka ba!
Wardugu! Ya fada da dan karfi yana mikewa,
Wardugu ma ya mike ya ce” Marahut!
Marahut ya tsura masa ido, a hankali ya ce” dan na kula wata, na aureta , ba laifina bane, laifin uwarka ne! Sannan dalilin halayan da na gane nata na rabu fa ita yanzu,
Wardugu ya hadiye abinda ya tsaya masa a wuya, ya karya kansa ya ce” sai dai yanzu Wardugu bashi da budurwa bare ka kwace,
Marahut ya daga hannunsa ya zabga masa mari wanda ya yi mugun kara kara, ji kake tas, ya maya masa a gefen kuncinsa wanda hakan ya sa hularsa dagawa,
Kan Wardugu a kasa a hankali ya dago jajayen idannuwansa ya sauke a fuskar mahaifinsa, Mahaifinsa, ubansa, wanda ya haife shi, a yau ya so a ce wani ne ya kai hannunsa jikinsa, kai kai kai, balaki,
Ido cikin ido suke duban juna, Marahut ya ce” ko me ka zama, ko me kake takama da shi dai haihuwarka aka yi, na yi tunanin rashin mutuncin naka zai saka ka daga hannu ka rama! Ka rama marin mana Wardugu!
Wardugu ya sakar masa murmushi mai ciwo , a hankali ya ce” ko shege mai mutunci ba zai rama ba bare kai da ka haifi dan halal ka bashi tarbiya?, kar ka daga murya yarana su ji, domin ban san in zan iya rike kowa, wai ina gudun ba nan gaban idona ba, ka san soja shegen yawo ne da shi, gashi da ramuwar gaya,
Ka je kawai Marahut.
Jikin Marahut ne ya yi sanyi, ji yake dama da hali da ya rungume shi ya shafa wajen da ya mare shi ya bashi hakuri,
A hankali zuciyarsa ke sauka har ya ji dumbin kaunar dan ta kuma mamaye khalbinsa bashi da wani , baya tunanin zai samu daga shi, fatansa su sauko daga dokin zuciyar da suka hau bisa gangancinsa, sai dai ya rasa yaya zai yi, shi ba zai duka gabansu ya basu hakuri dan ya kara aure ba, su ya dace su yi hankali su zubar da makaman yakin su, yanzuma ba wai ya zo ne dan Wardugu ya yi magana harkar Aisata ba, shima yana iya sakawa a saketa aman ya barta ta je ta yi kasonta kawai domin ta taka doka, ciki harda ta musulunci , da aurensa a kanta take bin wasu mazan.
Ya zo me dan ya kara ganninsa su sami hira ta kusanci na da da uba, sai dai ga yanda ta kare,
A hankali ya juya dan barin Office din,
Ja ya yi ya tsaya, a hankali ya dawo ya dube shi, hularsa da ta dage ya janyo ya gyara masa a kansa, ya gyara masa gaban rigarsa da kyau ya ce” Allah ya yi maka albarka, na yafe maka dukan abinda ka yi min wanda na sani da wanda ban sani ba, Allah ya kare gabanka da bayanka!
Yana gama fadar haka ya juya ya fice a office din,
Ran Wardugu a cakule ya hade takardun ya fito gaba dayansa a haukace ya mikawa Lieutenan Jalo takardun bai masa magana ba yana kallon mashin dinsa ya fice ya bar shi a wajen aikin ya kama tafia a kafarsa cikin sauri, ya yi niya a kafa zai je gidansa ba zai hau mota ko mashin ba, ya ki din , kai bama zai kuma hawa ba! Zai je a kafarsa , du wanda ya fasa kawo masa wargi ya ki Allah! (???? wani da laifi , wani da shan duka? Tap????),
Bayan kwana biyu, fitina ta dan lafa gefen Wardugu,
Juma.a ce yau, ranar da ake bada damar shiga gannin yan gidan kaso harma a dan jima a wajen su,
A wannan ranar ne mutane ke cika prison dan gannin nasu,
Wannan damar Walyn ta rike ta yi shiga irin ta larabawa ta yane kanta da dan kwalin bakar abayar da ta saka ta yane har habarta sannan ta saka bakin gilas,
A kafa ta samu ta fito bakin titi nan ta ja ta tsayar da mai taxi ta yi shatar ita daya.
Basu zame ko.ina ba sai justice ta ciri takardar gannin dan prison ya dauketa ya sadata da gidan kason,
A hankali ta cire gilas din idonta, sannan ta dan ja mayafin dan bude habarta dan kar ta jawa kanta matsala da masu tsaron gidan kason
Takarda ta nuna, ta je saman kuje ta zauna inda aka shiga aka kirawo mata wanda ta zo nema,
A hankali take takowa har ta karaso wajen warda aka nuna mata a matsayin uta ke nemanta,
Kallonta take, irin kallon san sannin wacece? Hakan ya sa Walyn ta bude rufarta dan ta shaida ta,
Murmushi Aisata ta yi tana dubanta, aman a kasan zuciyarta mugun kishin Walyn take, kai da tana da dama da ita ce ajalin yarinyar da ta auri gwarzonta!
Walyn ta kare mata kallo sama da kasa, cike da yanka da jan aji ta ce” *wanene shi*?
Bata amsa ba , sai da girarta irin na rikakun yan duniya da suka san kansu ta yi mata tambayar *Wane?*
Walyn ta fara shaka ta dubeta da kyau ta ce” *waye malamin da ya miki aiki kan Wardugu da mahaifinsa?* waye shi?, idan kika fada mani komai, zan saka a fitar da ke daga wajen nan.
Murmushin rainin hankali ta yi tana dubanta, cikin kissa ta ce” kina da damar sakawa a fitar da ni din ne kika shigo cikin gidan kaso dan samu adress din malamina?
Kina son samun kanki ne a wajen Gwarzona?
………
Share this
[ad_2]