BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 21 to 30

Da ido yake nuna mata ta matsa ya yi hugin din mamarsa , aman Agaishat bata gane ba domin ba.a taba haka da ita ba,

Idannuwansa ya lumshe, a hankali ya duka ya kai hannunsa ba wani dar ko tsaye tsaye ya kama hannunta ya aniya dagata daga cinyar Ayya, 

Agaishat da ta yi mutuwar kwonce???? ta zazaro ido tana kallonsa tartar

A hankali ya bude bakinsa ya busa mata iska wajen idannuwanta ya karasa mikar da ita kafin yake yatsina fuska, 

Ayya dake kallon ikon allah ta ce” kai daina taba min hannun yarinya ita ba irin wannan kawar taka bace! Meye haka zaka hanata hutawa?

Wardugu ya turo baki sai kace wani shagwababe ya duko ya dan yi huging din Ayya, a hankali ya ce” ni ni ne na wajenki kar ki manta Ayyana, ina kwana,

Ayya ta rungume shi itama tana murmushi ta ce” sannu da tashi Wardugu , aman ka ga yarinyata yanzu na fi ji da ita kan ku, ai ku maza ne ,

Ya yi murmushi yana kallon yanda Ayya ke kokarin maido da Agaishat jikinta,

Cika Ayya ya yi ya ce” amini abin kauna,

Mu.azam dake danna waya yana faman blok din yarinyar nan docter, domin ta whatsup sai kuka take masa ta fame shi fa walahi gatannan zuwa nigeriar ta dawo da shi a yi masa aiki, ya dan dagawa Wardugu hannu,

Wardugu ya girgiza kai ya ce” tashi ka ja ku bi bayana na raka ku, aiki ne da ni fa ka sani,

Mikewa ya yi inda su Ayya ma suka fice suka nufi mota ba tare da Wardugu ya koma bangaren walyn ba domin ya san ko ya je wata rigimar ce zasu yi dan haka ya shige dankareriyar sabuwar rangrover dinsa ya ja gaba su Mu.azam na biyr da shi a baya,

Du inda suka zo gilas kawai yake saukewa ya yi nuni fa yana tare da motar su mu.azam har suka karaso gidan Ayya

Wata mahaukaciyar mota fara ce fake a kofar gidan, suna karasawa mai motar da ya juya keyarsa ya juyo yana kallonsu waya a kage a kunnesa

Datijo ne dogo fari kal, cikin manyan kaya yake ya yi rawani aman ya bude habarsa, 

Gabansa ne ya yanke ya fadi gannin yaronsa cilo da ya malaka yanda ya fito daga mota ya zama cikenken namiji mai jini a hanci, 

A hankali ya hango matarsa, aminiyarsa, mai kaunarsa , ta fito daga bayan motar daya ta karaso wajen wardugu,

A hankali wardugu ya rike hannayenta yana dubanta cikin ido ya ce ” mahaifiyata, ban kama matar Marahut dan na hada ki rigima da shi ko dan daukan fansa ba, ta cancanci kamawar ne, ina rokon ki da kar ki biyewa kowa ciki kuwa harda Marahut! 

Ayya ta rike kuncinsa , ta sakar masa murmushi ta ce” na sani, kaida ba mace ba mai zai saka ka yi aikin mata? Na yarda da kai Wardugu, mahaifinka kai ya zo nema ba ni ba domin ya san wacece ni, ba abinda zai hada shi da ni , ka je aikinka, sai dai ina kara jadada maka ka kiyaye bakin mutane , ka yi aikinka domin Allah , 

Wardu ya gyada kansa ya mayar da ita mota inda tuni mai gadi ya bude mu.azam da ya sada kansa kar Aba Marahut ya gane shi ya ja motar ya shige gidan Ayya

Agaishat dake zaune gaban motar a hankali take hangen Wardugu har ya shige tasa motar ba tare da ya nuna ya ga halitar wani a wajen ba ya tayar ya ja motarsa ya nufi wajen aiki

Murmushi marahut ya yi bayan mai gadi yana kokarin rufe gidan ya dakatar da shi ya tura ya shige daidai Ayya ta fito daga motar, 

Kokarin tafiya take domin ta ga shigowarsa sai dai me, 

Muryarsa ta tsinta , muryarsa mai gigitata, a hankali cikin sanyi ya ce” *asalamu alaiki anmi Wardugu!*

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        3️⃣0️⃣

Dan jim Ayya ta yi, kafin take dora kafafuwanta ta fara hawa yan matatakala kwaya uku dake sadata da balbalin bangarenta,

A nitse a dake ya kuma furta” du musulmin kirki ya dace ya amsa salama koda iya abinda zai fada kennan,

Ja Ayya ta yi ta tsaya tinawa da ta yi tare take da su Mu.azam, ko ba komai bata so yarinyar da ta dauko riko, ta dauka tamkar yarta ta cikinta ta yi wani tunani a kanta, dan haka ta ja ta tsaya ta juyo a nitse tana kallonsa ido cikin ido ta ce” amen wa alaika salam,

A hankali ya kai hannunsa jikin karfen ginnin yana kallonta, matarsa uwar dansa, auren soyaya suka yi ba na hadi ba, auren fahimtar juna mai cike da nishadi, sai dai ya yi sake, ya yarda laifinsa ne hakan ta faru, a hankali ya ce” wa ya baki izinin yin tafia har kasar agadez kauyen agadez timiya ? Kika je kika yi har kusan wata biyu? Anmi wardugu banda fitar ta cikin garin Niamey yanzu kuma har kin fara yin ta nesa haka? Ba dai a so zuciyata ta huta …..

Ya karashe yana dan sada kansa,

Mamaki take, al.ajabinsa take, uhum lalema, me yake nufi da ita? Kennan yana bibiyar rayuwarta ko me? 

Fuska ta yatsina kafin take fadin” gidan nan ban yarda Wardugu ya saka ko sisinsa ba dan kar watarana ka zo da takamar danka ya gina, 

Marahut ya ce” bayan Allah ya halita min ziyarta inda gonata take a duk lokacin da na yi niya?

Haushi ne ya cika Ayya, yana nufin ita, dan kuwa ai matayenku kamar gonakinku ne, 

Dan juyawa ta yi ta ce” ka tarda shi inda yake ba gidana ba,

Dan daga murya Marahut ya yi , domin ta tafi ya ce” ki kiyaye fita kai sake ko dan yarmu da kika dauko kar ta koyi yawo ba izinin miji idan mun yi mata aure! 

Wani irin bude kofar ta yi ta rufota da karfin gaske wanda da ba dan glas din mai nauyi kuma mai karfi bane da kasa zai zubo baki dayansa.

Murmushi ya yi, a hankali ya sauko wajen su Mu.azam dake tsaye cirko cirko,

Mu.azam ya gama yarda wajen wa Wardugu ya yi gadon abubuwa, 

Gashi mahaifinsa ya kai shekaru sitin da yan kai aman yana abubuwa tamkar wani bajimin matashin sarki?

Yana karasowa ya saki fuskarsa sosai ya mikawa Mu.azam hannu,

A mutunce Mu.azam ya gaisar da shi,

Marahut ya amsa yana dubansa kafin yake kai dubansa wajen Agaishat, da yaren buzanci ya ce” ina murna da kasancewa Abanki yarinyata,

Agaishat ta ji abin sabo, abin ya zo mata a bawai, ikon Allah, mutun ya wannan, ya kirata da yarinyarsa, gashi fari karkarkar ita kuwa baka kirin aman bai nuna kyamata ba, harma ya fada mata ya yi murnar kasancewarta yarinyarsa,

Baki kawai ta saki tana kallon kama, kai har yannayin girman jikin domin Ayya bata da girman jiki irin wannan ,

Hannunsa da ya dora a kafadarta na dama ya ce” sannan ki yi ta kulawa da kanki ki yiwa Ayyarki biyaya, zan yi tafia sai na dawo ………..

Agaishat da wata kwallah ta tarun mata a ido tana kallo ya fice a gidan a kafarsa domin a waje ya bar motarsa,

Yana fita ta juyo wajen Mu.azam, da tsananin murna ta ce” ka ji me ya kira ni? *Yarinyarsa*, 

Mu.azam na kallonta shima da murmuahin a fuskarsa yana kallo hawayen murna ya zubo daga idannuwanta, 

Cike da zumudi ta ce” kuma kuma yace ya yi murna da kasancewata tare da su, yaya Mu.azam ni *BAK’A*, 

ai bai kai ga bata amsa ba ta cikashi ta shiga taka matatakalar da gudun tsiya dan zuwa fadawa Ayya cike da murna,

Sai dai tana shiga ta tarar da Ayya zaune ta hade rai tamkar an yi mata mutuwa, yannayinta ya nuna tana cikin yannayin bacin rai mai tsanani

A hankali ta shiga dan takawa dan karasawa kusa da Ayya, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button