BAK’A CE Page 21 to 30

???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣8️⃣
Bani da bakin da zan yi godiya a irin tarin kulawar da kuka nuna, da tashin hankalin da kuka nuna na wannan abin da ya faru, kunya ta kama ni, na ji kunyarku sosai na irin hada ni da Allah da kuka yi, wacece ni? Ni ba kowa bace da zan ki yin hakuri dan haka nake shaida maku ga *BAK’A* . Daga taku yar mutan niger
Kun yi sake , kuna gani tana zuwa ta shige dan ta samu ganninsa aman mu tun da yama muke zaune, a matsayin mu na iyayen matarsa yace ya gaji ba zai fito ba, kina ganni da takama bayan ta fada mana magana ta shige abinta,
Auntyn Walyn ke fada ranta na kara baci,
Mahaifiyar Walyn ta ja tsaki , ta ce” koma me take takama da shi ai mijin ya nuna mata iyakarta, yanzu ba da kishiyarta bace yaronta ke fada? Banza ita har ta isa ta nuna ita wata ce? Bayan an ci mata mutunci kowa ya sani?
Walyn dake zaune, gaba daya zuciyarta ke wani irin tashi, ta rasa me ke damunta kwanakin nan takan tsinci kanta a irin yannayin rashin jin dadin jiki, bata iya kara furta masu komai ba ta mike ta je dan ta saka a kara tsaftace masu wajen da zasu kwana, domin ba zata lamunci a rufe iyayenta ba, za.a samu matsala sosai,
Sai da aka sha rigima da Wardugu ya shiga wankan hantitin da Ayya ta jika a butarsa ta karfe,
Yana yin wankan ya fito yana jin yanda yake warin magannin, sai dai yana fitowa ta kuma tare shi da hayakin Hantitin nan yana ta bade shi ,
Jajayen idannuwansa kawai yake binta da su, in ba Ayya ba, wannan uwar gajiyar da ya kwaso ta zo ta tirke shi da wannan abubuwan? ,
Tana gamawa ta fita fallo da hayakin bayan ta debo turaren wutar dake jere saman coiffeuse din dakin tana tafe tana dan sakawa yana tashi a hankali,
Kansa kawai ya girgiza, ya cire jalabiyarsa ya saka rigarsa mai karamin hannun wace ta baiwa jikinsa damar bayanna ya saka wandonsa dogo fari na jalabiya saman gajeran ya fito,
Ayya dake kallon Tv, Mu.azam kuwa sai wani kara shigewa Agaishat yake yanai mata labari kasa kasa, wanin ta zaro dara daran idannuwanta, wanin ta dan yi murmushi, wanin kuwa sai dai ta rufe fuskarta da hannayenta wai kunya take ji,
Galala ya yi yana kallon kusancinsu da kuma yannayin su,
Ayya ce ta juyo wajensa , sai dai ranta ne ya baci gannin irin rigar da ya fito da ita, ita kam ya zatai da wannan sakarar dabi.a ta wardugu ta saka kannanun kaya? Sam ba al.adar batuben mutun bace, Batuben mutun yanda mace zata ji kunyar bayannar da jikinta haka shima namijin, sun fi saka manyan kaya sukan yi rawani ko su aza hula saman kansu, suna saka kananun kaya irin na zama aman dogon wando har kasa, riga mai mutunci su yi zanzaro abinsu, aman fa siri batube sai mata nai, shi ya saka take mamakin Wardugu, gatsai gatsai sai ya bi gari da wando daidai gwuiwa, riga mai yankeken hannu har yana wata takama,
Rai bace da yaren tubanci ta ce” Wardugu ! Nigey medi nubazzu ? Ay kubu nukoy ? Anna gnuduro indi hadin ? ( Wardu! damme bakajin magana , wannan wane irin rigane ? Idan mutane suka ganka me zakace?),
Wardugu ya kalli rigar jikin nasa, kansa ya shafa wanda haka kamar ya zame masa jiki, ya juya ya sako wata riga a saman wannan duda haka bai bala boturanta ba,
Yana dawowa ya zauna yana kallon Ayya,
Ayya ta girgirza kai ta ce” a gaskiya wannan abin sam bai yi ba, kai ba wani karamar kira ba , ka wani saka kananun kaya, yanzu haka a haka sirikanka suka ganka wardugu? Salon a fita da kai a baki ko?
Wardugu ya lumshe idannuwansa ya bude ya ce” basu ganni ba,
Me kake nufi da basu ganka ba?,
Wardugu ya daga kafada ya ce” ai na gaji ne, sai idan na huta Ayya,
Da kallo take binsa, a sanninta yana matukar jin kunyar iyayen matarsa yana darajasu, ko dan irin yanda sirikan namiji keda matukar daraja wajen mijin yarsu a al.adun tubawa, domin kuwa suna da dama sosai a kan mijin yarsu, aman yau yace wai ya gaji bai je ya gaisar da su ba? Ta so ta tsawatar sai kawai ta kyale, domin dai Walyn da Wardugu auren so suka yi, shi bai taba kawo mata karar matarsa ba, itama bata taba kawo masa karar rashin girmamata da Walyn bata yi ba, ai ido ba ma.auni bane abin duba ne, yana gani kuma yana sane, dan haka ta watsar ta mike tana duban Agaishat ta ce” ku tashi mu tafi kar mu kwana a gidan nan kun ji?
Wardugu ya kaleta yana talabe habarsa, ya ce” Ayya, ai yau sai dai ki yi hakuri da gorin wai kin zo gidana, yau kwana ma zaki yi Ayyar wardugu,
Ayya ta zaro ido tana kallonsa, ta ce” kai, ka rufamini asiri, ni na kwana a gidanka wardugu? Aa aa, ka tashi ka mayar da mu da kanka man,
Wardugu ya dubi Mu.azam ya ce” kai, zaka bado hankalinka nan ne? Bakin karfe dayan dare dokar ba wani karbar uzuri, motocin yan tafiya kawai za.a bari su je masaukinsu, suma sai dai su waye a can, ba zai yiwu ni na karta dokarnan ba Mu.azam zaka saka baki ko sai na …
Mu.azam ya taso yana dariya ya ce” Ayya, karfe daya saura kadan, ki yi hakuri, mutuncinki, girmanki ya fi karfin ki je cel Ayyarmu, kuma ke ke fadin ya yi aikinsa tsakani da Allah a rayuwa, ki yi hakuri Ayya,
Ayya ta yi shiru tana kallonsu,
Dubanta ta kai wajen Agaishat, ta maido wajen Wardugu,
Kanta ta girgiza ta mike ta karaso wajen Agaishat ta kama hannunta ta ce” tashi mu je bangaren mata,
Agaishat ta mike tana biye da Ayya,
Mu.azam ya dan yi taku dan raka su Wardugu ya riko hannunsa,
Mu.azam ya dawo da baya ya ce” namiji, bangaren Walyn fa zasu je?
Wardugu ya ce” eh na gani,
Mu.azam ya ce” anya kuwa za.a kwashe lafia?
Wardugu ya yi murmushi, ya maida dubansa wajen Mu.azam da kyau, kallonsa yake yana karantarsa,
A nitse ya ce” me ke damunka da ita? Batai maka kankanta ba? Me ke jan ra.ayinka wajenta? Ko bakin nata?
Mu.azan ya dago da sauri yana kallonsa, Wardugu, yanzu mutun yanzu ba mutun ba,
Mu.azam ya ce” ban gane maganarka ba,
…….
……………………
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣9️⃣
Wardugu ya shiga dan shafa sajensa, ya gyada kai ya mike yana dan nuna alamun zan kamaka ne ya yi ciki abinsa
Mu.azam ya bishi da kallo, ya maida kansa yana duban wajen kananun fitilu fararen dake kara kawata dakin,
Murmushi ya yi shima ya lunshe ido a ransa yake ayanna zan so na rayu da ita koda na yini daya ne
Ayya na zuwa bangaren Walyn ta yi salama , ba wani hayaniya ko nuna isa ta ita mahaifiyar mai gidan ta samu waje ta zauna tana duban Walyn ta ce” Walyn muna son daki ni da y’ata , muma kwanan gidanki yau ya kama mu,
Walyn ta mike ta nufi wani dakin ba tare da ta ce komai ba, inda mahaifiyarta kuwa sai ta fara hura hanci ance gidan yarta,