BAK’A CE Page 21 to 30

Tsareni ya yi da ido kawai, zuwa wani dan lokacin ya mike ya fice abinsa hakan ya haifar min da faduear gaban ko ya yi fushi ya bar ni ne?
Kwana biyu tsakani na dawo daga makarantar dare islamiya da nake zuwa a kusa da mu na tarar da kakata zaune tana jan carbinta da rufarta bata kwonta ba, ba kamar sauran lokutan ba,
Da sasarfa na karasa wajenta dan gannin abinda ke damunta sai dai ina zuwa ta rike hannayena tana kallona ido cikin ido ta ce” Zannaba, kina ta adu.ar neman Allah ya baki miji na garin nan kuwa?
Na amsata ina dubanta da wani irin yannayi ta ci gaba” an zo neman auren ki daga gidan Elum, Zannaba kin ji zuciyarki ta aminta da Marahut?
Wara irin kunya ce ta diro mani, domin fa Agaishat yata tubawa na da muguwar kunya, batuben mutun na da kunya harda ta mamaki, hakan ya saka na sada kaina kasa harma jikina ya fara rawa,
Kakata ta ce” kul, na hane ki da ki yi haka da ni, ke kawai gare ni kema ni kawai na rage maki, Allah shi ne gatanmu, zan so ace na bar ki hannu mai kyau, dan haka maza bani hankalin ki mu gama magana,
In takaice maki a wannan rana bamu kwonta ba du sai da muka dauki niyar istihara wace cikin kwana uku hankalin mu ya gama kwonciya har ma muka aminta da auren nan,
Marahut ya yi min gata , agaishat ya kai kudin aurena ya yi min kayan da aka jima ana labarinsa, aka daura aurena irin na kowace yar gata inda kakata ta bada mamaki ashe tana ajiye da sarkokin aurensu ita da mahaifiyata, ta kai aka buge akai min tafkekiyar sarka da abubuwan hannu na zinari irin na kowace batuba yar gata, sannan ta fitar da kadarorin mahaifanna harma da nata gaba daya ta raba aka yi min kayan daki sauran ta damkawa mai anguwar anguwarmu amana,
Wsshe garin auren mu Marahut ya dankara min wata makekiyar sarka ta zinari tatare da kwacakwablarta bisa al.adun tubawa wanda hausa ce cikin hausa, ba.a jima ba muka daga dan komawa bakin aikinsa inda aka maida shi domin baban likita ne kuma yana harkar kasuwanci da kiwo…..
Mun kasance cikin farin ciki, mutunta juna, da kaunar juna, muna tafiar da rayuwar aurenmu bisa tsarin islama muna kiyaye du wani abinda zai firgita mu sai dadaykun da baza.a rasa ba na yau da kulun!
A haka na samu cikin wardugu,
Mu kai rainon abinmu har na tashi haihuwa inda Allah ya taimake ni na haihu a hannun mijina a asibitin da yake aiki da taimakawar nurse..
.
Mun koma gida dan zanen sunna, nan Marahut ya gabatar da sunnan *WARDUGU* a matsayin sunnan da ya zaba,
Kowa ya jinjina lamarin sai dai ikonsa ne, dansa ne, aman sunnan Wardugu linzami ne ga mutun mai zuciya, mai fada, mai balaki, kai ba.a zama lafia da mai sunna wardugu, Wardugu! HUM, ko canfawa ne mun yi kuma yana bin mu, kwarai zahiri ne Wardugu duniya ne guda, ba sai an koya masa ba da abinsa aka haife shi…….
Ina wanka a gida wajen kakata, tana kula da lamarina sosai da sosai, wata rana muka wayi gari da kyautar Allah, inda mutuwa ta sake zagayowa ta tsame min wace ta min saura a tarihin iyayena,
Ayya ta yi shiru ta share kwalar da ta zubo mata,
Agaishat da ta yi lamo ta dora kanta a hannun Ayya, Ayya ta ci gaba” Agaishat na ji mutuwar baiwar Allahn nan, domin ni ita ce duniyata, ko me na kwaso ita nake fadawa a nitse ta warware min, ta rasu ta bar ni da jaririn da a lokacin bana iya daukansa da garaje dan girmansa masha Allah, ta bar ni da dan labubun yaron da yakan calara kuka wai shima nice mahaifiyarsa, na ga rana na godewa Allah,
Agaishat ta kara jimke hannun Ayya itama tana jin yanda hawayen ya zubo mata, Ayya baiwar Allah, bata da kowa gaba da baya, ashe du yanda mutun ya kai ga malakar arziki bashi da cikeken farin ciki na yanayin rayuwar yau da kulun?
Ayya ta ce” na dawo ga marahut, bani da kowa bani da komai sai Shi a nan cikin duniya,
Bayan an yi bakwai muka juya garinmu inda na dauki girma na ajiyewa kaina na karfi da yaji na ci gaba da karatun likitana da nake yi a Ensp,
Can tsakiyar dare nakan dadaba Marahut, idan ya farka sai nace” Marahut, kar ka wulakanta ni a duniya, kai ne duniyata, kai ne farin cikina,
Yakan riko ni jikinsa ya ce” ban aure ki ba sai da na gane ke ce lumfashina, a duniya baki daya me ya kai lumfashin mutun tsada? Ba zan yi garajen gannin hawayenki ba sai na kadara!
Magangannunsa da alkawarurukansa suka saka na samu nutsuwar zuciyata harma na warware na ci gaba da shagulgulana na yau da kulun tare da yarona,
Tun Wardugu na da wata bakwai ya mike, yana tafiya da kafafuwansa digir digir tamkar dan gwari,
Du inda na yarda na je da shi idan ya damki yaro ko matashi sai an kwace da kyar,
Ya kasance ba.a gardama da shi da ya warware, yana fama da ciwon athsm wace in dai na yarda ransa ya baci toh fa a kadan mu yi kwana uku a asibiti domin athsmar nan zata tashi ne ya kasance daga ta kwonta sai ta kuma tashi domin ba zai kwontar da hankalin nasa ba,
Wardugu zuciyar mahaifinsa ne, domin daga shi ko batan wata ban kuma yi ba, muna bibjyar komai nasa tamkar ranmu, kai har bama kawaici a nuna soyayarsa,
A haka Allah ya hada mu da baba tsofo, wanda kawai salama ya yi yace yana bayar da magungunnan hausa ne,
Nan muka zanta a bayan idon mahaifin Wardugu domin baya son lamarin hausan nan wai tsoro yake ya taba masa reins,
Cikin ikon Allah ya ki karbar kudina, muka ajiye magana idan Wardugu ya samu lafia zan yi masa kyauta,
Yakan zo lokaci zuwa lokaci ya kawo mana magannin da cikin ikon Allah muke bashi da nonon rakumi sabon tatsa da sasafe, tun ina boyewa har na bayannawa Marahut shima ya kama mani domin sauki kamar da wasa Wardugu na samu a hankali a hankali har ya daina lumfashi da bakinsa ya dawo yi da hancinsa,
Agaishat na kasance mutun mai shegen son mutane, ko dan na sakawa kaina bani da kowan nan a duniya sai Allah sai mijina? Ya kasance son yaya da yawan kula zumunci da jama.a,
A haka na hadu da babar aminiyata matar sarkin agadez, na hadu da kawata ta damagaran hajia Falmata, da sauran su,
Wardugu rashin lafiarsa kawai ya warke aman halaya na nan, a haka aka tsahe mu aka maido mu garin nan inda kwata kwata baba tsoho ya bace min na neme shi na rasa har muka taso aman abin na tsaye a raina sannan ina yawan tambaya,
Kwonci tashi wardugu ya tashi da niyar shi fa soja, soja, hakan ya sa mahaifinsa ya sama mana waje a Babar makarantar sojojin niger wace ke a kwalo, wace tun yaro na karami ake kai shi shikennan shi da iyayensa sai jifa jifa,
Karatu yake, sannan kwazo yake da shi ko a filin training,
Hakan ya sa babansu yake kaunarsa harma yake zumunci da mahaifinsa
Wardugu na da shekara ashirin da biyu ya fito gagarumin comandan, jikaken saurayi, kaukauran namiji, zakin zamani, yaro da kudi kamar yanda ake kirarinsa…….
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3️⃣3️⃣
To tunda Wardugu ya dawo sai kuwa yan mata suka ce bismillah, ba kalar wace bata zuwa , kin dai ga yanda yake uwa kurman nan? Toh haka zasu zo su karaci haukansu sai dai su yi su gama su tafi,