BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 21 to 30

Bata jima ba ta dawo ta ce” ga dakin an gyara Ayya,

Ayya ta mike Agaishatma ta mike suka nufi dakin da aka nuna masu

Suna zuwa Agaishat bayi ta nufa ta dauro alwallah,

Da nadin nan nata ta shinfida darduma ta tayar da sallar nafila domin dare ya yi sosai ya raba, ita kuwa yanzun ta zame mata jiki sai ta yita take iya rintsawa komai dare,

Kuri dai suke zaune suna kallon juna kowa da kudirinsa a kan dan uwansa, ita auntyn walyn mamaki take ashe wardugu har mahaifiyarsa, yo har mahaifiyarsa mana gashi itama dole ta kwana a gidan?

Dare ya raba , karfe biyu da rabi yayi aman wardugu ya kasa rintsawa,

A hankali yake sando ya sauka daga bed din domin nan Mu.azam ya zo ya kwonta bayan sun sha rigimar ba zai kwanar masa a gado ba yace shi kuwa nan zai kwonta,

Yana kokarin fita ya ji muryar mu.azam ya ce” ina zaka je?

Wardugu ya juyo da sauri, ganninsa zaune dare dare saman bed din ya saka shi zabga masa harara ya ja tsaki ya ce” matarka ce ni da zaka wani motsa dan na motsa? Wajen Walyn zan tafi

Mu.azam ya zaro ido ya ce” aman Wardugu baka da mutunci, wajen Walyn fa kace, bayan ka garza rashin mutuncin nan idan walyn ta kaleka komai jarabarka lale lale bata da zuciya! 

Wardugu ya kama haba irin mamakin nan, ya ce” kai aman baka da mutunci, ohk dare ya raba kowa ya samu nutsuwa yana shara baci ni ina nan juye juye sai ta ki kulani dan na bata mata? Da a yau da asuba zan kara aure walahi talahi a masalaci! 

Mu.azam ya zaro ido yana kallo Wardugu ya fice a dakin yana wata irin tafiya na ya kumsa masa haushi,

Kai ya girgiza ya koma kwonciyarsa

Wardugu na shiga bangaren ya tarar da su still nan saman kujeru, Walyn sai gyangyadi take, mahaifiyarta ta fara bacin itama , auntyn kuwa sai dan kada kafa take ,

Dakewa ya yi abinsa ya dan yi gyaran murya irin bai ahigo din nan ba, kafin yake yin salama ciki ciki ya shigo gaba dayansa

Su duka farkawa suka yi, yanzunma ya cire rigar ta sama sai mai karamin hannun hakan ya sa iyayen Walyn din saurin kawar da kansu,

Da idonsa ya yi mata magana, da idonsa ya isar mata da sakonsa kafin yake juyawa ya koma bangarensa,

Yana fita kasa kasa maman Walyn tace” Walyn, mijinki abubuwan da ya tara suna da yawa fa, shi ne rashin mutunci, shine fada, shine rashin kunya! 

Walyn ta lumshe idannuwanta ta mike ta nufi kofa bata ce da ita komai ba

Auntyn walyn da ta kume da haushi itama bata furta su ci kansu ba ta kawar da kanta tana dan kada kafa , niya ne ta yi yau ba zata yi baci a gidan Walyn ba! 

Walyn na zuwa ta yi niyar nufa dakinsa sai dai ji ta yi ya riko hannunta ba tare da ya yi mata magana ba sun nufi dakinsa,

Suna shiga ya shiga kokarin janye zip din doguwar rigarta ta atampa,

Tana tsaye tana kallonsa ya janye ya cire mata tana kallo yake kokarin janta bayi domin mafi yawancin lokuta haka ne ida zai sadu da ita sai sun je sun salo wanka kafin yake baje kolinsa,

Ja ta yi ta tsaya tana dubansa, kwarai ta so ta kiye masa sai dai ba zata manta wani lokaci da ta ki karbarsa ba irin yanda suka kwashi tsayin lokaci yana daure mata ba shi ba ita a harkar har sai da ta yi ta fama kafin ya sauko,

Rai a dan dagule ta nuna ai ita ba sai ta yi wanka ba,

Wardugu ya yi kalar tausayi ya ce” walyn wardugu, me yasa ba sai kin yi wanka ba? Kinga jiki da danshi danshi ya fi dadi tabawa????,

Kanta ta juyar ta shiga kokarin hana kanta garza masa rashin mutunci, a sama take kwarai take tausar kanta kar ta saki hanya ta hanyar karta masa rashin mutunci,

Binsa ta yi suka yo wankan,

Suna fitowa ya jata saman bed domin shima yana so ya yi ya jishi ya saku,

Da sauri sauri ya shiga romancing dinta, sai dai ya lura bata bashi hadin kai domin sai dan zile masa take, hakan ya saka shima ya zo mata kawai kai tsaye wanda hakan na wahalar da ita ainun, idan a dadi suke yakan bita a slow da dabaru ne aman yanzun shima sai ya je ya darza son ransa,

Yana samun nutsuwa ta shiga tura shi, 

A hankali ya dagata yana duban yannayinta

Rai bace ta ce” sai yanzu ka san da anfanina ko? Bayan ka gama wulakantar da ni da iyayena? Wardugu yaushe zan yi daraja a idannuwanka? Yaushe zaka daina wulakantani kai tsaye ? Dan ana fadin kai rigimame ne ai na yi tunanin kana iya zubawa kowa rigimarka banda ni! 

Walyn, 

Ya fada a hankali, kafin yake cin gaba” ki yi hakuri kin ji? Dare ne ki daina daga muryarki, sannan ko ba dare ba na fada maki ki daina magana tun karfi har tana fice tawa amo, mace kike, yar kwalisa ba wai wata kara zube ba, sai da na yarda da class dinki kafin na dauko ki, ki yi aiki da iliminki mana? Nifa ba ni na yi kamen nan ba! Aiki ne , doka ce ta hau du wani mai laifi,

To kawai dan nine sarkin son kai sai na ware mijin auntyn matata?,

Wardugu, kana da ikon warewar, in ka ware ba wanda zai daga maganar , kana da ikon zuwa ka fitar da shi a yanzuma ba wanda ya isa ya ja da maganar,

Wardugu ya tashi zaune, tuni hankalinsa ya fara tashi ya ce” kina nufin in na je na fido shi shikenan nine general Wardugu ba wanda ya isa ya ja da ni?

Walyn ta kale shi ta ce” karya na yi ne?

Wardugu ya girgiza kai ya ce” a niger, a duniya ba wanda ya isa ya zo ya titsiye ni walyn aman in fa a hanyata ta dawowa daga fido shi na mutu na tarda general din baki daya? Ya zata kare min? Shikennan dan ina tsoron bacin ranki da na iyayenki sai in bata tsakanina da mahalicina? Walyn wasa kike da lamarina, kina aurena aman baki san waye ni ba! Kema kin kwana a cel bare wani tsohon dan kacare! Kin san yana me na kama shi? Tare da wa? Ku kiyaye fitina sai ku zauna lafia walyn tashi ki bar min dakina! 

Rai bace ta diro daga saman bed din ta saka rigarta ta bar pant din a nan, sai da ta kai kofa ta ce” inma me yake yi shi a bayanne yake yi wa ya san me wani ke aikatawa da Alhinayettt! 

Tana gama fada ta yi waje da sauri abinta,

Da mamaki ya rakata da kallo, 

Ya so abin ya bata masa rai sai kawai ya yi watsi da shi ya mike yana murmushi ya shiga ya tsaftato jikinta ya dawo falo ya kwonta

Tun karfe bakwai aka farka a gidan Wardugu,

Ayya ta fito da yarta su sai gida,

Mahaifiyar walyn ta fito da kanwarta su mijinsu,

Mu.azam ya fito cikin dakakiyar shadar wardugu sai kanshi yake bazawa,

Walyn na daki tana ramuwar bacin da suka kwana zaune suna masifa da iyayenta,

Agaishat dake zaune jikin Ayya, domin yanda ka san mage haka take, ta lafe jikin Ayya kanta a konce kan cinyar Ayya take hangen yanda Mu.azam ke aika mata da murmushi, ya aske gashin kansa ya yi irin askin nan na samari ya yi kyau abinsa sai daukan ido yake, a baza abubuwan kari a falon na wardugu hakama na walyn,

Takunsa ya shaida fitowarsa,

Tafiya ce yake cikin isa da takama,

Yana fitowa du suka kai dubansu wajensa,

Wani irin faduwar gaba ne ya samu Agaishat, a ranta ta ayana ya salam,

Wardugu ya karasa direct wajen Ayya,

Yana tafe ne yana kallon yarinyar dake kwonce saman cinyar Ayyarsa, wace irin gaisuwa zai yiwa mamansa ne? 

Yana karasowa ya ja ya tsaya, kaki ne jikinsa tun daga hular kansa har takalmansu na sojoji, sababi ne bugagu ne na manya da galolinsa a jiki na shaidar shi din waye,

Gilashin idonsa ya cire ya saka idannuwansa cikin nata,

Wani irin tsam ta ji a gaba daya jikinta hakan ya saka ta kankame hannun Ayya, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button