BAK’A CE Page 21 to 30

Tuki yake zuciyarsa kuwa sai adu.a yake, Agaishat ma adu.ar kawai take inda Ayya ke kara buga lambar wardugu aman a kashe, bata shigama bale a dauka,
Danja na tsayar da su aka haske su da cocila dall a idannuwansu,, gaba da baya sojoji suka zagaye su har mutun uku,
Na kusa da direba ne ya kwonkwasa kofa,
Mu.azam ya bude yana dubansa,
Mutumen ya ce” motar Gn ce Oga,
Ya ce” eh na gane ai,
Ya ce” malan daga ina , kuma ina zaka je? Wa ka dauko? Sannan ka bude mana bayan mota zamu yi bincike,
Mu.azam ya fara bude masu motar, sannan cikin nutsuwa ya ce” ina tare da mamanmu ne, mahaifiyar Wardugu da kanwarmu Agaishat sai ni kuma amininsa ne, daga gida muka fito zamu je gida wajensa bisa umarnin mamansa,
Menene shaidarka? Sojan ya tambaya ba alamun wasa,
Mu.azam ya mika masa cartocinsa, sannan ya sauke madubin bayan ya dayan ya leka wajen Ayya,
Kwarai kuwa itace, waye bai san Ayya ba? Mahaifiyar General,
Gaishe da ita ya yi cikin mutuntawa ya ce” yi hakuri mama muna bisa aikin mu ne, ki tabatar mana da abinda ya fada,
Ayya ta ce” eh haka ne, ina son gannin Wardugu me yanzu yanzu,
Sojan ya gyada kai yana kallonta,
Wanda ke bincika cikin motar ya shaida masu ba komai cikin motar, dan haka ya mika masa takardarsa ya basu damar su fice
Cikin ikon Allah haka sukai ta haduwa da sojojin nan suna kara titsiye su ,
Harda wanda bayan dukan bayannan nan yace ai shi bai wani san Ayyar ba a bashi shaidar da ta fi haka,
Nan fa aka sha rigima da kyar masu taya shi suka tsawatar masa ya batsu suka tafi,
Tun abin karfe tara sai kusan sha daya suka karasa gidan Wardugu nanma suka tarar da wani balakin an hana iyayen Walyn fita sai dai su kwana a nan in kuwa suka fita aka kama su toh su suka gano, sun izata sai balaki take kan wardugu ya fito ya raka su ko ya basu shaidar da zata sakasu su tafi har gida lafia,
Suma su Mu.azam sai da aka titsiye su kafin suke samun shiga gidan,
Mu.azam na tsayawa ya sauke ajiyar zuciya yana kallon hajia rigima, domin Ayya ta hade rai ta yi kicin kicin da fuska tana kallon yanda suke tsatsaye suna ta magana suna tafa hannu suna balaki,
Mu.azam ya ce” Ayya, kar ki kula koya na roke ki,
Ayya ta yi murmushi ta ce” oh yarona, yanzu kai ke yi min gargadin kar na kula kowa, ai ka san bana kula mutumen da bai iya tsawatarwa zuciyarsa ba!
Bude motar ta yi ta sauka,
Ai kuwa tunkarar wajensu ta yi direct ba wani tsaye tsaye,
Tana zuwa ta ja ta tsaya itama tana yi masu kallon da suke mata,
Da yake akoy wuta ko.ina haske ya garwaye gidan kowa na gannin kowa ne,
Ayya bata fita sai ta shirya ko fitar da a rikice take ne, dan haka yanzuma sai baza kanshi take, ga lufayarta ta nada mai ruwan ja da baki, ta sha awarwarenta na zinariya,
Walyn ce ta ce” ina yini,
Ayya ta kai dubanta wajenta ta ce” lafia, sannan ta mayar da dubanta wajen iyayen Walyn din tanai masu kallon ido cikin ido,
Mahaifiyar walyn ta miko mata hannu ta ce” Hajaju ne, uwar gidan *MARAHUT* ke ce da tsakiyar daren nan??
Ayya ta sakar mata murmushi ta mika mata hannun itama ta ce” wa.alaiki salam maman Walyn, ke ce a gidan Wardugu da wurin nan haka,
Kanwar maman Walyn ta kali Walyn ta kuma kallon sirikan biyu, ta juya bangaren Walyn tana ayyana taf, lale ana cakwakiya a gidan nan,
Ita kuwa walyn kitson kanta kawai take sosawa, susar da bata san ko ta meye ba,
Ayya ce ta fara cika hannunta ta kuma kallon Walyn ta ce” Aa, Walyn yaron nan yana nan ne dai ko? Bara na shiga na gani Wardugu sarkin aiki!
Juyawa ta yi ta nufi bangaren Wardugun cike da isa, sai a lokacin Mu.azam ya lalaba Agaishat ya cire mata tsoro suka fito daga motar,
Mu.azam ruwan sanyi sai ya nufi wajen su dan gaishe su,
Walyn ta daga ta watsar da idannuwanta sannan ta zabgawa Agaishat wata muguwar Harara da kallon kyama ta juya tana riko hannun mamanta suka koma bangarenta,
Agaishat dake dafe da kirjinta jin yanda zuciyarta ke dokawa Mu.azam ya kallo,
Murmushi ya sakar mata ya ce” mu je Matar Mu.azam,
Ido ta zaro kafin take daga kafa da sauri ta yi gaba tana jin wata kunya kunya da wani irin abu game da Mu.azam din, yakan mantar da ita wacece ita ta halin nuna mata itama mutun ce mai cike da cikeken inci, yana yaba kalar fatar jikinta ta hanya kawatata da kalamai masu tsari da sence, yakan ce Allah ya datar da shi samunta, ita Agaishat yar gidan Sofo? Tana so ta biye masa tana tsoron ko wasa yake mata? Tana son ta yarda tana tsoron yan birni,
Ayya na shiga ta zarce har dakinsa na baci tana fadin” ina kake janyau, ka hargitsa mana gari ka lafe a gado, tashi tashi kaima ka yi kwanan zaune dan nema kawai!
Da wani irin sauri ya mike ya diro ya warci doguwar rigarsa yana faman sakawa ta shiga dakin,
Wardugu ya ce” Ayya, wai yaushe zaki dauna shigo min haka zaraf kawai? Me ya fito da ke a tsohon faren nan? Ya aka yi kika ratso sojawan hanyar nan? Wa ya kawo ki?
Maimakun Ayya ta bashi amsa sai cewa ta yi” baka da sutura a jikinka ne kake kwonciya Wardugu?
Wardugu ya dafe kansa ya furrta” Ya Allah,
Bakinta ta yatsina ta ce” fito ina jiranka
Sai da ya saka kayansa ya biyo bayanta,
Yana fitowa ya ga Mu.azam, da bakuwar nan ta ayya da shi ba zai iya fadin sunnanta ba dan bai wani rike ba,
Sai dai mamaki yake, yanzuma wasu kayan ne jikinta, shi abinda ke bashi mamaki yaushe ta iya saka kayan tubawa har yake bin jikinta haka? Yaushe ta iya saka kayan kansa nema ?
Kawar da kansa ya yi da sauri yana yatsina bakinsa yana ayyana ina ruwanka yo, ba dai Ayya ta daure mata ba?
Ayya ta karbi kulin maganinta ta umarci agaishat da ta bude frij dake nan falon ta fauko ruwan roba
Agaishat ta nufi frij tana tambayar kanta ina wajen budewar yake? Domin ba irin na gidan Ayya bane, wannan wani glass nema a jikinsa ko.ina tar tar yake ana hangen abubuwan dake ciki tar sai dai ba lale ka san wajen kunawarsa ba,
Ja ta yi ta tsaya tana kallo,
Ayya dake jira ta kallo wajenta ta ce” Agaishta kawo mana,
Agaishat ta juyo tana raraba idannu ta ce” Ayya, ina zan bude??
Wardugu ya girgiza kansa, Mu.azam ya mike ya je ya nuna mata ya bude mata, ta nuna masa wanda take tunanin ruwan ne?
Mu.azam ya ce mata” wannan ai jus ne, gidansa da kamarsa yake yannayin ruwa, aman kin ga jerin ruwan nan,
Nan ta dauko suka dawo wajen Ayya dake ta yiwa Wardugu fadan ya kwonta bai ci abinci ba dan ba sai ta tambaya ba ta sani ne kwonciyarsa zai yi, aman kwata kwata bata sako maganar matarsa ba ko iyayenta, bata da wannan lokacin,
Wardugu dai kallonta yake, ta bude ruwa ta tsiyaye fiye da rabi ta zuba maganin ta girgiza ta mika masa ta ce” shanye,
Wardugu ya cee” Ayya meye kuma wannan
?
Ayya ta ce” Wardugu, magannin baki ne, bakin mutane, ka san baki fa ya fi maye mugunta, baki ai ba dan uwa bane, bare yau ka janyowa kanka maganar mutane
Robar ya rike a hannunsa ya ce” Ayya, bayan walahaulan da nake yi kuma dai kin bani wannan jike jiken naki?
Ayya ta ce” walahaula hanyarta daban, wannan ma nasa daban, kai harda garin hantiti nake tafe, maza shanye ka dauko min buta a bayinka na zuba maka ka yo wanka ka turaru sai mu juya,
Ido ya zaro yana kallonta, kafin ya maido dubansa wajen Mu.azam da irin kallon kai ka kawota ko?
Mu.azam ya juyar da kai wajen Agaishat dake zaune kasa yana kallonta, domin kallonta na saka shi nishadi